Zee Baby Book 1 Page 3

************
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*Nigeria* karfe shida na yamma Wata jibgegiyar motace fara sal da ita saman babban titin malali cikin nutsuwa yake driving waya manne akunnesa sai murmushi yakeyi cikin amon muryasa mai dadin gaske naji yace” sweet baby kiyi hakuri wlh kukanki na daga mun hankali kiyi shiru ganina fah saman hanya zanzo na ganki shikenen ko OK Oya fito gani na karaso ina Sauri kar lokacin sallah magrib yayi ya fada yana tsinke kiran saboda ya Iso kofar gidan honr yai mai gadi ya bude masa ya danno hancin motar gidan yana parking ta fitowa masha Allah wata kyakyawa na gani baka ce sosai amma tanada kyau amma ba doguwa bace ba kuma bata fiye gajarta ba tanada hanci dede misali da idanuwa dede gwargwado tanada gashi ba laifi bakinta Dan karamine saidai tanada yar kiba kadan agaskiya dai batada makosa tanada kyau yar 23 year tanda faram faram batada daurin kai saide ta fiye sanyin hali batada hayaniya duk da a turai tayi karatun Nurse har tsawon shakara ukku isowa tayi ta bude motar ta shiga da sallama

tana murmushi shima murmushin ya sakar mata ” sweet baby uwar yan rigima ya gajiya bazaki bari ki hutaba kamar bamu hadu da safe ba ya cikin naki da fatan kinsha magungunan da na kawo miki kanta ta sada tana wasa da hannuta ” nifa kinga matsalata dake dagowa tayi Dan tasan halinsa yanzu zaiyi watsi da lamarinta ya tafiyasa Dan Sam bayason shariya ” my Dr yi hakuri ta fada tana kallonsa cikin dauriya Dan kwayar idanusa fusgar mutum sukeyi my Dr na kayi kyau sosai kamar na saceka ta fada cike da kunya ” OK Oya fadamun me kike so kika tisani da kuka sai nazo kuma gani kina wani sunne sunne ko cikinne ? kanta ta kwantar saman kafadarsa tana sabke ajiyar zuciya “sweet babyna menene bakida lfy ne ? ” my Dr na wlh idan nayi awa biyu ban gankaba banajin dadine amma yanzu banajin komai na warke ta fada cikin sanyinta murmushin gefen baki yai ya dagota kanta daga kafadarsa ya kura mata mayatattun idanunsa yanajin mugu mugun sonta da kaunarta na ratsashi Dan tarbiyyarta tayi masa tamkar ba aturai tayi karatu ba ” my mashakurah wlh nima ina sonki nifa na ganki nace kinmun so sai me ki ajiye hankalinki Dr Sardauna nakine ke daya insha Allah kinji sweet babyna idanuta ta lumshe ta daga masa kai kiss ya mata agoshi ” OK Oya shiga ciki kinji an fara kiran sallah kisha magani kinji? kai ta daga fitowa tayi tana daga masa hannu idanuta sun tara kwalla ya gani sairai idan yace ya lallasheta kuka zata saka masa shiyasa yaja motar ya fisgeta da karfi juyawa tayi ta tafi ta nufi cikin gida yana fitowa ya harba motar kan titi yana gudu sosai ya dauki hanyar kofar Marusa lowcos gudu yake shararawa sosai Dan ya samu sallah magarib, lokacin da yazo har an gama sallah honr yayi aka bude masa katoton get din gidan ya danna hancin motar gidan Ana harbar gidan yai parking ya fito gun mai gadi ya nufa agaguce yayi Alwalla ya nufi masallaci, bai fito daga masallaci ba saida akayi isha’i yana fitowa ya shiga bangaransu wow agaskiya ya hadu sosai d’akunane har biyar ukku daga farko biyu acikin wata yar kwana kwanar naga ya karya dakin karshene Nasa ya ciro key aljihunsa ya saka ya bude kofar wani ni’imataccen kamshi ya me fitowa tamkar yanzune akayi anfani da turarukan masha Allah nace saboda haduwar bedroom din wani royal bed makekensa d’akin ba tarkace amma zaka zata dakin amaryane ga wasu lumtsma lumtsuman kujeru na kayan jikinsa ya rage ya shiga toilet Yajima sosai ya fito daure da towel kirjinsa cike yake da gashi yana da fadin kirji sosai duk amunmurde yake tamkar yanacin karfe agaguce ya shirya ko mai bai shafaba yasa wando 3quater ya saka da Riga short ya fesa turare ya gyara sumar kansa tayi luf luf sai shegi take baka sudik wayoyinsa ya kwasa baki daya ya fito cikin kuzarinsa yake tafiya ko kofar bedroom dinsa bai rufeba ya nufi part dinsu ghaisha da sallama ya shigo parlon ghaisha na zaune Nawwara na jikinta yana shigowa ta Mike suna gaishesa yaran parlon hannu ya daga musu ghaisha tace” bokan turai baki ya turo kamar wani yaro zama kusanta ya kwantar da kansa saman cinyarta ashagwabe yace ” ghgaisha nah wlh duk nagaji” sannu Dr Sardauna ai Dole tin safe sai yanzu tausa ta fara masa” yauwa mamana Allah kuwa ciwon jiki nakeyi dariyace ta kamasu Hafeeza ce dariya ta kufce mata khalisat ta zaro idanu ta Mike sadaf ta gudu tun kafin ya dago aikuwa ya zabura zai tashi ghaisha ta rikeshi suna ganin haka suka matso suna bashi hakuri banda hafeeza da khalisat da suka Ari ta kare ghaisha tace”maza ku tashi kusan nayi ai yasan wa tayi dariyar mik’ewa sukayi suka bar parlon baki ya ciza ya kalli ghaisha” yanzu Dan Allah mamana kina kallo khalisat mai zubin nunar rana itada yar iskan yarinyanan sukamin

dariya kawai Dan nama mahaifiyata shagwaba dariyar ta danne ” haba Dr Sardauna khalisat baiwar Allah me take cewa acikin gidanan wlh banda ita akama dariya hafeeza ce ita zaka lakada amma banda khalisat baiwar Allah yarinyar da magana ma ba damunta tayi ba mareniyar Allah Aunty amarya ta fito daga kitchen tana dariya ” Wlh Aunty daurin gindinki dai ta samu Dr mun kabarsu zanyi maganinsu baki ya ciza Dan ya tsara launin azabar da zai musu bayan sun mance da anyi abun danshi baya horo kai tsaye ” Auntymu ki barsu zanyi maganinsu wayar sace ta dauki ringing screen d’in wayar ya kalla Ahmed ya gani mik’ewa yai yayi picking ya Kara a kunnesa ya fice daga parlon akofa suka ci Karo da Daddy murmushi ya masa “ah Dr kaida mutanan Saudia ” Daddy bari na dawo akwai hira ya tafi yana magana Daddyn kansa ya girgiza Dan yasan tambayarce bata masaba ya samu ya sulube masa Dr Sardauna mota naga ya shiga yamata key honr yayi aka bude masa get ya fice daga gidan aguje,

 

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

*Saudi Arabia* bayan sunyi sallahr isha aka fito da abunci Wanda ragone jibgegensa aka gasheshi da dafe dafen abunci irin irin nasu na larabawa Jamal sai baki yake washewa zaune suke akasa saman carpet sun baje baki dayansu suka hadu sunacin abuncin ummi Raiyan sai farin ciki takeyi ta tuno da mijinta da yaranta yan mazan Zee baby na kusan Mahabeer ta tisasa da rigima Dole sai shine yake bata abaki itama nata bashi su manal sai dariya sukeyi ummi dai kai ta girgiza Jamal shifa haushin Mahabeer yakeyi. dan de ba yanda zai yine suna kammalawa mai aiki tazo ta kwashe komai ta gyara gun sukaje suka wanko hannusu aka dawo Ana hira su jannat sai karfe goma suka tafi gida sun rakasu suna dawowa su ukku ita da Mahabeer da Jamal suka tardo majeed kofar gidan ya fito amota yashi gaban Zee baby cikeda rashin kunya ta rike k’ugunta tana girgiza zatayi magana Mahabeer ya riketa ya janyota cikin gida aikuwa kafin kofar ta rufe ya biyosu yana magiya ta sauraresa hararasa Mahabeer yake ransa abace cikin harshen turanci” kai malam kama gabanka tunda bata Sonka karabu mana da ita yau naga jaraba Dama haka kuke da kwawa ya dage sai masifa yake kirtama majeed shiko burinsa Zee baby ta kulasa dadi taji ta rungume Mahabeer tana dariya” yauwa Ahukuyah cimun durin uwarsa tunda ubansa yace baya kaunata na tsaneshi wollah bana sonsa yanzu dadi ya cika Mahabeer janyeta yai jikinsa ya kamo hannu majeed ya ingizashi waje jamal yace” wai kai ina ruwanka da shiga tsakanin masoya ” dallah malam yimun shiru yaja hannuta su shigo parlo sai cika da batswa yakeyi itako dadi takeji sai sangarta take zuba masa jamal na biye dasu ummi Raiyan tace ” Mahabeer wai dama tare kuke sakinsa tayi taje gun ummi ta rumgumeta ” ummi bari kiji rada ta mata akunne ” ah haba ikon Allah Mahabeer yanzu shirmenta zaka biyewa dariya yayi yana Sosa kansa hira sukaci gaba dayi sai karfe daya suka ma ummi sallama

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button