ZAIN ABEED

ZAIN ABEED 4

Page 4

Mutanan masu kama da arnan daji sabis yanayi kirarsu da kuma halayya, sune suka ɗauki Sara wacce ko kuka ta kasa yi sai wata wahalalliyar ajjiyar zuciya take saukewa, she wish ace Ubangiji ya ɗauki ranta a yanzu, babu Abinda yake damunta kamar halin da biyuninta Sairah zata shiga, tana can tana jiran ta kawo mata abinci, ga wata ƙaddarar ta faɗa mata, bayan ƙaddarar data sanya Mahaifin daya haifesu da cikinsu shine sanadin faruwar hakan, da ace bai kawo su jeji ya zube ba, ya jasu a ciki kamar yadda ya saba, babu dalilin da zai saya su shiga wannan wahalalliyar rayuwar, a yanzu babu abinda ta tsana a duniya sama da Mahaifin daya haifeta….Gaba ɗaya kan doki suka hau yayinda ɗaya daga cikinsu ya saba Sara a ka faɗa suka juya tare da nufar cikin gari, tafiya sukai mai nisa har suka iso ƙofar shiga wata ƙatuwar masarauta mai suna Zahel Masarautar Zahel Masarauta ce mai ƙarfi, wacce ta shahara a ɓangaren tsafi, Masarautar ta gino a can baya wajan Shekara ta 2,000 da doriya da suka gabata, Masarautar Zahel sun ƙware wajan bautar Gumaka, Dodo, Rana, Ɗan-maraki…Domin girma ne da masarautar saboda girman ta ne yasa suke tunanin samar da sarakuna guda biyu, amma tsananin tashin hankali da son zuciya yasa komai ya gagara, har kawo lokacin da Sarki Mabus ya hau kan kara ga, mutum ne mai ƙarfin iko, wanda ko kallonka ya yi sai da dalili, babu ruwansa da sabo, duk yadda kuke dashi idan Dodo ya buƙaci jininka bashi zai, gashi da mahaukacin kuɗi wanda ba kowa yasan inda yake samu su ba, Yana da mata sama da 20, banda ƴan matan da yake duk wata ya kwanta dasu, idan Allah ya yi a lokacin Dodo ya buƙaci jinin budurwa yana gamawa da ita, zai bada jininta.. Yanzu haka ƴan mata ne sukai ƙaranci a cikin Masarautar babu wanda zai kwanta dasu babu wanda zai bada jininsu a bisa wannan Dalili ya baza dakarunsa wajan samo masa mata, shine sukai katari da Sara.. Sarki Mabus na zaune akan karaga daga shi sai wani ƙaramin abu ɗaya ɗaure ƙugunsa dashi sai wata babbar laya a ƙirjinsa, da wata ƙatuwar wular fata akansa, fuskar nan tasa baƙa ƙirin kamar yadda zuciyarsa take ɓaka, sai muzurai yake gefensa kuma ƙaton wani gunki ne wanda aka ajjiye a cikin fadar na musamman… Ɗaya daga cikin dakarun da suka kama Sara ne ya shigo cikin fadar tare da zubewa a wajan, ya buɗe baki zai masa kirari Mabus yay saurin ɗaga masa hannu alamar ya dagata, cikin wata kakkausar murya yace “Kun samo?” Jikin Badakaren na rawa yace “Ai mana afuwa, munyi neman duniya a wannan gari na Zahel babu wasu ƴan mata face raguwar ƴan matan da suka rage mana a cikin Masarauta, Amma munyi karo da wata ƙyakkyawar budurwa a cikin jejin Zahel, idan ka bamu dama yanzu mu shigo da ita” Mabus ya kalli Badakaren jin yace “ƙyakkyawar budurwa, yasan gaba ɗaya ƴan matan Zahel baƙaƙe ne, amma wacce halitta ce take rayuwa cikin jejin Zahel kuma budurwa ƙyakƙyawa? Kada fa yana zaune a wargatsa masa sihirin da yake jikinsa na shekara da shekaru, kada a hanashi shiga cikin gari ya aiwatar da abinda ya saba, a fili kuma yace “Ƙyakkyawar budurwa fara?” Badakaren yace “Na rantse da abar bauta kabas ƙyakƙyawa ce, ban taɓa ganin mai kyanta a wannan garin na Zahel ba” Miƙewa Mabus ya yi yana zagaye cikin Fadar tasa, kafin yace “A shigo da ita” fita Badakaren ya yi babu jimawa, suka shigo da Sara wacce take ɗaure da igiya ta galabata sosai, wata zabura Mabus ya yi lokacin da idanunsa suka sauka akan ƙyakkyawar fuskar Sara wacce tai wani irin fari na wahala, gashinta mai matuƙar tsayi duk ya wargatse, “Gadiya ta tabbata ga Abin bauta kabas, kunce ta” Mabus ya faɗa yana mai kallon ɗan aikensa yace “Maza kira min boka” Da sauri ɗan aiken ya fita zuwa sashen da bokan masarautar Zahel ɗin yake.. Kunce Sara sukai wacce bata ma san abinda yake faruwa ba, sai bakinta da yake motsi a hankali tana faɗin “Twin Ruwa, Ruwa Twin” Kallo guda Mabus yaywa wani sai gashi ya dawo da wata ƙatuwar ana kamar kuttu, ya buɗe ya kafa a bakin Sara, da sauri ta janye bakinta tana girgiza kai saboda jin ba ruwa bane, Burkutu ce (Giya) A fusace Mabus ya miƙe tsaye tare da ɗauke mutumin da mari yace “Ubanwa yace ka bata Burkutu? La’ananne, Abin bauta kabas ya yi Allah wadai dakai, ku fice min” gaba ɗaya fita sukai, not too long Boka ya shigo tunda idanunsa ya sauka akan Sara yaji gabansa ya faɗi, wata zallar kama idanunsa suke hango masa a fuskarta wacce ya kasa fahimtar kamannin waye? Zama ya yi tare da gaida Mabus, Mabus yace “A kallo guda naji ina kwaɗayin yarinyar nan, ka duba min gobenta yanzu na gani ko akwai ni cikin ƙaddarar rayuwarta, ma’ana ka duba min Zanan ƙaddarar ta” Boka ya zube kayan aikinsa tsaf, hadda Madubin tsafinsa, Sara wacce ke kwance bayan an bata ruwa sai sauke numfashi take tana kiran sunan ƴar uwarta Sairah, ƙuri Boka ya yi mata da idanunsa, kafin ya kama miƙa hannu zai kama hannunta cikin sauri Mabus ya daka masa tsawa yace “Kada ka kuskura ka taɓa ta” Ya faɗi hakan yana matsawa kusa da Sara tare da kama hannunta ya nunawa bokan, sun jima a haka kafin bokan yace “Ya yi” Mabus yace “Labarta min me ka gani, yakai La’ananan boka?” Boka yace “Abu na farko, dole ka auri Yarinyar nan, auren ta shine zai kare ka daga sharrin wasu mazan da suke tunkaro ka, na biyu kuma Tabbas shigowar ta cikin Masarautar Zahel tsararran abu ne, ba ganganci ba, ka sani bakai ka kawo ta cikin Masarautar nan ba, Ita ta kawo kanta kamar yadda zanan ƙaddarar ta ya nuna, zaka samu ɗaukaka ta sanadin ta, wacce babu sarkin daya taɓa samu a masarautar Zahel, amma dole sai ka aureta, jininta ba zai taɓa shawowa a wajan Dodo ba, sai abu na ƙarshe wanda na kasa ganewa kuma shine mafi haɗari, amma zan ci gaba da dubawa tare da ƴan uwana bokaye” Jinjina Kai Sarki Mabus ya yi kana ya saki dariya yace “Dole ne ta zama Sarauniyar Zahel….

Today is Sunday, Misalin 3:30 na yamma Zain ya fito cikin wata haɗaɗɗiyar three-piece dinner suit, nevy blue ya sanya wani baƙin glass a idanunsa, sai ƙamshi yake, ga wani mars a fuskarsa, waya ce maƙale a kunansa yana magana da wani akan case ɗin fashin da akai wanda suke bincike akai, Zain yace “I’ll try my own best, wlh ko zai zama aikina na ƙarshe dole sai na binciko duk wanda yake da hannu wajan wannan fashin” Mutumin dake sauraran Zain ta cikin waya yace “In sha Allah, I’m with you komai zai zo da sauƙi, jiran dawowarka muke” Zain yace “this week ina hanya” Mutumin yace “Ok, me kaje yi a Mascow?” Shiru Zain ya yi can yace “Wani aiki naje, Nama gama, I’ll catch you later” Ya faɗa yana kashe wayar, juyawa ya yi suka haɗa ido da Abeed wanda shima ya yi shiga sak irinta Zain, ga wani haɗaɗɗan covet shoe a ƙafarsa, sumar kansa sai kyalli take, ɗan taune bakinsa ya yi, kamar ba zai magana ba sai kuma yace “U look like Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas” Zain yace “Daman shine, and you too u look like Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas” Abeed yana shafa sumarsa zuwa wajansa yace “Yeah” Zain yace “Idan na je maka show ɗin, nima ka zauna kayi min bincike Akan wata ƙasa wai Zahel” Lumshe idanun Abeed ya yi yace “Zahel?” Zain yace “Yap, ka haddace komai na binciken, nasa zaka iya ba sai kayi note ba” Abeed yace “Owk” Kallon juna sukai lokacin ɗaya sukai Murmushi kana suka rungome junansu, Abeed yace “Take care my singer” Zain yace “Ohh! Ai yau ne kawai, bye” yana faɗin hakan ya fita, Abeed kuma yaja idanunsa ya rufe, ya jima a haka kafin ya ja jikinsa zuwa bedroom, wasu Drugs ya ɗauka ya sha, kana ya dawo Parlo bayan ya cire kayan jikinsa ya zauna daga shi sai Cable-knit vest sai tracksuit trousers, System yaja gabansa, hannunsa riƙe da wani Apple juice mai sanyi yana sha, cikin nutsuwa yake danna keyboard na system ɗin, a hankali ya rubuta Zahel waro idanunsa waje ya yi tashin farko da yaga an nuna masa wani ƙaton gunki, A zuciyarsa yace “Ohh God!” daga ƙasa kuma bayanin garin Zahel ya bayyana, zare manyan idanunsa ya ƙara yi, abubuwan da yake karantawa akan Zahel ya munana, a yadda yake gani duk Musulmin daya kuskura ya shiga garin kisan gilla ake masa, shi kowa tayaya zai bar biyuninsa yay wannan aikin na kuskure, daman shi wata biyar suka rage masa, ko sun kashe sa bashi da matsala, amma ba zai yiwu ya mutu kuma a kashe ɗan uwansa ba, Mai martaba ba zai jure rashin su ba, haka ma Naila, Kamar yadda Zain ya tafi wajan show ɗin sa, shi ma zai ɗauki Wannan kasadar shi da kansa Zai je Zahel domin gano asalin abinda yake ɓoye, Sosai Abeed ya girgiza da ganin yanayin Zahel, bai taɓa tunanin har yanzu akwai irin wannan mutunan ba, kashe System ɗin ya yi gaba ɗaya, tare da jan numfashi ya ɗan kwanta jikin kujerar, ji yay gaba ɗaya ya kasa samun nutsuwa ba zai taɓa zuba idanu Zain yaje wannan garin ba, Tabbas a gobe zasu koma 9ja daga nan zai san duk yadda ya yi ya samu fita shi ɗaya. Wayarsa ta fara ƙara yana jinta yay banza da ita, wajan kira uku akai masa, tsaki yaja a kira na huɗun ya ɗauki wayar ashe vedio call ne, ya mance data akwai Wi-Fi a hotel ɗin, sunan RIYA ne ya bayyana, answering ya yi nan take fuskar wata budurwa ya bayyana, tana zaune akan kujera tasha kitso kwaɓe fuska tayi tace “Haba My singer, me nayi kake azabtar dani haka, tun kuna 9ja nake kira, hankali na yaƙi kwanciya, na kira Twin Zain yace kana wajan show, hope everything is ok?” Idanunsa a rufe ba zaka taɓa cewa dashi take magana ba, Riya shiru tayi ta ƙurawa faffaɗan ƙirjinsa ido, bata taɓa ganin mutum mai faɗin ƙirji irin na Abeed ba, ga wasu kwantattun gashi a ƙirjin nasa, sunyi kwance sai kyalli suke, jin shiru yasa Abeed ware idanunsa tsaf akan Wayarsa ganin kallon da take masa, yaja tsaki yana faɗin “Mayya” Murmushi Riya tayi tace “how are you?” Banza ya yi mata yana covering ƙirjinsa da hannayensa domin ya tsani kallo, ganin yay mata banza ya sa ta marairaice tace “Haba My singer, ni ban kai matsayin mata bane? Dako kallo na baka son yi? Kasan irin wahalar da nake sha akan soyayyarka” kai tsaye yace “to ki daina son mn” Riya hawaye na cika mata idanu tace “I can’t, ina masifar sonka, ban damu ka soni ba, burina na ganni a gidan ka matsayin matarka” Idanunsa ya buɗe tare da kallon ta, kanta ta sunkuyar domin bata tunanin zata iya jure kallon ƙwayar idanunsa, ya ɗau lokaci a haka kafin yace “Zaki mutu babu aure ke nan” Tace “Pardon, kana nufin ba zaka auren ba” girgiza mata kai ya yi yace “Babu soyayya a zanan ƙaddara ta, look Riya ke mace ne, kiyi amfani da time da kike dashi ki samu wanda zaki aura, ni Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas wlh ba zan aure ki ba” Kuka Riya ta fashe dashi tana ƙoƙarin Magana ya kashe kiran baki ɗaya, banda tsaki babu abinda Abeed ke ja, ya tsani mace mara aji sam a rayuwarsa, duniya ta lalace Mata suyi ta tallan kansu, wacce irin gantalalliyar rayuwa ce wannan, wani kiran ne ya sake shigowa ganin sunan Mai martaba yasa with so much respect Abeed ya ɗaga kiran, tare da marairaice yana narke murya yace “Abba..” Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas dake Zaune cikin shiga ta alfarma yace “Shalelen Naila” Abeed ya kwaɓe fuska yace “I’m nothing without you Abba” Mai martaba yace “Iyee kamar ni ne Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas” Abeed yay wani ƙawataccen Murmushi yace “Abba..” A hankali Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yace “Ina Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas” Abeed yace “Yes Abba..” Mai martaba yace “mene ya haɗaka da Riya?” Abeed yace “Wace Riya?” Caraf Naila tace “Wata gantalalliya ce mana, to idan ka aureta Allah ya tsine, sai ɗagawa Uban naka nono kowa ya huta idan ya matsa, Meye wata Biya? Ba dangi iya balle na baba, banda lalacewa ta zamani mace tana tallan kanta, wlh Allah ya tsine idan ka aureta, shiyasa kullum a bushe take ashe masifa ce take damunta zata lalata min jika, ƙur’anin Allah bata isa ba, babu ruwana hisba zan kai ta ai min iyaka da ita, banda ma ɗa na kowa ne meye haɗin mu da ɗan gidan Waziri, to wlh imani ne kawai ya yi min yawa shiyasa nake amsa kasuwar yariyar,mai idanu a tsakar ka…” Tunda ta fara mganar Abeed ke Murmushi yana masifar son Granny ɗin tasa, Mai martaba kowa kallon mahaifiyar tasa kawai yake, wai Waziri da yake ɗan ta wanda ta shifa shine ba dangi iya balle na baba… Abeed yay Murmushi yace “Wlh Naila lalata ni kawai take son yi gaba ɗaya nawa nake” Kuka Naila ta saka tace “Allah sarki abin tausayi, wlh tsayin ƙafa ne kawai, yaushe ka girma gaba ɗaya ma, zata ja mana jafa’i wai kayi aure, to Allah ya tsine idan ka aureta….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button