Zee Baby Book 1 Page 9

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Washe gari sai karfe shida ghaisha ta tasheta tayi sallah dan itama amakare ta farka hijab ta bata, ta saka ta fito ta nufi d’akinsu sai baccinsu sukeyi bayan sunyi sallah wanka ta shiga tayi ta dauro Alwalla ta fito doguwar Riga tasa ta saka hijab ta tayar da sallah tana gamawa ta cire doguwar rigar ta saka karama, ta Haye gado dan bacci takeji sosai bata jimaba ya kwasheta tin bayan da Dr Sardauna yai sallah Asubah Kenan aka kirasa, an kawo wata baiwar Allah tana matse tiyata ce akwai matsala yazo da kansa bacci a idanusa haka ya shirya agagauce cikin blue Suit, Wanda ba karamun kyau yayi ba duk bai tsaya gyara sumarsa ba ya fito A Sardauna sa turare ya fesa, ya fice ko part d’in iyayansa bai jeba dan ya tafi da niyar yana gama tiyatar zai dawo gida, saide fah yaci walaha Gun yima matar aikin wasu irin ruwa a cikin wata fata atare abun shi kansa ya basa tsoro amma cikin hukuncin Allah ancire duka shiyasa da yagama ya shiga duba sauran marasa lafiya kofa kofa yara yana musu wasa abinda yasa Kenan Dr Sardauna yakeda farin jini gun duk Wanda za’a kawo da sunan maras lafiya ne ko dan jinya Sardauna bai samu zamaba sai karfe 12:am yasamu ya bude Office d’insa ya shiga kamshin dadi ya bugi hancinsa ya lumshe idanu saman lumtsumemiyar kujera teburin sa mai tulin takardu yaje ya zauna ya kunna Ac yunwa yakeji waya ya dauka yai dailing din wata number buga daya aka daga ahankali yace ” kawomun tea mai kauri no shi kadai ya tsinke wayar ya dafe kansa dake masa ciwo ba acike minti biyar ba akayi knocking din kofar ya bada izinin shigowa

da sallama ya shigo ya amsa ” Yallabai barka da ranar ya beka masa ya amsa” thanks ” shikena bakason komai? kai ya daga ficewa yayi yana murmushi wannan doctor nasu akwai kamun kai ahankali ya keshan tea din har ya shanye duka har zufa yakeyi wayarsa ce ta dauki ruri screen d’in wayar ya kalla yana lumlumshe idanu ganin sunan sweet baby na yawo saman screen d’in yasa ya beka Zara zaran hannusa ya dauki wayar yai picking ya kara akunne ” my sweet babyna kinjini shiru ko wlh tun asubah na fito yanzu haka matar nake jira ta farka na tafi gida ykk ya jikinki ko inzone yanzu? ko me tace oho yayi murmushi ” nagode matar Dr sai nazo da yamma ki gaishemun da mama da dady ilove u my sweet babyna murmushi kan fuskarsa ya sakar mata kiss ya tsinke Kiran, sai bayan sallah azuhur matar ta farka Alhmdllh cikin haiyacinta Dr Sardauna yaji dadi sosai yasa aka fito da ita dakin hutu ya kara dubata babu wata matsala anyi aiki cikin nasara karfe biyu da rabi ya baro hospital tafe yake cikin mota driving yake cikin nutsuwa kida kadan kadan na tashi wayarsa ce ta dauki ringing suna Ahmed ya gani dauka yayi ya kara kunne” kai dan rainin hankali tunjiya baka nemeni ba ko? ” dallah can nida ba lafiya ba yanzu ma daga gun aiki na fito banajin jikina nabiyo hospial akace yanzu ka tafi gida wai bazaka dawoba sai gobe” eh nagaji kwanci zanyi na huta ” ganinan zuwa? ” Ok sai kazo ya tsinke wayar number Mahabeer ya kira bugo daya ya daga” hello Dr namu ykk? ” my brother yau bamu haduba tun safe ina hospital ” wlh nima Dr namu ina busy ne ko a kamfani ban hutaba wlh yanzu ma dan naga kaine na dauki Kiran ya aiki? ” Alhmdllh bro gani hanyar gida ” Ok ni sai zuwa karfe shida zan bullo nagode Allah yabar mu tare Dr namu dariya sukasa atare Sardauna ya kates Kiran ya maida hankalinsa yana tuki, har ya ISO gida honr yayi mai gadi ya wamgame masa katon get din gidan ya shige yana parking motar Ahmed na dannowa gidan murmushi yai ya fito ya rufe motar ya jira Ahmed ya ISO parking yayi ya fito rumgume juna sukayi suna dariya Sardauna yace ” Abokina karya kake lafiyar ka lau irin wannan daukan wanka haka dukan wasa yamasa Dr yaja hannusa sukayi cikin gida zazu shiga part dinsu Ahmad ya rikeshi” kai yaro ji mana gun bakuwa zamu nayi mata sannu da zuwa na gaishe da su ghaisha baice komai ya juyo suka nufi part dinsu ghaisha

Da sallam suka shigo parlon amsa musu sukayi yana ganin yayansa Nuhu ya nufi gunsa ya rumgumeshi ” babban yaya amun afuwa kwana biyu ban zaunaba shiyasa ban lekaba tun jiya da nadawo ya gajiya dariya Nuhu yayi ya kara rumgume Sardauna jama’a parlon sai kallonsu suke su Daddah da Aunty hauwa da Maijidda itama yayar Sardauna ce sai zainab kanwar Sardaukar wacce akawa aure yanzu haka tsohon cikine da ita sai kawu saminu kanan Daddy ne masha Allah parlon cike da yan uwa sunzo ma zee baby sannu da zuwa tana jikin Aunty hauwa azaune tanajin sallamarsa ta dago kai ta kallesa ganin ko inda take bai kallaba yana harako kinsa da yayansa yasa ta watsar da lamarinsa taci gaba da zuba musu surutu tana basu labarin saudia Ahmed ko tunda suka shigo da yayi idanu hudu da zee baby yaji wani Abu na masa yawo gabansa na bugawa da mahaukacin karfi yana jinsa cikin wani shauki dan yarinyar tayi masa daga kallo daya ga yanayin shigarta siket ne baki bakin guiwa da Riga mai dan tsayi fara ce tas tazo mata har k’ugunta kirjinta dam acike tamkar su fasa rigar su fito babu abinda ya kara tafiyar dashi irin hips dinta da tillar hancinta da ta k’asan labbanta barimar sai walkiya takeyi gashin kanta har gadon bayanta Wanda ta canza masa kaloli rabi ja rabi grey Nuhu yace ” Dr munzo sannu da zuwar kanwarka Ahmad ya karaso ya gaishesu duk su amsa Daddah tace” Ahmadu ya jiki kusanta ya koma dan tafi kusa da, zee baby ” Daddah ina wuninku jiki da sauki sannu da zuwa nazo ya fada yana nuna zee baby Aunty hauwa tace ” momy ” ana miki magana juyowa tayi ta kalli Ahmed ” wow dan gaye ka hadu kuwa kaima dan uwanmu ne ta daga masa gira dariya duka yan parlon sukayi Nuhu yace ” momy abokin yayanki ne Sardauna juyowa tayi ta kallesu karaf suka hada idanu wani mugun kallon tsana da kyama yamata ya dauke kansa itako tunda suka hada idanu tarasa duk wani karfin jikinta lokaci daya taji wani sanyi na ziyartata kanta ta dauke daga kallonsa tunda shi tun kallon farko yayi watsi da ita yayi kicin kicin nutsuwarta ta tataro tace” Ammin naga yana ruwan yan gidanmu Sardauna baice komai ba bar musu gurinma yai gun ghaisha yaje ya zauna zainab ce kusanta ta gaisheshi ya amsa adakile dan shi haushin masu zauwa ganinta yakeji kansa ta shafa” Dr kaci abunci kuwa ” wlh babu abinda naci mamana mik’ewa tayi ta kama hannusa suka nufi dining Nuhu yace ” ghaisha keki

ke kara shagwaba Sardauna sai kace wani auta baki zee ta tabe taci gaba da sabgarta Ahmed na janta da hira shiko ya fakene yana kallon surata duk shi ba mutumin banza bane amma tunda yaganta yakejin yanayinsa na canzawa tun tana basar dashi har tasaki jikinta suna hirasu tana bashi labarin saudia suna musu dariya dan sosai ya biyewa shirmenta sai dariya yakeyi zuwa tayi ta dauko jallabiya sabowa fara tas mai shegen tsada har aledarta da turare mai azabar kamshi ta kawoma Ahmed yaji dadi sosai yan parlon sai dariya sukeyi khalisat tunda Dr Sardauna ya shigo ta nemi nutsuwarta ta rasa gudun kar ya kamata irin na jiya ta janye jikinta ta nufi bedroom d’insu ta fada saman bed ta fashe da kuka dan abun ya fara damunta ga kishi ya cika mata zuciya saboda zancan za’ayi maganar auransa da mashakurah da taji dasafe Daddy nayi Mahabeer da zee zancan ya dameta kuka takeyi sosai kamar daga sama taji mutum akanta Aunty amaryace wani mugun kallo ta mata batayi magana ta fita tasan ma’anar kallon mik’ewa tayi ta sabko ta bi bayanta Dr Sardauna na gama cin abuncinsa bai tsaya a parlon yana tafe yacewa Ahmed ” kasameni a part d’inmu mik’ewa yayi ya kalli zee ” kanwata zan dawo musha hira kinji dariya tayi ” to yayana ina jiranka dariya yayi ya fice Aunty hauwa tace gaskiya yanada kirki tafi abonkin nasa son mutane kawu saminu yace kowa dai da irin halinsa amma Faisal yanada son mutane harakar da bata shafesa bace baya shiga zee baby bata ce komiba dan ta dauki niyar fita sabgar Sardauna dan batayin Wanda baya yinta shiyasa bata shiga hiraba gun ghaisha ta koma ta kwanta saman cinyarta kanta ta shafa ” momy kinajin yunwa kai ta kirkiza dan sanyi sanyi takeji tun lokacin da sukayi ido hudu da Sardauna jikinta ya saki takejinta wani iri ko hira da tawa Ahmed daurewa ne takeyi ” ko bakida lfy dariya tayi ” ummina sanyine nakeji wlh kara rumgumeta tayi ta rufa mata hijab zainab dariya tayi lalle yar ummi idanuta ta lumshe sama sama take jinsu har bacci ya dauketa Daddah ta Mike ” khadija kinmu kwace ko hafeeza tace daddah bari ma muje part d’inki musha hira ” aikuwa da yafi tunda na rasa hajiya Zainaba takwarata tafiya sukayi Nuhu ma sallama ya musu ya fice dama shi daya yazo kawu saminu ma tafiya yayi tunda bai samu ganin Daddy ba sai matan suna hirasu, lokacin da Ahmed ya biyo Sardauna har ya shige part d’insu har ya tube yana daure da towel yana shirin shiga bathroom ya shigo Dr Sardauna ya kallesa yaganshi da jallabiya da turare yana murmushi yace” Abokina zauna na fito akwai labari mai dadi ya fada yana shigewa bathroom ” wlh nima akwai labarin fito mu fadawa juna ya fada ya kwanciya saman bed d’in Sardauna……..

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button