Zee Baby Book 1 Page 7

????????7*

….kofar d’akin Dr Sardauna ya murda ya shiga da sallama ya fito daga wanka kenan daure da towel yana goge jikinsa ya amsa sallamar Mahabeer ya iso kusansa” Faisal meyasa baka tausayin Zainab yarinya cefa saida lallaba ba dukaba wlh bata da lfy tunda muka baro Saudia zazzabi take da amai amma kamata duka ko yaya take fah yar uwarka ce jinin kace bakada maraba da ita gata marainiya tunda Mahabeer ya fara magana Dr Sardauna bai kallesa ba murdaddan jikinsa ya shiga gogewa ya bude wardrobe ya ciro jallabiya fara sai kamshi take zubawa tamkar yanzu ya fesa mata turare ya saka jikinsa yaje gaban dressing mirror ya taje gashinsa Wanda yake kwance luf tamkar ka kitsa Dan Tara gashi yake tamkar yada indaiwa sukeyi ya dauki turaransa mai masifar kamshi da tsada ya fesa wlh zakace balarabene sak bai shafa mai ba” Faisal dakai fah nake magana? duk da yaji zafin abin da Mahabeer yamasa ga Wanda zee ta masa, ya juyo fuskarta dauke da murmushi ” sorry my brother bazan karaba

ni nafita ma harakarta sai kayi kokarin hanata karta kuskura tashiga sabgata,nima ok? ” insha Allah bata shiga ba amma ai kiné take tsoro ya zakace bazaka tsawatar mataba? baice komaiba ya dauki dadduma ya shimfida ya tayar da sallah la’asar har ya gama Mahabeer Na tsaye dan ya fahimci Sardauna yaji haushin abunda yamasa yana gamawa ya Mike wayarsa ta dauki ringing suna Daddy ya gani ya dauka yai picking ya kara akunnesa yana kallon Mahabeer ya daga masa gira ” hello Daddy” dan uwaka zo yanzu ina parlo kitt ya kashe wayar ” my brother karana takai muku ko? Hannusa Mahabeer ya kama suka fito suka nufi part d’insu Daddy da sallama suka shigo parlon zee baby na jikin Daddy tana matsar kwalla kusan Daddy ya zauna ” Daddy gani? ” meyasa da nace karka tabamun momy ka doketa momy wani irin duka ya miki? ” Ammin wlh bankaremun hannuwa yayi ya daureni a karfan gadon hospital ya rika harbani wai sai yaga bayana wai ni annoba ce ya makoremun wuya saida na suma baci ba sha haka ya barni har likintan abonkinsa saida yamun kuka saboda tausayi tunda ta fara magana Dr Sardauna bai dagoba ya kalleta har takai karshen maganar tana kuka kowa ya tausaya mata Daddy ya dagata ” ke Hafeeza maza kuje tayi wanka ta canza kaya tayi sallah tazo tafadi abun da takeson ci ko wani irine yanzu za’a nemoshi momy kuje kiyi wanka nine zan rama miki karki damu dariya tayi cikin farin ciki tabi Hafeeza suka nufi bedroom d’insu cikin fada Daddy ya fara magana” Faisal nine zaka rainawa hankali ka daureta kana bugo saboda zalumci yarinyar da uwarta tabaka Amana k’asakantar da kansa yai “Daddy ayi hakuri bazan sakeba nafita harakarta insha Allah idan tayi ba daidaiba ga Mahabeer

zai tsawatar mata jikin Daddy yayi sanyi marin da yayi niyar masa ya fasa dan yasan Sardauna yanada ladabi ” to naji ka kiyaye ba ruwanka da ita Mahabeer yace “Daddy tafi tsoransa ai Dole sai ana dan tsawatar mata mai ran karfe yace wannan haka yake Daddah tace” ko zata zauna part dinmu? Hauwa tace” da dai ta zauna gun yan matan ghaisha tace” hakan zaifi Aunty amarya tace” gaskiya abarmana kuma fah inaga Dole Faisal ne zai tsawatar mata Mahabeer naga bayason laifinta Daddah dariya sukayi Dr Sardauna tafiyarsa yayi dan maganarsu ko ajikinsa dan yayi Alkawalin baya shiga harakarta mutikar bata shiga tashiba Abu daya zaigani ya horata shaye shaye, suna shiga bedroom khalisat ce ta hada mata ruwan wanka taje tayi wanka tajima sosai kafin ta fito dauré da towel ta goge jikinta tas Hafeeza ta dauko mata Riga da siket na atamfa har taso tayi musu ganin karamin dinkine kuma tanada son kayan atamfa ta amsa, ta saka tayi masifar kyau atamfar ja ce anmata adon fari dinkin Riga da siket mai karmin hannu yayi mata kyau cuf ya mata da yake Hafeeza batada jiki itama amma saide kowa da irin dirinsa hafeeza ta kalleta” sister kinyi kyau sosai? ” shukran bani dadduma nayi sallah shimfida mata tayi tasaka hijab ta tayar da sallah, suna zaune har ta gama ta kalli khalisat ” meye sunanki? ” khalisat yar uwata Hafeeza” ita na sani kece ban saniba ai ke babbace kin grimemu sosai mekike jira bakiyi aureba? kunya ta kama khalisat har hafeeza ma

mik’ewa hafeeza tayi ” sister muje parlo fuska ta yamutsa ” ni kwanciya zanyi ina shantocina ne ko suna gun Ahukhuya? ” gasunan ajere waiwayawa tayi murna ta kamata taje ta bubude komai da ta dauko sunan har kwayoyinta da sirot dinta na kwalba gudun kar su gani yasa bata fidoba duk da tana matse karamar jakarta ce bata ganiba wayarta na ciki ” my khalisat muje parlo muyi hira ko ta fadi tana kallon hafeeza tare suka fito parlon ba kowa duk sun kama gabansu sai ghaisha kade tana waya khalisat taje jikinta ta kwanta zee baby ta tureta” gani yarinya ke katuwa dake ai nima ummi tace dariya hafeeza tayi khalisat tayi murmushi ” my zee zo ki kwanta to ta Mike ta matsa mata tako zauna ta dora kanta cinyar ghaisha tana waya gashin zee ta shiga shafawa zee tana murmushi ummina dawa kukeyin waya nima inaso akiramun ummina dariya su khalisat sukayi yada zee take shagwaba saida ta gama wayar ta kira lumber ummi Raiyan bugo daya ta daga da sallama suka gaisa da ghaisha taba zee baby ” hello ummina wallahi nayi kewarki sosai? ” Zainaba nima nayi kewarki dan Allah ki zauna lafiya da kowa kinji yarinyata? tafada tana goge kwalla” ummina insha Allah ai satine kadai zanyi na dawo gareki murmushi Raiyan tayi ” ina Mahabeer dazu ya kirani mun gaisa har Dr ma baki na tabe ” suna lafiya ummi sun jima sosai suna hira kafin suyi sallama taba gaisha wayar” ummi ina Ahukhuya? ya fita zai dawo kinji kai ta daga sukaci gaba da hirasu

Dr Sardauna bayan ya fita part d’insu ya koma ya canza shiri cikin kananun kaya wanda sukayi masifar kyau ya fito ya nufi gidansu Ahmed dan ya isheshi da kira yazo yamasa Allura zazzabi ke damunsa yana zuwa yayi parking akofar gida ya tura get ya shiga gidan har parlon su Ami ya shiga da sallama tana zaune” Dr ne ince mutumin ya takuraka ko? ” ami babu komai dama da kullum sai nazo indai ba aiki yana ciki ko” yana part dinsa mik’ewa yayi ya mata sallama ya nufi bangaran Ahmed yana parlo sai nishi yakeyi ” dallah can ragon namiji kawai tashi mutafi asibiti zama yayi kusansa ya dafa jikinsa zafi radau ” Dr Wlh inajin jiki fah ” tashi muje dai mik’ewa yai dama jallabiya ce jikinsa suka fito rikeshi yayi suka fita har kofar gida suka shiga mota sa hospital din Dr Sardauna suna zuwa yashiga masa gwaje gwaje ya saka masa drip da ya sha magani ganin magarib ta gabato ya shiga toilet ya dauro Alwalla ya fito ” namijin duniya na tafi masallaci kai ya daga masa yana mamakin tsokanar da Sardauna yake masa yau ba shegen miskilancin sa, tunda ya tafi bai dawoba saida akayi sallahr isha’i ya dawo har lokacin drip din bata kareba ya zauna ya kira mashakurah suna hira su ta soyayya sai shagwaba take zuba masa yana lallabata” sweet baby wlh inaso na ganki amma agajiye nake yanzu ina komawa gida sai bacci ” karka damu Dr nima inason ganinka amma nafi bukatar ka huta na ajiye shagwabar ” ok thanks sweet bye ya tsinke Kiran Ahmed ya zuba masa idanu” ni fah Dr naga kamar son da kukewa juna yayi yawa ku ragema yan baya mana banza yamasa ya Mike ya karawa, drip d’in gudu minti biyar ta gama yacire masa, ” malam ina magana fah? ” banda lokacin ka ” to naji wai naga da araga mana maguguna ya hada masa” Oya mutafi

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button