ZAIN ABEED 1
Allahamdulillah! Thanks to Almighty ALLAH (swt). For giving me opportunity to start this book. ZAIN_ABEED
Finally, I just want to say that this would never been possible without all of you and I am so, So grateful for everything You have done for me. You guys have seriously made my dream come true and you’re the reason Gaslight even made it this far. I hope that You Will continue to support my Journey as an Author And I can’t wait for You to read the published version
just follow my pen, For i assure You, You Are going to fall in love with
Seriously Love guy’s!❤️ Lot’s of Love NIMCYLUV.
Sadaukar ne ga ADDAH RAMLA #Mai dambu ko bayan babu ni wannan shine zaki tuna dani🥰 Much luv.
I’m just wanted to say Duk wanda labarin bai masa ba, Wallahi ya faɗi duk abinda yay niyya👌🏾Nice dai Marubuciyar Moon, Tsintacciya, Abu Maleek, Sirrin mu, Kwaila ce, Uncle ne e.t.c
Hazon da ake yi, a ƙasar Moscow bai hana jirgin Aeroflot-Plus sauka a Sheremetyevo Airport dake nan ƙasar Moscow ba. The weather is too high pilot ɗin da ƙyar yake iya ganin, mai bashi direction ɗin sauka ƙasa. Banda Snow babu abinda yake zuba. Mai asthma kam sanyin babbar illa zai iya yi masa, zai iya sashi cikin critical condition. A hankali jirgin keyin parking har ya samu wajan tsayawa. Daga can cikin jirgin kowa passengers ne suke ƙoƙarin zame belet ɗin jikinsu domin sauka daga ciki. A hankali yaja numfashi mai ɗan ƙarfi yana matse hannayensa suna bada wani, sauti na gajiya. Wrist ɗin hannunsa ya duba yaga 1:15Am na dare. Gently ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihun suit ɗinsa, walking slowly ya ƙarasa Vip side. He’s just thinking why har yanzu biyuninsa bai fito ba? Is he alright or what? If sanyin nan ya yi effecting health nasa? A fili yace “Ya rabb, ga bawanka” buɗe ƙofar vip ɗin yay a hankali yana mai tura kansa ciki. Cak ya tsaya saboda ganinsa da yay a kwance saman duguwar kujera. Infact bai da alamar tashi, saboda ya lumshe idanunsa tare da harɗe hannayensa a ƙirji Numfashinsa na sauka a hankali. He’s sleeping peacefully yay kyau sosai a baccin, domin gaba ɗaya sumar dake goshinsa ya ɗan zuba fuskarsa kamar wata mace. Ƙuri ZAIN yaywa ABEED da idanunsa wanda suke cike da Zallar so da ƙaunar abokin haihuwar tasa (Twins). Ƙarasa shiga yayi har zuwa inda Abeed ke kwance, yana zuwa ya saka hannunsa ya ware masa hannayensa da suke ƙirji. Shiru Zain yay ganin ƙirjin Abeed na ɗagawa, kafin a hankali ya ɗura kansa a ƙirjin na Abeed domin gano what wrong with him yake jan numfashi haka? Something is fishy Abeed baya bacci cikin airplane. Kansa ya janye kafin a hankali yace “I don’t know what wrong with my Biyuni, bai san me yake ɓoyewa ba,is he hiding something for me? No! Abeed bai zai ɓoyan komai ba, shine rayuwata nine rayuwarsa, he can’t do that…. seriously” ya faɗa yana ɗaukan iphone ɗin Abeed, sosai Zain yay mmkin ganin 20miss call na RIYA tun suna 9ja take kira Abeed, ba kira ɗayan da ya yi, respond. Cike da damuwa Zain yace “sorry Riya, In sha Allah zan shige maki gaba” wayar Abeed ɗin ya saka cikin Aljihu, yana faɗin “I love You Biyunina” motsi Zain ya ji, ya juya da sauri haɗa ido sukai da Abeed, yaga duk yadda ƙwayar idanunsa take blue amma yanzu tayi wani mugun jaa. Shiru yay yana noticing ɗin sa, amma bai gane komai ba. Cikin sakin fuska yace “Yaushe ka tashi?” Kamar Abeed ba zai magana ba sai kuma ya ɗan buɗe baki da ƙyar yana yatsuna fuska, cikin slow voice yace “from i love You Said” ya faɗi hakan yana miƙewa tsaye, tare da unlock na suit nasa. Murmushi kawai Zain yay yana girmama, nauyin bakin Abeed hatta shi da aka haifesu rana ɗaya, lokaci guda,wata guda, shekara guda wani time ɗin banza yake masa. Da mutum uku Abeed yake rayuwa yaji daɗi na farko, abokin haihuwar sa Zain, na biyu Mai martaba sai kuma Naila. Zain nada tsayi, fari ne shi idanunsa ma fara re ne, fuskarsa a sake bashi da wata damuwa, damuwarsa ɗaya akan Biyuninsa. Baya ɓoye komai yana da sauƙin kai. Abeed kuma yana da zuciya baya ƙaunar kallo ko kaɗan idan ba wajan show yaje yana gabatar da waƙarsa ba, baya ƙarya sam bai san yadda ake ba, Idan yace Yes of course yana nufin Yes ɗin. Ko waye kai baka isa yay maka ƙarya ba, fari ne tass, yana da manyan idanu wanda ƙwayar idanun ta kasance blue, ga suma mai kyau har gaban goshi take sakkowa, sumar goshin kuma ita ta banbanta tsakaninsa da Zain, da ita ake iya gane waye Abeed waye Zain. Amma har gobe akwai abinda Abeed yake ɓoyewa Zain, Meye shi?. Toilet ɗin dake cikin jirgin Abeed ya shiga yana tafiya a hankali hannunsa zube cikin Aljihu, yana shiga cikin toilet ɗin ya maida ƙofar ya rufe, kana ya jingina da jikin ƙofar yana jan numfashi da ƙyar, bai damu dan ya rasa ransa ba, amma idan ya rasa ransa wanne hali Zain zai shiga? Wannan tunanin shine yake ƙara damun Abeed yake ya hanashi barci, domin abincike ya nuna cewa saura wata biyar ciff wa’adin rayuwarsa a duniya zai ƙare. Zain jin Abeed shiru ya sanya ɗan yi knocking ƙofar, tare da faɗin “Hey my frnd is everything okay?” Shiru Abeed yay saboda Aman da yazo masa, cikin sauri ya ƙarasa wajan sink ya fara amai wanda rabin aman duk jini ne….. Bakinsa ya wanke tas tare da wanke fuskarsa kana ya buɗe ƙofa ya fito, yana fitowa cikin sauri yay gaba abinsa ba tare daya tsaya Zain ba, yay hakan ne kuma saboda baya son ya fahimci wani abu. Da idanu kawai Zain yabi Abeed dashi. Har zai fita sai yaga inhaler ɗin Abeed girgiza kai kawai yay tare da ɗauka yabi bayansa. A strains ɗin jirgi yaga Abeed tsaye kansa a sunkuye fuskar nan a haɗe tayi jajir, juyawa yawa yay nesa dashi yaga ashe wata baturiya ce ta kafe Abeed ɗin da kallo, murmushi yay yace “Can i call her?” Still Abeed shiru yay, Zain yace “shall we..?” Sai a lokacin Abeed ya ɗaga fararen idanunsa da suka fara dawo wa daidai, ya tsorawa Zain idanu, alamar akwai Abinda yake buƙata wajansa. Dafe kai Zain yay yana faɗin “Ya rabb, i almost frgt wlh” hannu ya sanya a cikin Aljihu ya ɗauko wani mars mai kyau, kana ya matsa kusa dashi suna farcing juna yana sanya ma Abeed mars ɗin tare da faɗin. “How was your body? Sanyin bai dame ka ba ko?” Abeed idanunsa ya lumshe, kana ya buɗe har ya buɗe baki zai Mgna, yaga Wannan baturiyar tana ƙara kallonsa. Hannuna ya ɗura a shoulder ɗin Zain kana ya juyo dashi gabansa hakan yasa ya rufe fuskarsa da jikin Biyunin nasa, fararen idanunsa ya wara kana ya ciro wani ring na Daimond a hannunsu ya kama hannun Zain ya zura masa, yana sakin wani cute smile murya can ƙasa kamar mai tsoro yace “Zakai replacing nawa” ya faɗa yana kama hannun Zain ɗin zuwa wajan wata hadaddiyar mota da tayi parking gabansu, gaba ɗaya a baya suka zauna, driver ya kwashi kayansu, shima ya shiga motar kana ya jasu suka bar airport.
About Azimut Hotel Tulskaya Moscow Motar tasu ta tsaya, Zain ne ya fara fitowa sai Abeed, har lokacin mars ne a fuskarsa, sai wani glass daya saka a idanunsa, kasancewar zuwan sirri sukai yasa, Zain shima ya saka mars cikin nutsuwa ya kama hannun Abeed suka fara shiga cikin reception na hotel alrdy an gama musu komai, key kawai Zain ya amsar musu suka haura sama, room 120 suka tsaya, Zain ya buɗe musu suka shiga, Kallon Abeed Zain yay yace “So what about your show? A wanne hall ne?” Abeed yana cire rigar jikinsa yace “Ba zani ba” da mmki Zain yace “pardon?” Abeed ruwa mai sanyi ya ɗauka tare da ɓalle murfin gorar zai kai bakinsa,Zain yay saurin kwacewa babu alamar wasa yace “Are You at of your sense? Kalli yadda bakinka ke hayaƙi saboda tsananin sanyi, shine zaka sha that stupid water?” Ka faɗa Abeed ya ɗaga irin he doesn’t care ɗin nan, kana ya ƙara ɗaukan wani ruwan zai sha, again Zain ya ƙara kwacewa cikin ɓacin rai tare da ɗaga murya yace “Wai baka tuna cewa lafiya bata isheka ba? Ka manta issues ɗinka na Asthma?” Baya Abeed yay tare da zama kan kujera yana jan numfashi ya jima a haka kafin ya ɗago kansa ya kalli Biyunin nasa, gently ya miƙe tsaye har zuwa inda Zain yake murya a sanyaye yace. “Mutuwa kake tsoro? To….” Cikin faɗa Zain yace “Kada ka sake yi min mgnar mutuwa a nan, kuma mutuwar ta rasa wa zata ɗauka sai kai? Wlh duk sanda aka wayi gari babu kai Tabbas a rana nima zan rasa raina..” taɓe baki Abeed ya yi kawai, yana ju yawa ba tare da yace komai ba, ganin yadda jikin Abeed ɗin ya yi sanyi ne ya sanya Zain saurin shan gabansa, Cak Abeed ya tsaya da tafiyar da yake, kafin ya ɗaga idanunsa suka haɗa idanu da Zain, ganin yadda idanun Zain ya cika da ƙwalla yasa Abeed ɗan zare ido yace “what again?” Kasa mgn Zain yay sai kawai ya rungome Abeed tare da faɗin. “Stay with me Biyuni na, stay with me ABEDDEEN” Murmushi mai ciwo Abeed yay yasan cewa, ɗan uwansa bai san meke damunsa ba, ciwon Asthmar da yake damunsa shi kawai ya sani, a ransa yace “Dole na tafi na barka, I think my mother is calling me” a fili kuma yace “Love u” A sanyaye shima Zain yace “To the rest of my life” da ga nan duk freshen up sukai na jikinsu. Kana suka kwanta bacci, Zain yay bacci cike da damuwa inda ya ɗauki al’ƙawarin zai samu tattauanawa Da Babban likita akan ciwon Abeed.