ZAIN ABEED 5
Page 5
Abeed ya ɗan shafa fuskarsa zuwa gemunsa, feeling happy yace “Naila ko kallo na bana son tayi,tsoro nake” Naila ta ƙara fashewa da kuka tace “A’a wlh masifa ce da maita irin ta matan yanzu, yanzu fisabilillahi kallon na mene? Koda yake muna zaune da ita ne amma wlh babu da tabbaci da Zuciyarta, rufin asiri dai yana da daɗi amma da nace Audil ya jawo mana masifa ya kawo mana Mayya” Ta ƙare zan can tana matse hawaye, ganin hakan yasa Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas ya ɗan lumshe idanunsa cikin nutsuwar sa, da kamewa yace “Naila kiyi hqr” Kallonsa tayi tsaf tace “A’a bana son munafurci meye hqr kuma? Ina raga maka ne sbd wannan tafkeken rawanin, maza ka kira min Audillahi (Waziri). Shiru kawai Mai martaba ya yi domin ya san rikicin mahaifiyar tasa, Wayarsa ya ɗauka kasancewar ya bar fada ya ɗan nemi hutu, kiran Waziri ya yi, bayan sun gama waya ya ɗauki Apple a hankali yana ci, can ya nisa yace “Naila Oumarar fa?” Tace “Ai dole naje gaban ma’aiki, na kai masa kuka na, Wannan yaran da baya ƙaunar aure ƙilan shafar aljanu ce billahil lazi, ai su mugwayen mutane ne, basu da kama babu mamaki wata matashiyar aljanarsa ta aure sa” Shiru Mai martaba ya yi idanunsa a lumshe, yana sauraran yadda take zuba magana ta rikici, Sallamar Amintacciyar kuyangar Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas ne ya katse wa Naila Maganar ta, taɓe baki tayi tace “Ke kuwa kiyiwa kanki liɗifi, ko masilin ne kina shafawa, haba wannan baƙi kamar an maki baki” Kuyanga Bira tace “Allah ya ƙarawa Naila lafiya da nisan kwana, daman Wazirin Masarautar Bilhira ke neman iso” Naila tace “Shidai wannan da nema min mgn yake, wallahi wasu sai suce bani na haifesa mene iso kuma Allah na tuba?” Numfashi Mai martaba yaja ya ɗanyi gyaran Murya hakan ya tabbatar da cewa ya bada dama, Fita Kuyanga Bira tayi, tana zuwa ta samu Waziri tsaye cikin shigarsa ta wata alkyabba mai taushi, rusunawa tayi tace “Allah ya taimaki Waziri Mai martaba uban manyan goben wannan masarautar ya bada dama” Jinjina Kai Waziri ya yi yace “Gdy nake Bira” yana faɗin hakan ya shige cikin ƙyakkyawar tirakar ta Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas, yana zuwa ya samu Naila zaune tana lumshe idanu, Sallama ya yi Mai martaba ya amsa a ladabce, yana ɗan gyara muryarsa, Gaisawa sukai, Waziri yace “Barka da hutawa Naila” Naila tace “yanzu nake cewa sashinka zani, gari da yawa ai maye ba zai ci kansa ba, tunda na shigo Yake haɗe fuskarsa, shine nace to ka dan nace a haɗe zumunci ne wannan yaran da Riya take masifar so a bata shi kada ta mutu taja mana masifa, Itama dai ƴar wallahi ruɓaɓɓciya ce me zatai da wani Tagwaye fisabilillahi, nidai ba zan hana ba idan na hana sai na mutu ayi ai” da mamaki Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yake kallon mahaifiyarsa, yanzu tace idan Abeed ya auri Riya Allah ya tsine amma yanzu ga abinda take faɗa, shi dai bai ce komai ba, domin yana faɗa zai jawo wata maganar, Naila tace “Yanzu kaje ka tattaro abinda Allah ya baka ka fara shirin biki, shi kuma wancan tunda ƙaddararsa ke nan, sai dai ya dawo yaji na kai masa kuɗin na gani ina so” Waziri yace “Amma Naila a bari su fara haɗa kansu mana, ban sani ba ko Abeed baya son Riya kada a shiga haƙƙin sa” Naila tace “Nice na haifi iyayen yaran, kuma nice nace a haɗan auren duk wanda zai mutu ya mutu mana billahi wa’adinsa ne ya yi” tana faɗin hakan ya miƙe tare da ɗaukan sandarta tayi waje, gaba ɗaya suka bita da ido, Waziri yace “Bana son wannan haɗin, za’a shiga haƙƙin Abeed, nasan Riya na sonsa, amma shi fa?” Mai martaba yay shiru kamar ba zai magana ba sai kuma yace “Nikam ba ruwa na, abinda tace shi za’ai ina da tabbacin komai zai daidai” Waziri yace “To Allah ya tabbatar da alkairi, amma kada a faɗawa Abeed” Mai martaba ya jinjina kai tare da yin shiru.
Abeed ya taɓa baki yace “Class zero, beauty zero, girki zero, Mtwss” wayar ya ajjiye can gefe, sannu a hankali kuma tunanin Masarautar Zahel ya shiga yi masa yawo cikin tunaninsa, Ya san har abada Zain ba zai hqr da zuwa binciken ba, an yarda dashi a matsayin na gartaccen lawyer, wannan dalilin yasa aka haɗa shi da wasu police na state Cid. Miƙewa ya yi tsaye zuwa wajan fridge ya ɗauki ruwa mai sanyi zai sha yaji ance “Ohh! Hello” juyawa yay da sauri, Zain ne tsaye hannunsa zube cikin Aljihu sai rigar suit ɗin daya cire ya ɗura saman shoulder ɗin sa, he looks so worried, na ganin abinda Abeed ɗin yake, cikin damuwa yace “Baka jin magana Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas” ya faɗa yana buɗe wani fridge ɗin nada ban, ya ɗauko masa bottle of water mai ɗan dama, tare da tsiyaya masa a cup yana faɗin “drink this, and drp that…” Amsa ya yi idanunsa akan Zain so yake yace “how was the show going..?” Amma kalmar tayi masa nauyi da girma a baki, after ya gama shan ruwan ne, ya kalli Zain ɗin wanda yake cewa “Is Riya called?” Gently Abeed ya ɗaga kansa alamar “Eh” Zain yace “I see” Abeed ya buɗe baki da ƙyar yace “Ykk, i mean ya show ɗin?” Zain yace “Ohhhu, ashe mahaukaci mutum yake zama a wajan?” Abeed yay cute smile yace “kaso ka zama dai” Zain yace “pardon?” Shiru kawai Abeed yay tare da ɗaukan ruwa mai sanyi ya bawa Zain, Zain kuma ya girgiza kai yace “murya nake bani mara sanyi” ya yi hakan ne sbd bazai iya hana Abeed sha ba, shi kuma ya sha, Zama Abeed ɗin ya yi kusa da Zain, shi kuma ya shiga bashi labari yana cewa “ban san haka ka tara fans ba, wata budurwa kam wlh na ɗauka rungome ni zatai” taɓe baki Abeed yay kana yace “Oops, nace shari’ar nan, ba zaka iya bawa wani case ɗin ba?” Zain yace “bani na amsa ba, bani akai sbd an yarda dani kuma dole zan tabbatar da gsky tayi halinta” Abeed yace “to kace ba zakai ba mana?”… “Kana hauka? Tabbas zanyi” “Owk” kawai Abeed yace yana lumshe idanunsa, can ya nisa yace “Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas” Zain yace “Na’am” Abeed yace “kana son yin aure ko?” “Of course” A hankali Abeed yace “To Promise me” Zain yace “About?” Kai tsaye Abeed yace “Ni da kai na zan nema maka matar aure, kaban wannan damar” Murmushi kawai Zain yay domin ya san Abeed baya hulɗa da mata, tayaya zai gane nagartacciyar mace har ta zama matarsa? A fili kuma yace “Promise, ko wacce kaban zan aura zan kula da ita daidai iyawa ta”… Washe gari da safe Abeed ya fito cikin voyal irin na sarakai mai masifar kyau, Black colour ya haska fatarsa, sumarsa har baya, cikin nutsuwa yake tafiya a hankali without making any sound, a haka ya fice daga cikin bedroom ɗin zuwa reception, kai tsaye kuma waje yay tare da shiga motar hotel ɗin, gudu yake sosai a tsakiyar titin da zai kaisa hospital, can ya ɗauki Wayarsa ya kira wata number, babu jimawa akai answering yana shiga hospital ɗin yace “Something new?” Dr Adyan dake zaune a office ɗin sa na ƙasar 9ja yace “till now ba wani labari,buhh I’ll try my own best, u don’t have to be worried za’a nemo.” “Ok” kawai Abeed yace yana kashe wayar, zuciyarsa a cunkushe babu daɗi, har farkar tambayar Dr Adyan yake yaji yace masa ba wani labari. parking yay kana ya fito bayan ya sanya maras har office ɗin Dr Siya ya shiga… Dr Siya yace “me zakai da allurar kwana biyu Mutum yana bacci?” Haɗe fuska Abeed yay yace “stop asking too much” Dr Siya yace “Ok, bari na rubutu maka akwai a pharmacy idan akai allurar mutum zai kai kwana uku har huɗu yana bacci ba zai fahimci komai ba” rubuta masa yay kana yaje pharmacy ya siya, daga nan ya nufi hotel ba. Misalin 11 na safe jirgin su Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas da Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas ya ɗaga zuwa Nigeria.