ZAIN ABEED 10

Da yamma Amma na zaune tare da Zain suna magana a hankali kafin yace “Amma mene yasa zaku biyewa maganar Naila? Ita yanzu me zata ɗorar akan soyayya da zaman takewar aure” Amma tace “Waye zai iya da rigimar Naila, tunda tace sai anyi auren Abeed da Riya kasan babu makawa sai anyi” Zain yace “I’ll talk to her” shiru Amma tayi can kuma tace “Sara taƙi cin komai, hatta Rubutun da aka yi mata taƙi sha ina jin tsorar yanayinta” Zain yace “Tana ina?” Amma tace “she’s in the bedroom” Miƙewa yyi yana faɗin “ɗazo naje hospital zuwa 5pm Abeed zai dawo gida” Amma daba wani shaƙuwa sosai tsakaninta da Abeed ɗin tace “Allah ya kaimu” yace “kin masa sannu da jiki Amma?” Tace “Allah ya bashi lafiya” kallonta kawai yyi sai kuma ya nufi part ɗin da Sara ke ciki….Sara na kwance akan bed tana sanye da wando VGOLD palazzo trousers da riga Silhouette tayi lamo akan bed ɗin idanunta a buɗe ta ƙanƙame pillow, A hankali Zain ya turo ƙofar tare da tsayawa a door way yana ƙare ma Sara, ya jima yana kallonta kafin ya ɗan saki Murmushi yace “Mamana” da sauri Sara ta rufe idanunta tana ɗan tura baki, ƙarasa shigowa ciki yyi tare da tsayawa a kanta yana kallon yadda take bacci domin ya ɗauka bcci take, kanta ya shafa yace “sorry Mamana Allah zai baki lafiya” yana faɗin hakan ya fita zuwa waje, ganin bai ga Amma ba ya sanya ya nufi part ɗin Naila, tsaye yyi saboda jin muryar Riya na kuka tana cewa “Naila ki taimakamin Kice Abeed ya aure ni, zan mutu Naila” Naila tace “Idan kin mutu Allah ya tsine, aure kuma kamar anyi an gama ina cewa nina haifi ubansa, duba nan kiga wanann nonon nawa dashi na shayar dashi” ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaga rigar ta kafin tace “Yoo Allah na tuba daidai nuna tsaraici bashi da kyau ne, na haifi Jafaru na haifi Uban ita Rariya take kowa, Allah na tuba ba gwada mahaifiyar ki bama, ita uwar tawayen ba dangin iya balle na baba fa, kawai taimakon musulunci ne kin sanni akwai tausayi da imani har kuka nake dan tausayi” Riya na ƙara narkewa jikin Naila tace “Ba kince zaki ma Uncle AY Mgna ba?” Naila tace “meye kuma AY Allah na tuba, wannan da bashi da cikakken hankali, wajan Mai martaba zani dakai na, na daina jiran wannan ison na Jakadiya Abar” Murmushi Riya tayi tace “Naila kina son ki rasani” Naila tace “A’a wlh ko a mafarki bani nace zaki auresa ba? Allah na tuba ida bai min biyayya ba ai sai bakina ya kamasa maza tashi kije” Riya ta miƙe tsaye tare da fita, ganin Zain a bakin ƙofa yasa tayi Murmushi tace “Our big lawyer” ya ɗan kalleta yace “Sis” ya faɗi hakan yana shiga ciki, taɓe baki tayi tare da yin gaba, Zain ya ƙarasa shiga ciki kallonsa Naila tayi ganin fuskarsa a ɗaure yasa ta fashe da kuka tace “Wlh inaga aljanu sun shafi yarinyar nan, banda haka mace ba aji ba komai, Allah na tuba mahaukaciya ce ni da zan ɗauki lafiyayyan yaro na bata shi, kalleta fa idanunta a tsakar ka” Zain yace “Drama Queen” tace “me kace?” Yace “cewa nayi bake kika haɗa auren ba?” Tace “Inji Ubanwa? To mai ƙarya a ƙona shi a wuta wlh” shiru kawai yyi mata can kuma ya miƙe tare da fita ya nufi hospital… Lokacin daya isa asibitin ya samu Abeed zaune cikin wasu Racing jersey da Camouflage-print cargo trousers, sai wata red ɗin P.cap daya sanya, farar ƙafarsa sanye cikin Mon mule slippers, jikinsa ne ya cewa Biyuninsa ne ya iso, hakan ya sanya ya ɗaga kansa a hankali suka haɗa ido, har zai magana sai yyi shiru, kafin suce Komai Dr Adyan ya shigo hannunsa riƙe da file da wata injection, ɓata fuska Abeed yyi sosai, Zain yace “Dr da alama allura zakai masa ko” Dr Adyan yace “ba kaga yadda yake muzurai ba, sai an shiga cikin mutane a dinga ɗagawa amma ana tsoran allura” Abeed yyi musu banza, ganin da gske Dr Adyan so yake yyi masa injection ɗin ya sanya ya miƙe tsaye, tare da nufar ƙofa a hankali hannunsa zube cikin Aljihu, Dry sukai tare dashi da Zain, Dr Adyan yace “Our singer nace kada ka manta mgnar mu, domin zanyi tafiya ƙaro karatu amma gobe nake tunanin zan shigo sai mu yi mgn” Abeed murya can ƙasa yace “Talkative” yana faɗin hakan sukai waje, Bayan Zain ya amsar masa maganinsa. A hankali Zain ke jan motar sbd yanayin jikin Abeed har suka ƙarasa Masarauta, Abeed ne ya fito yunwa yake ji sosai cikin dauriya yake takawa, Zain ya biyo bayansa da sauri suka jera Zain ɗin nayi masa sannu, A Parlo suka samu Abba da Amma, Abeed ya zauna ƙasan carpet yana lumshe idanunsa, Amma ganin yadda ya zauna kusa da ita yasa ta miƙe tare da faɗin “Bari a kawo maku abinci” Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yace “how was your body Shalelen Naila?” Abeed na buɗe ido yace “Allhamdulillah Abba, barka da yamma” Abba yace “Yana da kyau ka samu hutu fa” Zain yace “Abba babu inda zashi ai” Abba ya jinjina kai tare da cewa “Allah ya ƙara sauƙi” ya faɗa tare da miƙewa ya nufi part ɗin sa, domin ya tashi daga fada, Zain yace “Amma kawo abincin nan” tace “ok” a nan carpet ta jera musu kana tayi part ɗin Abba, babu ruwan Amma sa sarauta ita kema yaranta abinci haka ma Mai martaba, Zain yace “bari na sauya kaya” Abeed ya jinjina kai, har ya rufe idanunsa sai kuma ya buɗe saboda ganin Sara tsaye bakin ƙofa ta tsora masa ido, yanayinta kawai ya gani ya gane cewa abinci take buƙata, bata fuska yyi tare da haɗe rai Murya can ƙasa yace “Come” kamar jira take tace “Twin” juyawa yyi yaga bbu kowa a parlon, a gabansa Sara ta tsaya ya shiga ƙare mata kallo can yace “juya” bata fahimci me yake nufi ba hakan yasa ta ɗan zaro idanunta waje kamar yadda taga yyi, hannunsu ya saka kamar mai tsoran taɓa abu ya ɗan riƙe belet ɗin wandon ta ya juyar da ita, tsaki yaja ganin yadda kayan ya kama jikinta gashi kanta baku ɗan kwali daman ita kai duk gayyar aljanu, zame hannunsu yyi yace “sit down” shiru tayi masa, a ɗan ƙufule ya ja hannunta ta zauna ƙasa, sukai very close da juna, baya ya matsa ya kalli abinda take kallo, soyayyan naman da yake ta ƙamshi take kallo a hankali yace “Mayya” ganin yyi mata banza tace “Twin” ta faɗa tana nuna masa naman, ya kalleta can ya miƙa hannu tare da ɗaukan naman yace “Haaa” shiru tayi masa domin bata fahimta ba, gently ya sanya tattausan Farin hannunsa tare da tallafo haɓatar, yace “Buɗe” bakinta buɗe ya ɗan kallon fararen haƙoranta a hankali kuma ya sanya mata naman a baki, Murmushi tayi ta amsa ta fara ci ganin zai ajjiye hannunsa tayi saurin riƙe hannunsa tare da cewa “Twin…..
Ina faɗa da babbar Murya na kusa gama free pages😒😍 Duk wanda yake da niyyar biya ya biya tun yanzu a saka shi a original grp👌🏾 zaka biya #500 via 6850917335 Na’ima Shu’aibu sulaiman fidelity bank ka tura Evidence ta wannan number 08119237616 ƴan Niger suyimin mgn zan faɗa musu yadda zasu biya.