BAKAR INUWA 5
Typing📲
*_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_*
_{Gara rana dake}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
Episode 5
……….Bada son ran ɗan-azumi ba aka kwashi Raudha zuwa asibiti. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso, inda aka amshi Raudha dake a jigace har batasan inama kanta yake ba zuwa yanzun. Ko sisi Fatima bata da shi, tayi ƙarya ne kawai dan Abbansu ya bari a kawo Raudha asibiti. Tana ganin an amshi Raudha ɗin ta fito ta nufi ofishin Doctor Rufa’i, sai dai anyi rashin sa’a wai baya nan yamaje Ɗillo tun jiya. Dawowa tai inda Mommy da Abban ke tsaye a ƙofar ɗakin da aka shiga da Raudha ɗin. Zama tai itama tabi ayarin ƴan tagumi, a haka har doctor ɗin ya fito yana mai kwantar musu da hankali akan karsu damu komai zai dai-daita, dan zai rubuta musu wasu allurai da zasu sayo, da zaran anma Raudha ɗin inssa ALLAH zata samu nutsuwa. Cikin gamsuwa da rashin damuwa aljihunsa zaiyi tsuwwa ya miƙe yabi doctor ɗin, har yaje ya dawo mommy da Fatisa da Fatima bakinsu bai saɓa ba. Sai da ya dawo da takardar ya mikama Fatisa ɗinne ta ce, “Abba ya zaka bani kuma? Ba cayay a sayo ba?”.
Wani shegen kallo ya watsa mata ita da Fatima fuska a ƙwaɓe. “Kunci bua’ubaku, ƴan bua’uban yara da basa ko ganin mutuncina. Ni kikema magana haka kamar kina a gaban tsohon kwarto”.
Fuska Fatisa ta ƙwaɓe tana ƙunƙuni, zai sake magana Asabe ta katsesu.
“Wai nikam maganin zaku sayo a cetomin yarinya ko tazubar ɗinne ya motsa muku a bainar nasi?. Kai kullum bazaka ja girmanka ga yaran nan ba balle tauna harshenka da baiko da linzami wajen sakin magana”.
“Kar yayi linzamin mana. Banda shegantaka irin tata ba itace tace tanada kuɗi ba shine zata wani tsareni da idanu na rashin ta’ido. ai sai da nace ku bata ɗan libiya amma tace tanada kuɗi ko……”
“Ni dai ya isa da ALLAH. Ke Fatisa anshi kije ki sayo”.
“Mommy nifa wlhy banda ko sisi anan. Nace inada sune danya yarda akawota asibiti. Dan haka sai yaje ya nemo inma baida su, dansu dai likitocin nan bawai batun lamuni suka sani b…..”
Hannu yakai zai kwaɗa mata mari ta tashi ta fita a guje Fatima na take mata baya. Babu ko kunya ya rufa musu baya shima duk da kuwa tsufa ta fara kamashi, ga sigari duk ta gama cinyesa a tsayee….
“Subahanalillahi! Malam ɗan-azumi lafiya kuwa?”.
Cak yaja ya tsaya yana huci saboda jin an ambaci sunansa. Sai kuma duk ya diririce ganin Falalu mai shago tare da Alhaji Maude Dallatu, ya ɗan tura hularsa baya yana ƙaƙaro murmushi. “A’a Falalu kune anan? Ince dai lafiya ko?”.
“Ai kai ya kamata mu tambaya ko lafiya kuwa baba?”.
Cewar Alhaji Maude duk da kuwa zai iya girmar ɗan-azumin ko suyi sa’anni.
Fuska ya marairaice kamar zaiyi kuka, saboda hangen damar dake garesa ta ƙarshe da mafita kenan. “Alhaji wlhy Raudha ce babu lafiya muka kawo asibiti. Shine waccan ja’irar na bata ta sayo magani take shirin min ƙyuya irin nasu na yaran zamani”.
Fatisa tai saurin waro ido waje suna kallon juna ita da Fatima da gumtse bakunan su jin dariya nason kufce musu.
“Ai sai dai haƙuri baba. Inga takardar”.
Alhaji Maude ya sake faɗa a ladabce yana miƙa hannu ya amshi takardar hannun Abban. Kamar bazai bashi ba dai yana ɗan nannoƙewa sai kuma ya miƙa masa. Koda Alhaji Maude ya amsa bai wani tsaya dubawa ba ya kalli Falalu dake ɗauke da kaya niƙi-niƙi alamar duba wani mara lafiyan sukazo ko makamancin hakan. “Falalu ƙarasa ciki ina zuwa”.
“To ranka ya daɗe, amma daka kawo ni sai naje zai fi”.
“No karka damu jeka ciki kawai zanzo yanzun”.
“To a shigo lafiya”.
Falalu ya faɗa cikin girmamawa yana ɗan murmushi.
“Baba ka jirani nan kaima ina zuwa”. Alhaji Maude ya sake faɗa yana tafiya da kallon mal. Ɗan-azumi. Kafinma yace masa wani abu har yayi nisa. Hannu ɗan-azumi ya ɗaga sama yana godema ALLAH daya kawo masa Alhaji Maude a lokacin daya dace, sai dai a ransa kuma ya ƙudira dolene kuɗin da duk zai biya na maganin sai Fatisa tayi kashinsu. Yana nan tsaye ko mintuna goma ba’aiba sai ga Alhaji ya dawo, da taimakon sa sukaje inda aka kwantar da Raudha ɗin. Babu ɓata lokaci doctor ya amsa dan dama su kawai yake jira.
Alhaji Maude na nane da su har kusan awa uku, dan sai da Raudha ta farfaɗo ta koma normal barci da allurar ta sakata sannan yace musu zaije ya dawo zuwa anjima. Godiya suka dinga masa kamar zasu gurfana ƙasa. Yana juya baya Asabe ta warce kuɗin daya mikama Baba tana faɗin. “Ɗan cin rabo, kaci naka zaka hau kan haƙƙina”.
Hannu yakai zai damƙota a fusace. “A gidan wane shege akace rabonki ne? Asabe anya zakiga ANNABI kuwa?”.
“Ai tare da kai zamu gagara ganinsa kwantar da hankalinka jemage maƙi jinin ƙasa sai samaniya..”
Cikin takaicinsu Fatisa tace, “Asibitine fa Mommy. Yanzu dan ALLAH idan ya dawo ya jiku kuma fa? Mudai wlhy kuna zubar mana da mutuncinmu”.
Baki Asabe ta ƙyaɓe. Batare data tanka ba ta zari dubu biyu ta miƙawa baba ta saƙe sauran a zane. Ƙin amsa yayi, sai dubanta da yakeyi cikin takaici da ɓacin rai. “Mikike nufi?”.
“Babu abinda nake Nufi sai haƙƙinka dana baka gashi nan. Tunda ALLAH kaɗai yasan abinda kaci kaima”.
Wata dariyar takaici da tafi kuka ciwo yayi ya ɗauke kansa. “Asabe kina wasa da lamarina wlhy. Ince dai nine silar haɗa auren ko? To wabilahillazi zan iya rusashi a gabanki kuma na bashi wata sai dai ki hangi arziƙin”.
Duk da taji tsoron zancen nasa dan tasan zai iya sai ta balla masa harara. Zatai magana likita daya ƙaraso ya katseta. “Baba zaku iya tafiya da ita babu damuwa”.
Gaba ɗayansu suka juya gareshi, kafinma suce wani abu Fatima da bata tanka musu ba tunda suka fara ta afka ɗakin da Raudhan take Fatisa biye da ita. Asabe ma ɗakin ta juya da niyyar shiga mal. Ɗan-azumi ya samu damar warce kuɗin data saƙe a cikin zani. A wani irin muguwar zabura ta juyo, sai dai kamar walƙiya ya ɓacema idanunta. Ranta yayi ƙololuwar ɓacin da har ma ta kasa bin bayansa balle yin magana har Fatisa da Fatima suka fito riƙe da Raudha. Yini guda harta sake ramewa, sai idanu zuru-zuru ga allurar da akai mata yasa barcin bai gama sakinta ba.
“Mommy mike damunki?”.
Raudha ta faɗa a hankali idonta akan Asabe. Ƙwafa Asaben tayi tana magana cikin ɓacin rai, “Minene kuwa zai dameni idan ba ubanku ba, wanda ƙaddarar rabonku ta zama silar haɗuwata da shi. Wlhy a wannan gaɓar kuwa lallai zan shayar da Dauda zumar mamaki. Yanda yake jinsa tantiri nima tantiriyarce ta gaske, kuma zan tabbatar masa da hakan yau basai gobe ba”.
Dariya Fatima ta ɗanyi dan ita ko’a jikinta. Raudha kam hawayen da suka ciko mata idanu ne suka silalo a hankali. Hannu ta kai ta share da ɗan cije baki saboda kanta dake sara mata.
A haka suka hau mashin ko sisi babu a jikinsu. Sai da sukazo gida Asabe ta shiga ta kawoma mai napep ɗin masifa fal ranta..