ZAIN ABEED 5
Masarautar Zahel.
Tsananin Wahala ya sanya Sairah ko gabanta bata gani, tayi kuka ta kira sunan twin babu adadi, hakan yasa ta fara tafiya ba tare data san inda take zuwa ba, har ta iso ƙofar shiga Masarautar Zahel. Daga can taji ance “Kamar baƙuwa ce?” Gimbiya Noro wacce take cikin keken sarautar ta dakatar da kuyanginta, tare da masu izinin sauke ta, a wahale suka sauke keken da yake wuyansu, Kallon Tsaf Gimbiya Noro tayi mata tana ƙara ware idanunta, gabanta ne ya faɗi kanta ya shiga sarawa, da ɗan sauri ta shafa cikinta, can tace “ku kirata” Wata Kuyanga ta ƙarasa Wajan Sairah wacce take shirin faɗuwa, hannunta tasa ta shiga janta wata ƙyakkyawar tsawa Gimbiya Noro tayiwa kuyangar hakan yasa ta daina jan Sairah wacce bata gane komai, tana zuwa Gimbiya Noro ta kama hannun Sairah tare da shigar da ita cikin keken, hakan yasa wata Amintacciyar kuyangar ta tace “Abin bauta ya taimake ki, amma hakan ya saɓa dokar masarautar Zahel” Gimbiya Noro tace “na sani, ki tabbatar wannan mganar bata isa wajan Mabus ba, zan ajjiye ta a waje na akwai amfanin da Zatai min” tana faɗin hakan suka ɗaga keken zuwa cikin Masarautar daman ta fita shan iska ne a lambun Kan’an. Mabus na zaune yace “Ba’a fito da sanyin idaniya ta bane? Dodo ne zai sanya mata albarka” Wani dogari yace “Ana shirya ta ne” Mabus yace “tsoro nake kada Dodo ya buƙaci jininta a yanzu, domin ina jin ta a ƙoƙon zuciyata, wai ashe daman haka ake jin Soyayyar, fuskarta kaɗai ta isa tasa na samu nutsuwa, kamar Abin bauta yay min zalunci daya sanya naji ina son wata ƙabilar ba ƙabilar Zahel ba, maza jeka tawo min da ita” dogarin ya koma wani sashe inda a nan ne aka ajjiye Sara, tana zaune kan wata kujera an dasa mata madubi a gabanta, wani irin kayan ado ake sanya mata na gwala-gwalai, idanunta sunyi jajir kuma sam ba kuka tayi ba, kawai jarumta ce, fuskarta babu walwala sam, tunda tazo ƙala bata ce ba da idanu kawai take kallon kowa, matar dake shirya ta tace “Abin bauta ya saka maki jarumta yake Sarauniyar Zahel ta gobe tashi muje” ta faɗa tana kama hannunta, miƙewa tayi tsaye suka fita waje, kamar Mabus zai hauka haka yaji, gaba ɗaya wajan Dodo sukai, suna zuwa wajan ya ɗauki wata girgiza da ƙara can suka ji ance “Kada a bari ta ƙara yin Sallah…..