YANCIN KI Page 51 to 60 (The End)

mc ya amshi abun magana yana dry ” ameen sai dai kuma gasky wannan abokin naka baiyi kankaba saboda kowa da irin ra’ayinsa ..
Ita kuwa sajida tun da ta zauna Kan kujerar da
ta ke mallakinta amatsayinta na amarya, hankalinta yasoma barin gangar jikinta, gabadaya tunaninta ya azzara ne akan burin zuciyarta,” wannan karon ma irin zaman rayuwar datayi da emran zatayi da khalid kenan,
tayiwa kanta mgnr zuciyarta na kokawa ….
Dan a yanzu har tasoma hasasho yanayin zaman nasu , Dan sam bata ji zuciyarta zata amince ta hakura ta amsa rayuwa dashi amatsayin miji gareta .
a halin yanzu hankalinta a matukar tashe yake tana sake mamakin yadda khalid ya makalewa aurenta dole, yayinda ga en mata nan birjik a gari da suka fita komai ,”ayanzu datasani take da bata zauna ta hakura da auren emran ba, ga kuma abinda karshenta ya dawo ta bige da auren jinjiri “wace irin rayuwa ce hk ?
“wace irin kaddarar ce haka ta giftawa rayuwarta?
gabadaya komai ya rigada ya cakud’ewa mata tarasa nemowa kanta mafuta “yanzu ya zatayi da rayuwarta?
sosai tayi zurfi cikin tunani Dan kwata kwata ita zantuttukan hamza abokinsa baa shi ga kunnunwata ,hankalinta da tunaninta suna can ga fu’ad dinta ,tana jin ina ma wannan ranar ta kasance ranar aurensu ce da fu’ad dinta sanyin idanunta, hasken zuciyarta, lizamin rayuwarta ,bugun zuciyarta…
“ina ma mafarki take, ba’a gaske bane duk abinda ke faruwa daita? har sanda khalid ya lalu’bo tafin hannuta cikin nasa fuskarsa cike da matsanancin farinciki batasani ba ,Yayinda ta koina acikin hall din murya mc ne ya karad’e gurin ,inda yace “ana son ganin ango da amarya a flow, waigowa Khalid yayi ahankali yana dubanta fuskarsa na sake fad’ad’a farincikinsa.
Amman ganin yanayinta al’amun tashiga duniyar tunanin yasa take murmushin dake fuskarsa d’aukewa cak zuwa wani malolon bakinciki da tarin damuwa, ransa yasoma ‘baci zuciyarsa tashiga rawa rawa Dan ko ba’a gaya masa ba yasan wani tunani take yi daban wanda ba nashi bane .
“shi kuma wulakancin da bazai ta’ba lamunta dashi ba kenan yana zaune ana tunanin waninsa ,ransa a matukar ‘bace ya kai bakinsa daidai saitin kunneta had’e da tausasa muryarsa tmkr bai so yin mgnr yace “ke tsohuwar kawai kiyi maza ki dawo cikin haiyacinki da natsuwarki ana bukatar ganinmu yanxu Dan kin wani shantake atunanin iska …. tunanin abinda bazai ta’ba fissheki ba …..
yana gama fad’ar hk ya mike tsaye tare daita yana kirkiro fara’r dole zuciyarsa a dagule, alokacin shi kad’ai yasan tashin hankali da zuciyarsa take ciki ..
Ahankali yake rike da hannunta yana tafiya ,ita kuma tana biye dashi abaya masu d’aukar hoto da masu d’aukar video suka matso kusa dasu sosai suka shiga aikinsu ,na d’aukarsu har sanda suka sauko daga mazauninsu zuwa tsakiyar hall ,inda mutane suka sake rud’ewa gurin d’aukarsu hoto, sauti na musamman aka sakar musu Amman sajida tayi tsaye ta kasa motsa koda D’an yatsanta ne ,ganinta sam bata ga wani abun rawa ba……
Idan ma rawa zatayi ta rasa Wanda zata tsaya yi rawa dashi sai Khalid ..?
“Ina wannan abun kunyar ba da ita za’a yi ba ,ganinsa take agabanta tmkr mazuru ne agaban zaki ….
Duk da ransa a matukar ‘bace yake ,Amman ya d’aure yayi k’ok’arin sanyawa zuciyarsa da gangar jikinsa jarumta ya kai hannusa daya ya kamo hannunta, while dayan hannunsa na kan west dinta ya matsota ya manneta ajikinsa yana jujjuyawa daita ahankali ahankali .
ai take hall din ya d’auki ihu mutane suka dinga fitowa daya bayan daya, Suna lika musu kudi , tsawon minti 30 sukayi a flow suna rawa ko nace Khalid yake rawa sannan suka koma mazauninsu still hannunsu na sarkefe da juna ….
Bayan sun zauna aka soma ciye ciye da shaye shaye, yan’uwansa suka dinga shiga rawa suna cashewa son ransu, can mc ya sake neman amarya da ango inda yake cewa “uwar ango da kanta zata nuna bajintarta ..haka ba Dan ran sajida yaso ba suka sake fitowa, sai dai abinda ya d’aga mata hankali da bata mamaki bai wuce yadda taga mahaifiyar khalid din taki kallon inda take amatsayinta na matar d’anta ,d’anta kawai ta fuskanta tana zuba masa ruwan kudi shima yaciro rafar yan dari biyar biyar yashiga lika mata , suka ware amarya gefe tmkr basu san Allah yayi halittata agurin ba.
nan fa yan’uwa da abokin arziki suka fito suka dinga yi musu liki wasu daga cikinsu ,su likawa sajida wasu kuwa kiri kiri suka ki, sai mahaifiyarsa hjy zainab da Khalid kawai suke ta fama yiwa liki .
anci an sha an gwangwaje, yayinda ango ya dinga hawa da sauka da amaryarsa, iya hakurin sajida ya k’are inda tace “wallahi ba zata sake tashi fita koina ba , daginsa nayi mata kallon wulakanci da gani gani, daman kasan abinda ka shiryawa zuwa na kenan Dan a wulakantani yasa ka matsa sai nazo?
yadda sukewa auren namu rashin dacewarsa haka zalika abun yake agurina ,wallahi wallahi tunda ka zabi zama dani ka tsiyowa kanka wulakanci da bakinciki tattare da babban tashin hankali har sai ranar daka sakeni dan bazan ta’ba iya zama da kai amatsayin miji ba …..
jin bai ce mata komai ba ya sake bata damar cigaba da maganarta “dan Allah ka kalleni ka kalli kanka nayi maka kama da kalar matar aurenka ban da tsaurin ido irin haka?
“me zanji a aurenka?
“me zaka iya min?
“aikin banza kawai daza’a kawo mutun tsakiyar dangi ana masa kallon tozarci ,da wulakanci bama za bar mutun da abinda yake ji ba da tarin gajiya, dan girman Allah mutun ya sake kankabar riko hannuna da zumar tashi zuwa wani guri ta k’arasa mgnr tana juyar da kanta gefe had’e da jan tsaki.. .
yayi tmkr bai jita ba, yana sake kirkiro murmushin karfin hali duk da azahiri gaskiya maganganunta suna shiga cikin kunnuwansa had’e da kai wa kwalkwaluwarsa farmaki daki daki yake nazarin magnganunta ,ganin sai faman mita ta keyi tana maimata kalmar bazata sake tashi ba, yasa shi cewa “duk ki gama rantse rantseki na banza sai dai banso hkn ya faru ba, Amman sai kin tashi, matsawar aka kiranmu.
” zance gajiya kuma kirki damu kina da d’an shila a hannunki wanda zai iya d’auke miki duk tarin gajiyarki.
taja gutun tsaki aciki ranta taki cewa komai ,Dan kar ya nemi rainata cikin bayyanar nasi .
sai faman cika take tana batsewa azahirin gsky rashin kallon arzikin da mahaifiyarsa da wasu daga cikin daginsa da suka yi ta mata ,ya dameta matukar sannan yayi mugun tsaya mata arai ..
Hall ya hargitse da hayaniyar jama’a inda ta nemi ango tarasa yashige cikin jamarsa ..
gashi duk rabin mutane sun fara wuce wa, ai ko ranta ya sake dagulewa da kyar take janyo numfashi tana fitarwa tsabar bakinciki batayi auni ba sai gani tayi hall din yana neman watsewa sai ita kad’ai zaune akan kujerar tsiya da zuciyarta tayiwa suna da hkn ,da wasu tsirarun mutane , tun ranta na ‘baci yazo ya daina, sai dai hankalinta a matukar tashe yake cike da matsanancin tsoro da faduwar gaba .
tayi tsuru zaune tana mamakin ikon Allah tattare da zallar wulakancinsa gareta ..can sai gashi cikin sauri ya dawo yana cewa “tsohuwar amaryata tashi muje, ko yanzu ma kina son na d’aukeki ne?
Tsam ta mike tsaye tayi gaba tare da yin kasa can da muryarta tace “uwarka ce karewa tsohuwa dan rainin sense kawai .