ZAIN ABEED 7

Lokacin da Abeed ya isa Zahel dare da riga da yayi nisa, amma bisa tarin Mamaki sa, mutane ne ko ta ina kamar kasuwa ake ci a wannan daran, he was so surprised da ganin hakan he never sow something like that a all his life nasa, ajjiyar zuciya ya sauke trying to control his self, yanayar kuma da tayi masa yawa ne kuma ya sanya ciwon kasa motsawa, gashi bashi da wani medicine wanda zai iya kare kansa ga ciwon kan, iska ya fesar ta cikin bakinsa, a hankali ya zura dukkan hannunsu cikin sumar kansa ya shiga hargitsawa, he just wanted to pretend. Bayan ya gama baza sumar tasa, ya ɗan zuge glass motar, ware manyan idanunsa yay ganin gaba ɗaya babu kayan arziƙi a jikinsu, and idan har ya fita haka akwai prblm, cikin gajiya wa da al’amuran garin ya buɗe baki cikin cool voice nasa yace “you’re mad Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas, ka kawo kanka halaka..” kayan jikinsa ya kalla yaga wani black ɗin yard ne mai taushi, rigar jikinsa ya cire tare da yaga ta, kana a hankali kamar mai tsoron taɓa jikinsa ya zame wandon kayan, ya naɗa rigar a waist nasa, in few minutes yay shiga irin nasu, slowly kuma ya fito daga motar can nesa yadda ba za’a gane sa ba, ya ɗauki wata ƙaramar Camera ya saka a jikin wata ƙaramar necklace daya sanya, wacce zata iya masa all recording na abinda yake buƙata. Cikin nutsuwa yake tafiya, nutsuwar sa na iya bayyana da waye shi, domin duk yadda yakai da ɓoye Asalinsa kallo guda zakai masa kasan cewa ya haɗaka jini da sarauta. Cikin kasuwar garin ya shiga yana ɗan taɓe baki fuskarsa babu walwala sam, ga wani wari da hancinsa yake jiyo masa, deep down na zuciyarsa sunayen Allah kawai yake kira, ga wata faɗuwar gaba wacce rabonsa da ita tun shekarun da suka gabata… Wani dattijo ya gani can zaune waje guda, ji yay ya samu gamsuwa da dattijon wajansa ya ƙarasa, har zai masa sallama sai kuma yay shiru, Dattijon ya ƙurawa Abeed idanu kafin yace “Abin bauta ya taimake ka…” Wani irin runtse idanu Abeed, nan take jikinsa ya fara rawa amma ya daure can yace “Ina son shiga.” Shiru yay domin sam bai san abinda zai ce ba, fuskantar hakan yasa Dattijon faɗin “Wannan lokacin kasuwa ne, gobe kuma ake bikin addu’ar bokaye” a sanyaye Abeed yace “biki? Boka?” Dattijon yace “ko baka da labari ne? Sarki Mabus shine ya buƙaci hakan domin ƙarawa masarautar Zahel tsaro” gently Abeed ya jinjina kansa yana jin confidence a tattare dashi, kamar ba zai Mgna ba sai kuma yace “da safe kenan?” Dattijon yace “ƙwarai, da safe ne, ko wanne boka zai je da kayan aikinsa yay addu’a, Sannan yaywa sarauniyar Zahel ta gobe addu’a, domin umarnin abin bauta kabas sarki Mabus yake jira da tuni ya kwanta da ita ta zama matarsa” gyara tsaiwa Abeed yay kafin yace “nazo a daidai” Dattijon yace “kamarya?” Fararen idanunsa Abeed ya lumshe kafin ya buɗe yace “ina nufin Nima boka ne, kuma dani za’ai addu’ar, zan shiga cikin Masarautar.” kallon Tsaf Dattijon yay masa kafin yace “kuma ba kai kama da boka ba” ganin kamar zai samu wani bayanan wajan tsohon yasa Abeed ya ɗan tsuguna domin komai a ƙyamace yake yinsa, cikin sauke ajjiyar zuciya Abeed yace “like how?” Dattijon yace “I mean u don’t look like Magician” with much surprised Abeed ya ware idanunsa yana mmkin jin turancin da dattijon yay, cikin ƙasa da murya yace “why are you speaking english? Inside of Hausa ko yare naku?” Dattijon yace “and you too, mene yasa ka shigo Zahel bayan ba ɗan garin bane?” Abeed ya shafa kansa, gaba ɗaya ya takura da wannan maganar can yace “something fishy” Dattijon yace “Of course, ni nan ɗan jarida ne, kamar yadda kazo neman sirri haka nazo, shekaru na, kusan 10 a nan, ban samu abinda nake so ba, na zama bawa a masarautar Zahel, babu wanda ya gane ni musamman da nake baƙar fata, kallo guda nai maka nasan akwai dalilin zuwanka, shiyasa nai saurin keɓe kai na nasan za kazo gareni” Abeed kallon mutumin kawai yake, kafin ya numfasa yace “to! Babu amfanin zuwanka ke nan?” Dattijon yace “haka kake gani? Duk wani information ni nake turawa,ta Ɓoyayyiyar na’ura, abu ɗaya zan faɗa maka ba zaka iya Sarki Mabus ba, da ace wani zaici galaba akansa da nine farko” lumshe idanu Abeed yay kana yace “Oh! Ni tabbacin abinda yake nake son samu, bawai cin galaba akan sa ba” Dattijon yace “idan haka ne, nine nan zan baka, akwai memory guda biyu a waje na, duk recording na abinda yake, kaga no need ka shiga ciki” jinjina kai Abeed yay cike da gamsuwa yana jin gaba ɗaya abin yazo masa da sauƙi, cikin ƙasa da murya yace “Me Sarkin yake haka ne?” Dattijon yace “Duk wani mummunan fashi daza kaji ance nayi shine, haka duk wasu ƴan mata da ake nema a rasa shine yake sace su, kawai dan ya kwanta dasu, yabawa dodo jininsu” Abeed ji yay kansa yana wani irin sarawa, faɗuwar gaba ta riskesa, he just thinking wani abu nada ban, can ƙasan zuciyarsa yace “No! Never” shiru ne ya biyo baya, babu wanda ya a sake cewa komai a cikinsu, can tsohon yace “dole sai dai ka kwana tare dani, asubar fari sai ka ɗauki hanya” jinjina kai kawai Abeed yay, domin baya jin zai iya cewa komai, infact ko bacci ba zai iya ba, he can’t sleep serious, wajan ƙarfe biyu na dare Dattijon ya haɗe kayansa kaf, yaja Abeed zuwa can wani ƙaramin gida bayan gidan Sarautar… Washegari da safe Masarautar Zahel ta cika sosai, sbd bikin addu’ar da Za’ai domin ƙara wa masarautar Zahel tsaro, baka jin komai zai kaɗe kaɗe da raye raye, ta ko’ina bokaye ne suke shigowa cikin Masarautar, ƙarfe 10 daidai Sarki Mabus ya bada umarnin a rufe ƙofar shigowa cikin Zahel. Time ɗin Abeed na tsaye, shida Dattijon yana basa memory, cikin tashin hankali Dattijon yace “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, munyi sake” Abeed ya juya fararen idanunsa alamar “what happened?” Dattijon yace “Shi ke nan, idan ba Allah ne ya rufa maka asiri ba, ka shigo Zahel ke nan, domin an bada umarnin a rufe ƙofar shigowa Zahel, babu kai babu tafiya kuma suna ganin motarka zasu ƙone ta” shiru Abeed yay, shi sam baya damuwa dan ya mutu ko an kashe sa, yasan JAHADI ne, kuma silar hakan sai ya samu NOOR a kabarinsa.. a zuciyarsa yace “what should I do now???…” Dattijon yace “baka da wata mafita kawai, ka shirya matsayin bokan mu shiga cikin Masarautar, akwai wata ƙofar sirri sai ka fita ta wajan” cikin few minutes Dattijon ya shirya Abeed cikin wasu kaya gaba ɗaya kamannin sa suka ɓata, daidai lokacin da ake ƙoƙarin Sanarwa a rufe ƙofar shigowa cikin Masarautar Abeed ya sauko ƙafarsa ta dama ciki, mai rufe ƙofar ya dakata yabi Abeed da wani irin kallo, bai dai ce komai ba, Dattijon ya biyo bayan Abeed kana aka rufe ƙofar.. shigowar Abeed cikin Masarautar yay daidai da lokacin da Sara take zaune akan wata kujerar mai azabar kyau, tun bayan abinda ya faru bata cewa komai, ta manta yadda ake komai, Sallah, azkar, karatun Alkur’ani she forgot everything, ga wani tsoro daya ɗarso a Zuciyarta, yanayinta ya sauya ta koma kamar wata zautacciya. Ji tayi ƙirjinta ya buga, da sauri ta miƙe tsaye tana dame kanta tare da faɗin “Abin bauta kabas ka taimake ni” ta faɗi hakan yana zame wani mayafi da yake jikinta, ya rage daga ita sai wani kaya wanda ya rufe mata kirji zuwa waist nata, ji tayi kamar ana janta zuwa wani waje ana kiran sunanta, fararen ƙafafuwan ta, ta ɗaga ta fara tafiya da ɗan sauri, har ta ƙarasu wata ƙofa data gani a rufe, Cak ta tsaya tana bin ƙofar da kallo tana tunanin ta ina zata buɗe ta. Babban boka ne ya kalli Mabus yace “daidai yanzu ya dace ka kwanta da yarinyar nan, domin samun albarkar abin bauta kabas” miƙewa tsaye Mabus yay yana jin wani irin farin ciki a zuciyarsa, abinda yake kwaɗayin samu yau gashi cikin sauƙi zai samesa, kai tsaye ɓangaren daya ajjiye Sara ya nufa… Sairah ce tsaye tun safe take wajan bayan fitar Gimbiya Noro wajan addu’a, samun kanta tayi da son fita domin shan iska tana son ganin yadda Masarautar Zahel take, wani ƙyalle da yake kanta ta jawo ta rufe fuskarta dashi, cikin sauri ta fito cikin farfajiyar masarautar ta fara tafiya, kanta a ƙasa tana tsaka da tafiyar taji tayi karo da ƙafar mutum, cikin sauri ta ɗaga kanta nan take sukai idanu huɗu da Sarki Mabus, wanda tunda ta shigo masarautar bata taɓa ganinsa ba, Sarki Mabus kuwa mamakin yadda akai ta fito yake, domin a tunaninsa Sara ce, nan kuwa Sairah ce, bai ce mata komai ba ya kama hannunta zuwa sashinsa, yayinda tsoro da fargaba ya hana Sairah cewa komai…. Dattijo ne a gaba sai Abeed suna tafiya da sauri gudun kada su sake makara, gashi hanyar da zasu bi dole ta sashinsa Sarki Mabus ne, cikin ikon Allah har suka ƙaraso sashinsa ba wanda ya gansu, suna ƙoƙarin buɗe wata ƙofa, kamar daga sama haka Abeed yaji saukar muryarta, tana faɗin “Twin.. Twin.. Twin” kalmar da take faɗa ke nan, Zain ya faɗo masa a rai, domin wani lokacin haka yake ce masa “Twin” Cak ya tsaya tare da ɗan juyawa ya kalli Ƙofar, zuciyarsa na tsananin bugawa wacce bai san ko tame bace, Dattijon yace “Babu da lokaci ka taho mutafi, mun kusa ƙara sawa ƙofar” Abeed kamar me neman wani abu na shekara da shekaru haka yake bin ƙofar da Sara take bugawa da kallo, kamar zaibi Dattijo sai kuma ya tsaya, ganin kamar Abeed ba zai taho ba yasa Dattijo ya shiga jansa da ƙarfi, sun kusa kawai ƙofa Sara ta saki wata ƙara tare da faɗin “Twin” Abeed bai san lokacin daya hankaɗe Dattijon ba, cikin sauri ya nufi ƙofar yana zuwa ya sanya ƙafa ya daki ƙofar nan take buɗe tana shirin faɗawa kan Sara yay saurin riƙe wa, a tsugune ya sameta ta tura kanta tsakanin cinyoyinta, gashinta duk ya baje ya rufe mata gefen fuska, wata faɗuwar gaba ce ta ƙara saukarwa Abeed wacce ya daɗe bai samu kansa a ciki ba, cikin sauri ya dafe ƙirjinsa yana faɗin “Ya Salam!” Ya ɗan jima a haka, idanunsa kuma ƙuri a bayan Sara, Sara jin kamar mutum a kanta yasa ta ɗaga jajayen idanunta kai tsaye idanunta ya faɗa cikin na Abeed, cikin sauri Abeed ya janye idanunsa, a lokacin nan wallahi Numfashinsa kusan ɗaukewa yay, he can’t believe abinda yake gani yanzu, juyawa yay har yana shirin faɗuwa da niyyar barin wajan, Ya Rabb, da ƙyar Abeed ya samu ya tsaya da ƙafafuwan sa, saboda wata iriyar rungoma da Sara tayi masa ta baya, tare da kecewa da kuka tana faɗin “Twin” jarumta ya arowa kansa, ya ɗan sanya hannunsa tare da zameta daga jikinsa, sam yaƙi yadda ya ƙara kallonta, Dattijo da yake tsaye yana kallon ikon Allah, domin kallo guda yaywa Sara yasan cewa sato ta akai, da sauri Dattijon yace “maza ɗauko ta, wlh sato ta akai” girgiza kai Abeed yay, yana ja baya abin mmki yana ja baya Sara na ƙara matsawa wajansa, a wannan karan gaba cakumesa tayi tana ɓoye fuskarta a ƙirjinsa tana kuka kamar ranta zai fita, ganin cewa shima a yanzu komai na iya faruwa dashi ya sanya ya hankaɗe Sara daga jikinsa, yana zuwa baƙin ƙofa Dattijon yace “Ai kuwa ina tunanin itace wacce Mabus zai kwanta da ita” Abeed bai tsaya jiran jin abinda Dattijon zai ƙara cewa ba, ya juya wajan Sara da sauri yana zuwa ya ɗaga ta Cak zuwa jikinsa da sauri ta ƙara ƙanƙamesa,shi kuma Dattijon ya buɗe musu ƙofar fita daga cikin Masarautar, a hankali Abeed ya sanya ƙafarsa waje domin barin Masarautar daidai lokacin da zuciyarsa data Sara take bugawa a cikin lokaci guda……