#Kannywood #Labarina #Izzar_SoKannywoodLabarai

Babban Burina A Yanzu Na Samu Miji Na Gari Nayi Aure >Fati Zinariya

Shafin Rumbun Nishadi na Jaridar Leardeship Hausa ya zakulo muku daya daga cikin fitattun Jaruman Kannywood wadda take haskawa a yanzu wato FATI MUHAMMAD ADAM wadda aka fi sani da FATI ZINARIYA ko HAJIYA SARAH cikin fim din Izzar so.

Jarumar ta bayyana wa masu karatu babban burinta a rayuwa da kuma irin gwagwarmayar da ta sha wajen ganin ta shiga masana’antar Kannywood tare da sauran wasu batutuwan wanda suka shafi sana’arta ta fim ga dai tattaunawarta tare da YAKUBU FURODUSA.

Masu karatu za su so su ji cikakken sunanki tare da dan takaitaccen tarihinki

Da farko dai nii sunana Fati Muhammad Adam wadda aka fi sani da Fati Zinariya, ko kuma na ce Hajjiya Sara, An haifeni a garin Kano anan na girma karamar hukumar Nassarawa unguwar Brigade ‘yan tsire, kuma a kano na yi makaranta.

Me ya ja hankalinki har kika karkata ga harkar fim?

Ya gwagwarmayar shiga fim din ta kasance?

Gaskiya ba a magana, Saboda ina tsoron mahaifina sosai, tsabar tsoron mahaifina da nake yi Boss ma nake ce masa, kuma kaga ina mugun shiri da Dad dina sosai muna da fahimtar juna, amma dai idan nayi laifi ina mugun tsoronsa, saboda idan na yi laifi ma kafin ma ya ji zancen toh wallahi jikina ne zai fara yin rawa sosai, zan ji hankalina ya tashi gaba daya, saboda bana so abinda zan bata masa rai har ta kai abinda zai kaibya ce zai daken ko zai wani abu. Toh tun a lokacin dai ana taimun maganar shiga fim din, tun abin bai shiga jikina ba har kuma na ji ina son sana’ar, Akwai wani matshi a layin mu irin masu sai da katin nan, idan na yi kwalliya sai ya ce min fosta, ni kuma ba na son sunan raina baci yake, sai wata rana akwai wata antina kozin sista na ce Anti Khadija a Abuja take sai ta zo Kano, sai nake ce mata kin ji wannan sunan ni wallahi ba na son sunan ni ba ‘yar fim ba, ni ba mawakiya ba, ni ba wani abu ba sai na fita wan can gayen ya rinka ce mun wata fosta ni wallahi bana son sunan, sai ta ce ai sunan fosta ba wani abu bane ba, toh haka dai.

Lokacin da kika kawo maganar kina son shiga fim, wanne irin kalubale kika fuskanta a dangi musamman yadda a lokacin ba kowa ne ya fuskanci fim ba?

Gaskiya ne, kalubale kuwa ba a magana har ga Allah, kasan shi a rayuwa tarbiyya an ce daga gida ake samun shi, kuma shi daman idan mutum mai tarbiyya ne duk wani hali da za ka shiga a rayuwa ba za ka so wannan tarbiyyar nan taka ta lallace ba, ko kuma ka samu wani sunan da za ka bata  gidanku da shi ba. Idan mutum shi daga gidan tarbiyyar ya fito, ko yaya dai sai ka nuna wannan halin. Farko dai ya kamata ta ci gaba da karatu wanne fim kuma?, surutu dai kala kala, toh ni tunda dai iyayena suka lamince mun suka saka min albarka akan sana’ar, “Idan wannan sana’ar da zan shiga da rabona Ubangiji Allah ya sakani a cikin wannan sana’ar, idan kuma ba shi ne hanyar cin abincina ba Ubangiji Allah ya canja min sana’a” tare da addu’o’i ya ce amin” Toh daga lokacin dai duk wani abu na ‘yan uwa tunda iyaye shika shi maka albarka, har iyaye suka yadda duk fitar da za a yi za a ce Allah ya tsare gaba ya tsare baya, Allah ya dawo da ke lafiya. Aka ga dai shekara daya biyu uku dai tafiyarka bai lalace ba, ba ka daina zumunci ba yadda kake dai abun naka dai karuwa yake na girmama mutane da mutumta kowa da wanda ka sani da wanda baka sani ba kowa naka ne, sai kuma su ga ba wani abu da ya canja a kan tarbiyyata, illa ma abun ma karuwa ya yi, shi ya sa abun ma yake ban mamaki wai ace mutum ya shiga fim tarbiyyarsa ta lalace ya zama irin dai abu dai haka rayuwa marasa kyau, toh sai dai daman da wannan mishon din a cikin zuciyarsa.

Amma dai ga mutum mai fahimta,  wanda ya san mene duniya take ciki, toh kuma kake so ka kare mutuncin gidanku, ba zai taba yiyuwa a ce wai za ka shiga sana’ar lalacewa a ce kowa ya so ba wallahi ba zai taba yiyuwa, amma ga mai wayo daga lokacin da ka shiga sana’ar har duniya ta fara ganeka aka gane waye kai, me ya kamata ka yi? ka boye duk wani abu daka san cewa zai taba maka kariyarka ka kiyaye shi, kasan cewa shi wanda ba a sanshi ba sai ya aikata abunda yafi haka ma ya wuce lafiya amma kai fa da aka sani bunka ma fa ake da sharrin baka ma aikata ba, sharrin ma ake binka da shi ballantana ka aikata duniya kuma ta shaida ka ga ka janyo wa kanka bacin rai wanda babu abin da ya kamata ka sakawa iyayenka da shi illah ace yadda ka shiga fim din nan ka fice shi da salama ba wani hau ba wani abu dai daya fada maka, sai ka gode wa Allah, ba dan komai ba ko da ma babu kure ba ka samu komai ba ko ba komai dai atlis iyayenka sa alfahari da kai yadda ka shiga sana’ar Allah ya hada ka da miji nagari ka fita salamun-salamun ka yi aurenka babu babban rufin asiri da ya fi wannan. Kuma ina tsoron abinda za a ce min yau na aikata abu har ya kai kunnen iyayena ina mugun tsoro sosai.

Kasancewar a yanzu kina daya daga cikin wadanda suke haskawa a masana’antar kannywood, ya kike ji yadda masoya suke kaunarki?

Ka san a rayuwa aka ce mahakurci mawadaci, komai idan ka yi hakuri kai dangana ka yarda cewa Allah ne yake yi ba wani ba, duk yadda ka kai da son abu idan Allah ya ce wannan abun ba naka ba ne toh ka hakura idan kace kuma za ka tilasta kanka na farko ka wulakanta kanka, ka ci mutuncin kanka, ka zo kuma daga baya wannan abun ka zo ba ka same shi ba, amma idan ka yarda da cewa Allah ne yake ba wani ba duk abinda za ka gani ka shanyeshi ka yi hakuri, a cikin tsaigaitacciyar hanya Allah zai bude maka naka ka zo kana jin dadi kana murna kana alfahari da shi, ba karamin dadi nake ji ba, sabida a rayuwa ba abinda ban ji ba, kuma ba abinda ban gani ba.

Duk da dai sana’ata ce ba zan fadi abinda zan tona asiri ba, amma duk inda mutum yake a rayuwar duniya kana da masoya kana da makiya, koda kuwa ba ta wannan bangaren ba a dangin uwa ko na uba duk ana samu za ka ga komau ka yi shi bai masa ba sai dai ka kawar da kai kamar ba ka san ma yana yi ba toh komai sai ka yi hakuri a rayuwa, ba abinda ya fi hakuri a duniya. Ina son masoyana sosai kuma ina alfahari da su, ni wallahi ko mahaukaci ne indai ba zai cutar da ni ba, na rantse da girman Allah indai yana kaunata toh wallahi ina kaunarsa ballantana kuma mutane masu hankali maza da mata na birni dana kauye gaba daya ina kaunarsu, ina alfahari da su, ba karamin dadi nake ji ba. A yanzu ma da na yi suna sai na kara sauke kaina na kara maida kaina simfil kowa bawa ne kuma duk inda na ga mutum ina girmama shi ina mutunta shi kuma har gobe ina mutunta mutane.

Me za ki ce game da Jarumin Izzar so wato Lawan Ahmad game da yadda ya sakaki a wannan babba aikin?

Hakane ba abinda zan ce masa, duk da dai na farko shi wannan malami da na baka labari a baya, da nake cewa ya zo ya samu Dad dina ya masa bayani har mahaifina ya amince toh ai shi ne mutumin farko da ya fara hada ni da Lawan Ahmad ka san malamai da malamai sun san junansu, shi ne ya fara hada ni da Lawan Ahmad ya ce toh ga amana dalibata ce kuma ‘yata ce ya bashi amanata tun a lokacin, ni ban san kowa ba dalilin Lawan Ahmad na fara sanin mutane daban-daban ya hada ni da wannan furodusa din, da wannan darakta din yau da gobe har ya zo ya yi min wani fim dinsa mai suna kanwata na manta sunan dai fim din abun ne da yawa ina tunanin kamar haka sunan yake.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button