YANCIN KI Page 51 to 60 (The End)

“me’ad ki kular min da kanki duk da kince kin daina sona Wanda ni nasan karya ne hkn bazai ta’ba kasancewa ba muddin ina raye ……
“Idan kuma hasashena bai zamanto gaske ba ,kiyi k’ok’arin ki dawo da soyayyata sabuwa fill acikin zuciyarki saboda babu kalmar rabuwa acikin tsarinmu kmr yadda kika sha Fada min abaya, Dan ko kin barni ni bazan barki ba sai dai mubi juna ……
yana gama fad’ar hk ya kamo fuskarta yayiwa lips dinta light kiss “bye take good care of yourself for me before na dawo a fafata ya juya yasoma tafiya yana taku kmr bai son taka kasa , tabi bayansa da wani irin kallo kirjinta na dukan uku uku har ya bar office din idanunta na Kan kofar ta kasa d’auke idanunta akan kofar daya fita.
ahankali cike da matsanancin sanyi jiki ta k’arasa tayiwa kofar key ta dawo ta d’auki hijabinta ta saka sannan ta d’auki farar envelop din daya bar mata ta koma mazauninta ta zauna tana sauke ajiyar zuciya sannan ta bud’e envelop din inda ta ci karo da wata farar takadar tasoma dubawa a natse .
gyara zamanta tayi sosai saboda abinda idanunta yagani fu’ad ne ya kusan taka matsayin MD na companies din dayake aiki tare da Karin albashi na dubu dari duhu da hamsi Akan 150k dayake amsa a watanin baya da suka gabata,sababbin motaci guda biyu da gida….runtse idanunta tayi hawaye suka gangaro bisa kuncinta ahankali ta furta “Allah kenan babu yadda bai iya da lamarinsa ba ,abinda suka dade suna jiran zuwansa, azahirin gsky tayi matukar farinciki ,duk da batare zasu ci wannan samuwar datazo masa ba wunin ranar kusan cikin farinciki da annashuwa tayisa ……..
**************
Asabar din karshen wata march ,kofar gidan tshohun commissioned of police na Nigeria makil yake taf da dubban jama’a dake cikin garin lagos da wajenta , suka sheida d’aurin aurin khalid Ismail money mis road da sajida Aliyu a lagos state central mosque a kan Sadaki mafi kankanta…..
Mmn sudais ce
????????????????????????
‘YAN CINKI
????????????????
????????????????????????
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
*AUNTY BASEERA WANNAN PAJIN NAKI NE , INA MATUKAR GODIYA BISA GA SOYAYYARKI , ALKHAIRINKI,KULAWARKI GARENI ALLAH YA BARMU TARE*????????????????????????
Page 82
……..tana tsaka da bacci ,tayi wata irin zabura ta mike zaune akan gadonta tana zare idanuwa ,gumi na karyo mata ta koina a sansar jikinta tmkr ac dake cikin d’akin ya daina aiki . kirjinta ne yashiga mahaukacin bugu da karfin gaske, yayinda kunnuwanta ke sake jiyo mata abinda ya farkar daita daga baccinta,sautin muryar maroka tacigaba da jiyowa suna tashi ta koina ,a kofar gidansu maroka ke yin kirarin Amman ji take timkr acikin d’akinta sukeyi ,tayi wata irin zabura ta mike tare da hantsilowa daga saman gadon jikinta na wani irin kyarma……
ta fito daga ita sai rigar bacci iya cinyarta .
tana k’arasowa parlour’n nan tashin hankalinta ya karu sakamakon fuskokin mutanen daban daban tagani makil acikin parlour’n suna cike da matsanancin farinciki, wanda hkn yasa tayi tsaye turus tana binsu da wani irin kallon mamaki yayinda hankalinta ke k’ara tashi ,sakamakon yadda marokan ke maimata kirari Tare da ambato sunansa Dana mahaifinsa da kakanninsa “yeeeeee kuwa jama’a ku sheida an d’aura auren sajida Aliyu da khalid money mis road jikan sani gilo… Allah ya sanyawa aurensu albarka ,”hakika khalid kashigo gidan girma tare da sa’ar mallakar ‘yar gata shalele agurin mahaifinta , hjy sajida ikon Allah yarinya irin arziki wacce ta taso cikin arziki ,hjy sajida kiyi min arziki ki sha min arziki ,arziki nke so daga gareki ,ina son kujera hajjin bana da sabuwar mota yar yayi , take dady yace an bashi ,”khalid kaima irin arziki ne wanda ya gada tun daga kan ka kannin kakaninsa, ka nuna halin girma khalid banda makodo domin gadon gidanku ……ai kuwa aka kashe dariya.
“shin gaskiya ne abinda kunnuwanta suke jiyo mata daga bakin maroka nan ko kuwa har lokacin mafarki take yi? Tayiwa kanta tambayar tana mai kai
hannunta ta muntsini gefen kuncinta taji ko mafarki take ko kuwa a zahiri ne abinda ke faruwa an d’aura aurenta da Khalid .. …..
jin zafin da taji ne yasa ta fahimci a zahirance ne ba mafarki ba ,take jikinta ya d’auki kar karwa …….
wata daga cikin makociyar ce tayi bud’a ” eyyyyyirrrrrr “ga amarya nan ta fito ,nan hankalin mutane gabadaya sukayo kanta kowa ka kalli fuskarsa agurin cike take da tsantsar farinciki da annashuwa.
cikin haka sai ga aunty nadiya ta fito daga cikin d’akinta rike da Wasu kaya zumar zuwa ta tasheta a bacci tasanyata tayi wanka tasa batare dasanin komai ba .
da sauri sajida tak’aro gareta “aunty yaushe duka wannan abun ya faru batare da sanina ba… ?
“Wai ma auren wa aka d’aura yanzu ?
aunty nadiya takamo hannunta cikin nata tace “ki natsu sajida ki dawo cikin natsuwarki mu … ..
Tayi saurin katse aunty nadiya ta hanyar cewa “bazan ta’ba dawowa cikin natsuwata ba har sai naji zahirin gsky abinda ya faru plz auntu ki gaya min auren wa aka d’aura ?
“saboda ‘kwa’kwaluwata tashiga rudu da gigita akan abinda kunnuwana suke jiyo min daga waje .
Aunty nadiya ta kamo hannuta cikin nata “muje d’akinki muyi magana .
fixge hannunta tayi da karfi daga cikin na aunty nadiya jikinta na rawa, hawaye na bin kuncinta “duk abinda zaki gaya min ki gaya min shi anan ,anan nake son jin komai tak’arasa mgnr tana durkushewa kasa bisa gwiwowinta ,itama aunty nadiya kasa tayi kmr yadda sajida tayi had’e da raunata muryarta Dan kar mutane su fahimci yadda auren yakasance “kukan ya isa hk sajida ,aurenki da Khalid aka d’aura yanzu..
wata irin gigita tayi daga tsugunnen datake tare da d’aura duka hannuwanta bisa kanta” shikenan abinda take tantama gaske ne ya ta faru takare …
take jinta da ganinta ya d’auke na wuncin gadi tashiga kallon jama’ar dake tsaye akanta suna mamakin abinda ke faruwa…
cikin HK tawagar angwane suka sanyo kai cikin gidan bisa al’adar jahar Lagos ,byn d’aurin aure ,ango zashigo tare da abokansa domin gaida dagin amaryasa, sannan suyi hoto da amarya,suna shigowa parlour’n idanunsa ya sauka akan durkushe tana kuka, Sam khalida bai yi tsamanin ganinta hk ba, saboda a tunaninsa ya d’auka zata hauka yi fiyye da hkn.
aunty nadiya najin shigowarsu ta mike tsaye ta koma gefe guda cike da jimami, shi kuwa khalid da sauri ya k’arasa inda take zaune tana zare idanuwa ya tsuguna agabanta tare da baza babbar rigasa ya rufeta dashi dan kar abokansa su karewa yanayinta kallo, yanayin da shi kad’ai ya cancaci ganinsa..
idanunsa ya tsura mata yana kallon yadda hawaye ke bin kuncinta gabadaya ta gigice ta fita haiyacinta, kallo dayan dayayi mata ya gane kalar tashin hankali datake ciki, matsota yayi sosai kmr zai shige cikin jikinta muryarsa a kasalance yakira sunanta”sajida tashi ki koma d’aki, ki suturta min jikinki ,ki daina mamaki da hukunci Allah, kinga yadda alamarin ubangiji yake ko?
nayi magana da harshen malaiku Allah ya amsa ….
tayi masa shiru kasancewa bata cikin hankalinta ,Dan kwata kwata bata San abinda yake fad’a ba ,maganar duniya yayi mata Amman ko gezo batayi ba agurin, ta dawo tamkar mutun mutumi yayinda abokansa suka shiga tsokanarsa … bai juyo ya sauraresu ba yacigaba dayi mata mgn ,kusan minti goma ya lura da tasoma dawowa cikin haiyacinta, Dan haka yasanya duka karfinsa ya cici’beta ya rungumeta bisa kafad’arsa Wanda take parlour’n ya haigitse da ihun jama’a..aunty nadiya kanta sai dataji kunya ta kamata “aunty nadiya ina ne d’akinta ? Inji cewar Khalid