ZAIN ABEED

ZAIN ABEED 1

Alarm ɗin dake jikin wayar Abeed shine ya fara ƙara, wanda ya sanya Abeed ɗin motsawa kaɗan, slowly kuma ya shiga ware idanunsa saboda nauyin da sukai masa, sam bai yi bacci daran jiya ba, idan ya tuna mgnar Dr Siya yay masa, komai nasa tsayawa yake. He can’t even think mene yake daidai, mene ba daidai ba. Juya ya yi bakinsa ɗauke da addu’a ya ƙarasa buɗe idanunsa, kafin a hankali ya janye duvet ɗin daya rufe jikinsa dashi, miƙewa tsaye ya yi har zai shige toilet sai ya juya ya kalli Zain da har yanzu yake bacci, baya ya koma ya ɗan ja yatsun ƙafar Zain kamar yadda ya saba, ganin ya yi motsi yasa Abeed shigewa toilet. Miƙewa Zain ya yi kai tsaye shima ya shiga wani toilet ɗin. Kusan a tare suka shirya cikin wasu farar Arabian jallabiya mai taushi, Masjid ɗin dake cikin hotel ɗin suka shiga, ana idar da sallar suka dawo gida. Zain ne ya zauna kan kujera cikin sauri yake danna keyboard ɗin system, wani babba case ne dashi wanda zai ja ragamar shari’ar, criminal case domin zargi ne na fashi, har da kisan kai, the case was super bai taɓa samun case mai haɗarin wannan ba, Idanunsa ya ɗaga yana kallon Abeed dake tsaye yana tsiyaya madara a glass cup yace. “Ina confused wani abu” shiru Abeed yay, haka nan yaji baya mood ɗin na Magana, jin shirun yay yawa ya sa Zain yace “Arrogant…” Taɓe baki Abeed ya yi, kana a hankali ya dawo baya ya zauna kan kujera cikin nutsuwa yake shan Madarar, sai da ya shanye tass kana gently ya kalli Zain yana mai shafa gemunsa yace “Me kace?” Ɓata fuska Zain yay yace “Shafa kaji” Cije baki Abeed ya ɗanyi yace “Sorry” Juyawa Abeed system ɗin Zain yay yace “Look, already nayi searching all na abinda nake buƙata but…” Abeed yace “But wat?” Zain yace “firstly wanda nake zargi da akaita fashin, babban mutum ne, secondly yadda akai amfani da mace wajan gudanar da aikin, Lastly bayan fashin da mutumin yake akwai wani abu da yake da ƴan mata, wanda har yanzu shine abinda ban gane masa ba” taɓe baki Abeed ya yi yana Miƙewa tsaye yace “U hve to drop this criminal case ɗin” tunda suka zo sai yanzu Abeed ya yi mgn mai ɗan tsayi, da Mmki Zain yace “Kasan me kace?” Abeed na lumshe idanunsa yace “ka taɓa ji nai hauka ne?” Murmushi Zain yay yace “how can i knw, ina mgnar serious kana wani magana” shiru kawai Abeed ya yi, for some minutes kana ya miƙe ya kalli Zain kamar zai Mgna sai kuma ya yi shiru, gane cewa akwai abinda Abeed ɗin ke son faɗa yasa Zain yace “Speak up my friend, what’s in ur mind?” Abeed ya buɗe baki murya can ƙasa yace “Zakai replacing nawa wajan show”… “Why? Bayan ka amshi kuɗin jama’a, then ta yaya zan iya waƙa nida ba aiki na ba?” Cewar Zain, gaba Abeed ya yi abinsa yana mai faɗin “Be ready, zaka je matsayin ni” yana ƙoƙarin shigewa cikin wani bedroom Zain yace “Oh! Hello idan aka gane cewa bani ne Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas ba fa?” Kai tsaye Abeed yace “No one knows” Ya faɗa yana shigewa bedroom ɗin. Da yamma Zain na zaune watching TV, Abeed ya fito cikin dark blue ɗin floral jacquard one button suit. Zain na ganinsa ya miƙe tare da ƙarasa wajansa, hannun Abeed ɗin ya kama ya ɗaura masa wrist kana ya tsuguna ya sanya Leather shoe yana faɗin “Ina zaka?” Murya can ƙasa Abeed yace “I have a meeting” “meeting?” Zain ya faɗa da mmki, tare da sake faɗin “Yaushe ka tsara?” Shiru ya yi bai magana ba, ganin yadda ya ɗaure fuska yasa Zain yace “it’s okay, kaga weather garin is not good, so take good care of yourself ok?” Abeed na barin room ɗin yace “I’ll..”


A wani yanki dake kudancin garin Katsina. Cikin Wata haɗaɗɗiyar prvt school ta maza da mata. Da sauri class teacher ɗin Yake tafiya it’s already late, amma har yanzu basu fito daga cikin class ba, bayan dukkan student na makarantar sun tafi, kowa ya watse what wrong with them su kullum basa ganewa, they didn’t understand what is good and what’s wrong. ”lazy babies” ya faɗa a Zuciyarsa, cikin class ya shiga shiru babu ƙarar komai, idanunsa ya shiga rarraba wa can ya hango su a zaune ɗaya na drowning a mac nata, ɗaya kuma ta ɗura kanta akan kujera, da mamaki Teacher ɗin yace “SAIRAH” Wacce aka kira da Sairah ɗin ta ajjiye color ɗin hannunta tare da kallon Teacher ɗin, farar yarinya ce ƙyakkyawa, kana kallon ta kasan bafulatana ce ko kuma wani yanki na Fulani, kai tsaye ba zaka fasallata kayanta ba, yanayinta kamar na Kajol😌tana da tawadar Allah a saman hancinta. Ƙuri tayi masa da ido ganin hakan yasa Teacher yace “Haba twins yau kuma me akai maku?” Shiru tayi masa sai kawai yace “Ok tashi ƴar uwar taki” juyawa tayi har lokacin kanta a ƙasa a hankali Sairah ta shiga tashin ta “SARA! SARA!SARA!!” ganin ta motsa yasa ta zame hannunta. Wacce aka kira da Sara ta buɗe idanunta Subuhanallahi, wallahi babu wanda ya isa ya iya bambance wace Sairah wace Sara komai nasu iri guda ne, tawadar Allah ce kawai ta banbanta ta Sairah a saman hanci ta Sara a ƙasa. Ikon Allah buwayi gagara Misali Cikamakin Annabawa da Manzanni, wanda yake halittar Mutane a mahaifa ɗaya, hukumcin sa da buwayarsa ta sanya su zo duniya a tare wanda akewa laƙani da TAGWAYEN ASALI. lumshe idanun Sara tayi kana ta ɗan murguɗa baki, kasancewar ita bata barin ko ta kwana, saɓanin Sairah da take da mugun haƙuri. Teacher yace “Twins ɗin Dady mai akai maku ne yau?” Wata uwar harara Sara ta watsa masa cikin siririyar muryarta mai tsiwar gaske tace “Heyyy! Shut up… And leave” cikin sauri Teacher yace “Ok daman Dadynku yazo ɗaukan ku” da wani sauri suka haɗa baki wajan faɗin “what? Daddy?” Sara ce ta fara yin gaba Sairah kuma ta ɗaukar masu bags nasu. Yana tsaye a kusa da motarsa cikin shiga ta ilhama gaba ɗaya ya naɗa fuskarsa idanunsa ne kawai a waje, yana ganinsu ya saki Murmushi mai sauti tare da buɗe musu hannunsa, gaba ɗaya suka shige jikinsa suna faɗin “We miss you alot Daddy” shiru kawai yay musu Sairah ta shiga gaban mota, Sara a baya kana ya jasu suka bar sclh ɗin. Bayan sunyi nisa sosai ya ɗauke hanyar zuwa gida ya nufi wata hanyar, Sara da bakinta baya shiru tace “Daddy ina zamu?” A taƙaice yace “Unguwa” tun suna Shira sukai shiru bacci ya ɗauke su har suka sake farkawa, wani baccin ya ƙara ɗaukan su.. cikin wani jeji ya shiga mai tsananin duhu da ban tsoro, kana ya kashe motar ya fito, da ɗan sauri ya shiga tashin su “Sara, Sairah” kusan a tare suka farka da mmki suka ce “Daddy area nan is not good, mu koma gida” shiru yayi kawai sai ya jasu jikinsa ya rungume, sun jima a haka kafin yace “Waye ni a wajan ku?” Sara dake tafi surutu tace “Kai ka haife mu Daddy,kai ne babban mu farin cikin mu” da sauri yace “I’m not your father, ban taɓa haihuwa ba, bare na samu albarkar tagwaye kamar ku, Sara ki kula da ƴar uwarki twins ɗinki, Biyuninki, ki kula da ita a nan zan barku” da ƙarfi Sairah tace “Daddy a nan fa? Idan abu ya cinye mu fa?” Yace “Ba abinda zai same ku, rayuwarku cikin jejin nan tafi fiye da wacce za kuyi a waje na, ni ba mahaifinku bane, Zan barku a nan Ubangiji ya ƙaddara saduwar mu” yana faɗin hakan ya shafa kawunansu, ya shige mota, tuni Sairah ta fashe da kuka tana ƙanƙame ƴar uwarta, Sara dake tana dakakkiyar zuciya ajjiyar zuciya kawai take saukewa, idanunta sunyi wani masifar jaa. Daddy da gudu yaja motar yana tafe a motar wani abu mai zafi ya shiga bin fuskarsa, parking ya yi kawai sai ya fashe da wani Irin kuka tare da faɗin “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un i lose my own children….

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button