Zee Baby Book 1 Page 7

tunda kaji sauki Dole ka rainamun wayo fitowa sukayi Dr Sardauna sai gaishesa ake yana amsawa sama sama Dan bacci yakeji ga baisha sigari ba tunda ya dawo daga kano, ko amota iskacin Ahmed yayi tama Sardauna amma bai ko kallesaba bare yasamu arzikin magana har suka iso kofar gidansu Ahmed ya fito ” Dr namu sai gobe idan na gama wartsakewa zanzo nama kanwarmu sanu da zuwa baimasa maganaba yaja motarsa ya tafi Dan lokaci yaja karfe kusan tara gudu yayi sosai yana zuwa yayi honr aka bude masa get ya shige parking space ya shiga ya faka yana fitowa part d’insu ghaisha ya shiga da sallama ya shigo parlon duk su hallara Ana hira zee baby na kusan Mahabeer zaune sai sangarta take zuba masa dannkwayoyin da taje yanzu taciyo aboe sun fara mata aiki shiko sa lallabata yakeyi su Daddy namusu dariya kusan Daddy ya zauna ya gaishesu ” Dr Ashe baka gidan” wlh Daddy Ahmed ne ba lafiya muna hospital amma yanzu da sauki tunda taji shine danma karta kallesa ta boye kanta jikin Mahabeer dhiko baisan Allah yayi ruwantaba ghaisha tace” ayya Allah bashi lafiya Ashe shiyasa yau bai lekoba tashi kaci abunci tunda ya shigo khalisat ta zuba masa

idanu tana kallonsa amma ba Wanda ya lora da hakan dagowar da zaiyi karaf ya kamata tana kallonsa wata uwar harara ya zabga mata ” ke ni sa’ankine ko salon raini ku tsare babba da idanu ya fada yana wucewa hafeeza dariyarta ta boye Nawwara ta bishi gun cin abuncin khalisat taji kunya duk da ba Wanda ya kawo aka da itace sai aunty amarya wani mugun kallo ta watsa mata tashi tayi sum sum tabar gun Daddy basu luraba don hira suke da ghaisha akan zee baby itako zee saboda daukar magana dan ta kuntatawa Dr yaki cin abuncin ya kwana da yunwa ta kalli Mahabeer ” Ahukhuya yunwa nakeji muje kabani abunci mik’ewa yayi ya kama hannuta suka nufo kan dining din Daddy yaji dadin yada Mahabeer ke kula da zee wani tunani ya darsu azuciyarsa tunda dama sunyi sunyi dashi ya fito da mata kullum sai yace abashi lokaci Dr yana cikin hadawa kansa abunci suka iso yaja mata kujera ta zauna shima ya zauna ” Dr ya jikin Ahmed? ” Alhmdllh bro bai sake magana ba sanin ba lalle ya sake kulashiba yasa yaja bakinsa gum ya hadawa zee baby abuncin ashagwab’e tace” Ahukhuya bani abaki Dole ya bata abaki haushi ya cikata ganin Dr yaki ko kallonsa yanacin abuncinsa anutse shida Nawwara tana masa surutu kai kadai yake daga mata zee bakin cikin abuncin da yakeci take so take ya kwana da yunwa tarasa me zata masa gashidai atsorace take da yanayinsa tunda taga Mahabeer dinma shayinsa yakeyi burinta ya kwana da yunwa mik’ewa tayi dan ta fara jin juwa Mahabeer ya kalleta ” ina kuma zaki kinacin abunci? ” wayyo Akhuya cikina ciwo wayyo zan mutu tayi luuu zata fadi da sauri Mahabeer ya tarota su Daddy sukayo kansu Dr Sardauna ko gezau baiba kallonsu ma baiba Daddy yace” Faisal maza bari cin abuncin zo dubata ciwon ciki ai Dole sauyin ruwane ransa adagule ya Mike amma bai nuna azahiriba ” Daddy ai saidai muje hospital sai agwada ta ko? ” eh maza kamata ku tafi ” bro kaimun ita mota bari na dauko abu adaki Mahabeer hankalinsa

atashe yake ganin idanuwanta sun rufe numfashi daket ya dauketa yai waje da ita ghaisha kamar tayi kuka tace” yarinya tunda ta diro kasarmu babu lafiya baiwar Allah mungude ma Allah da mukeda doctor agida Daddy yace” ko zamu bisune sai ga Sardauna ya shigo” haba Daddy tunda ina tare da ita babu matsala yanzu zan dubata mu dawo ba komiba ne sai canjin ruwa Daddy yace” Allah yama Abarka ya amsa da “Amin yana fucewa lokacin da yazo Mahabeer na zaune da ita cikin mota agidan baya sai firfita yake mata ya shigo motar ” Dr tare zamu ko nabarku? ” my brother duk yada kayi ka zauna kawai muje tare inaga kamar idan taga idanunka bazata tsaya adubata ba amma idan bataga idanun saniba zaifi ” eh kuma hakane kwantar da ita yayi tanajin zai fita ta rukoshi jikinta duk ya saki hankalinta atashe don tanajin tsoron daga ita sai Sardauna ” Akhuya na warke kaini parlo murmushin jin dadi yayi” to mukoma ciki Sardauna ya kalli mahabeer ” my brother meyasa kakeso ka maida kanka wani lusari mace ta juyaka yanzu kana ganinta cikin wannan halin sai kukoma ba’a duba lafiyartaba ” sorry Dr wlh farinciki nakeyi ta farka my zee yi hakuri adubaki yanzu zaku dawo bai jiraba tayi magana ya saketa ya rufo kofar hankalinta idan yayi dubu ya tashi kafin tayi wani yunkuri Dr yaja motor da karfi yake honr aka bude masa get ya fice aguje ya harba motar kan titi wani irin gudu yake shararawa wayoyin sa har biyu sai ringing suke amma bai dagaba hankalin zee baby ya tashi amma sai ta dake taki fito da tsoronta cikin tsiwa tace” Dr Malam kayi driving asannu ko bakaga banida lafiya ba? iskar da ta debota ma bai ganiba lips d’insa kawai yake cizawa dan yagama yanke hukuncin gobe ko atiti baza taresaba bare agida don ya gano nufinta abuncin da yake cine bataso cikin lokaci kalilan suka shigo cikin hospital din honr yayi aka bude masa get ya shigo da motar yana parking yaga motar gidansu mashakurah wayarsa ya duba yaga mahaifintane da sauri ya bude motar ya fito bai kalletaba yace ta fito kin fita tayi ya nufi gun motar yaga tafito mahaifiyarta na rike da ita tana matse baki gunsu ya isa” mama sannu ku cikine? ” eh muna ta kiranka” to mushiga daga ciki hannu mashakurah ya kama su na biye dashi zee ta bude motar ta biyosu suna shiga suka zauna nan reception shikuma ya nufi wani hadaddan room da ita zee da ta Iso ko taka iyayan mashakurah bata biba da kallo suka bita sunga dai barabiyace amma ko mayafi babu jikinta gashinta asake har tsakiyar bayanta dinkinbya kamata kuma sunga daga motar Dr Sardauna ta fito mama tace ” ikon Allah wannan ko itace wacce su mashakurah sukaje tarota Kano Alhaji Ma’aruf yace” ba mamaki bakiga tsabar kamar da take da Dr taba ta tura kofar ta shiga yana cikin duba mashakurah dan kuka take masa yada yake danna mata ciki Dole ya dan rumgumota yana lallabata yana dubata idanu zee baby ta zaro da harshan larabci tace” kai Allah ya kamaka Dr Sardauna wallahi sai na fadawa Daddy isakanci kakeyi da mata a Mustashfar ba aiki ne yake kawoka ba da sauri ya juyo da kansa ya kalleta ransa yayi mugun baci ya saki mashakurah zai tashi da sauri ta rikeshi tana girgiza masa kai fisge hannusa yayi ” sweet baby yi hakuri bari na fitar da ita kinsan batada hankali inaso na dubaki anutse, nufo gun zee aguje ta ida shigowa tayi gun mashakurah ta labe bayanta” Allah bazan fitaba hannunta ta dora bayan mashakurah ta mintsineta da karfi saida mashakurah ta zabura tasaki kara dan taji zafi sosai kamar tayanki naman bayanta taji akan idanun Dr Sardauna idanu ya zaro sauri ya kara “ke dubbah tuleliya banza iskancine ya kawoki Mustashfar ko Allah ya tona muku asiri yana isowa ya damki wuyanta ya mikar da ita tsaye ya kifa mata mari ya kamo gashinta da karfi ya murda ya bankare mata hannuwa baya saida sukayi kara wani irin fitsari taji ya kamata dan azaba da gashin kanta ya jata yayi kofa da ita tayi mugun tsorata da yanayin sa ga azabar zafin da takeji sai ihu takeyi ” wayyo zai kasheni wai ba kowane mashakurah ce tasaki kara saboda cikinta ya murda baisan lokacin da ya wurgar da zee ba yayi kanta da gudu…….

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button