Zee Baby Book 1 Page 4

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Karfe takwas na safe jirginsu ya sabka Egypt sabka da jirgiya yayine ya tashi Mahabeer da ya kananade zee suna shakar barci manne da junansu idanu ya bude cike da mamakin irin baccin da yayi tashinta yayi taki tashi dan sam bacci bai ishetaba bakinsa ya kai kunneta ” my zee,na kitashi mun iso cairo juyan jirgi za’a mana zuwa Nigeria kinji my zeena? Shagwab’e masa tayi tanarke masa tana turo baki ashagwab’e tace” Ahukuhya? ” na’am my zeena ya akayi” shiru tayi tana kallonsa murmushi yai mata ” bacci ko kai ta daga masa, tana lumshe idanunta ganin mutane sun fara fita ya mikar da ita Dole ta tsaya mikewa yayo ya ciro karamar akwatunsu ya gyara mata mayafin abayar ya kama hannuta suma suka sabko dogayan motocinan sai kwasar yan k’asa k’asa takeyi suka shiga aka kaisu inda zasu zauna kafin jirgin da zashi Nigeria ya shirya suna zaune tana manne

Kusansa yayi ta lallabata taci wani Abu taki Dole ya hakura basu wani jimaba sosai ko awa daya basuba suka shiga jirgi yanzuma jirgin na shirin tashi yaga tanason yin amai rumgumota yayi yana bubbuga bayanta ya shiga mata rada akunne” my zeena please karkiyi amai ki daure wlh damuwa nake shiga yanda yake matan cikin ikon Allah taji batajin aman ta dago kanta ta zuba masa shanyayun idanunta tana murmushi tana shafar fuskarsa haka suka kure junansu da ido har jirgin ya nutsa sararin samaniya idanuta ta janye tana dariya ta dora kanta kafadarsa, ana raba abunci akazo kansu lemo kadai ya amsa adan cup yasha itako tace tea Mahabeer ya matsa ata amshi pizza ya bata abaki taci ta koshi ya bata magani saboda jikinta akwai zafi ya kwantar da ita jikinsa ya rufeta da mayafi ba jimawa tayi bacci dan dama ita wuni baccine tunda bata na dare bare yanzu safiyace shima baccin ya daikeshi ya jingina bayansa da kujera

????????????????????????????????????????????????????

karfe shabiyu da rabi na rana jirginsu ya diro garin Kano Mahabeer idanusa biyu jirgi ya sabka ya tashi zee idanu ta bude ” munzu gida fah yanzu sai Katsina murmushi tayi ta shafi fuskarsa mikar da ita yai dan masu sabka har sun sabka yan Kano yan Abuja ne basu fitaba tashi yai ya d’aura mata Niqab dinta ya kama hannuta dayan hannusa, rike da jaka itama tana rike da jaka saida zasu fito wata latijuwa takira Mahabeer dan ita Abuja zata ya dawo ” d’ana gaskiya ka iya rikon mace rayuwar auranku ta burgeni kai da yar balarabiyarka gatadai yarinya karama amma akwai nutsuwa Allah ya sabketa lafiya Allah ya karamuku dankon soyayya Allah yasa mutu ka raba kai da ita yaji dadin Addu’arta cikin farin cikin ya amsa yana godiya, suka sabko kallon gurin take ya burgeta sosai suna

Fitowa ta cire niqab ta tatare abayar ta dauré Mahabeer ya fara mata fada ta rufe jikinta surata duk awaje kar wasu yan iska su kalle masa ita shagwabe masa tayi yayi hakuri zafi takeji yanda ta shagwabe yasa yaji tausayinta maybe ko zafin takeji amma ransa bayason wani yaga kyawunta ya yaba ta lokacin su Daddy sun jima da isowa tarbarsu bayan sunje sun gama sa hannu anga posport dinsu sukaje gun kayansu Mahabeer ya jido ya zubaso cikin abun tura kayan bayan angama aunasu suka fito inda jama’arka ke tsayuwa domin tarbar baki Daddy ne ya fara hangosu ya kirasu Mahabeer yaga yan gidansu su shida ne sukazo sai Nawwara ita karamace Dr Sardauna na hango cikin wani danyan boyal baki mai masifar tsada da kyau ya manna bakin gilashi kan fuskarsa wlh fadin kyawun da Sardauna ya zuba bata lokacine saide fuskarsa ba walwala harda mashakurah nagani taci uban kwalliya ta kece raini agaskiya tayi mutokar yin kyawu tana kusa da masoyinta sai wasu mace da namiji sukam ban sansuba sai ghiasha fuskarta dauke da farin ciki Mahabeer ya nunawa zee baby yan gidansu idanun da zata dago idanusu ya sark’e da juna amma ita bata ganin kwayar idanusa saboda gilashi ranta amutikar bace amma zahiri wani makirin murmushi dauke kan fuskarta ta kauda kanta tace” Auzubillahi minal Shaidanir Rajim Mahabeer ya kalleta yana nuna mata Daddy tana hangosa saboda ta sansa sosai ta pic ta yada Jakarta ta saki hannu Mahabeer ta ruga da gudu tana dariya shima dariya yakeyi Sardauna tsaki yaja ya kauda kansa aransa yace ” Allah rabamu da jaraba gudu take amma gani take kamar an kara mata nisan gurin dariya suke ta mata yada ta zage tana gudu ko ina na jikinta motsi yakeyi masha Allah sai kallonta jama’a suke dan zee ba kyau Bade da sura tana dabda isa gurin Daddy sai kawai ta yanke jiki ta fadi da gudu sukayo kanta Mahabeer ya kira sunanta da karfin gaske “Zainab…. arikice yayi kanta da gudu kafin yazo Daddy har ya dagota amma abin mamaki bata mutsi babu alamar rai jikinta Mahabeer ya karasu ya amsheta yana kirkiza agigice amma bata motsa hankalin Daddy yayi mutikar tashi ya kalli Sardauna da yakema mashakurah masifa akanme zata to indai tana tare dashi karta kuskura taje kwalla tausayin zee ta goge ta sada kanta kasa Daddy haushine ya cikashi yace “dan ubanka zo maza dauki yarinyar muje asibiti mafi kusa ka dubamun lafiyarta idanu Dr Sardauna ya zaro bakinsa na rawa yace” Daddy ni kuma zan dauketa saboda Allah ga Wanda ya kawota nan Daddy bai sake maganaba yaje gun Mahabeer yace ya ajiye Zainab ya tashi baiyi musuba ya ajiyeta yace duk su tafi har mashakurah yace ta biyosu ya kalli Dr Sardauna yace” idan ka cika dan halak karka tabata kabarta ta mutum ka kaimun gawarta Katsina komin dare mu muntafi sai ka kawo mana gawarta yaja tawagarsa ghasha tazo ta dafa Sardauna cikin lallaba kome tacemasa oho kai ya kada yana kallon masoyiyarsa da aka hana tabishi saboda wannan banzar lips dinsa ya ciza da karfi yana kallonsu Mahabeer sai kukan zuci yakeyi kayansu yaje ya turo suka fice mashakurah harda kukanta an rabata da masoyinta bazata amotarsa ba sororo yayi yana gani har suka fice ransa yayi mugun baci ya nufi gunta yana yamutsa fuska ya kalli hannuwansa yaja tsaki sunkuyowa yai ya yaja mata rigarta ya ciccibeta ransa amutikar bace amma sai yaji sakwat kamar ya dauki yar karamar yarinya batada nauyi ko kadan miyau ya zubar ya kara hade face yayi waje da ita shikadai yasan yada yatsara cin uwarta da zai mata da zaran ta farfado….

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button