Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 5

    Har aka sha ruwa Malam ɗan-azumi bai yarda ya dawo gidansa ba, dan yasan halin Asabe sarai. Ya tabbatar yau duk da azumin dake a bakunansu sai sun tara ƴan kallo a cikin anguwa, shi kuma baya buƙatar hakan tunda yasan shine mara gaskiya, shiyyasa ya zaɓi ƙin dawowa gidan har aka sha ruwa. Yadai samu gasashen naman kazarsa da fura mai sanyi yaci yay ƙat. Ya kuma ɗora da indomie da ƙwai da shayi wajen Bello mai shayi. Sannan ya ɗan zuƙa sigarinsa kara uku. 
   Sai wajen sha ɗaya na dare ya lallaɓo a tunaninsa kowa yayi barci. Sai dai yayi rashin sa'ar cin karo da Asabe dake zaune dakaka tana zaman jiran shigowar tasa. Yanako shigowa tai caraf da rigarsa taci kwalarsa. Tun sunayi iya su har kowa na gidan ya farka. Dama Larai na laɓe tana kallon komai tun farko tana kwasar dariya, tunda taga Asabe zaune taƙi shigewa tasan akwai wata a ƙasa dama, balle itama akwai tsiyar data harbo, dan tun maganar da taji a ɗazun game da Alhaji Maude Dallatu mai son Raudha hankalinta bai kwanta ba, suna fita a gidan itama ta fice.
    Rigimace sosai ta harƙume a tsakaninsu harda doke-doke. Dan sai da maƙwafta suka shigo aka rabasu da ƙyar. Kuka sosai Raudha keyi tamkar numfashinta zai bar gangar jikinta. Dan ko leƙe bata leƙo ba dama tunda aka fara faɗan tana ɗaki kwance. 

         Abu kamar wasa har gabannin asuba wannan faɗa yaƙi rabuwa. Mutane har sun gaji sun koma gidajensu sun barsu. Ƴan gidan kam har yara sun farka dan kowa ya gagara barci. Duk suna a tsakar gida, Raudha ce kawai batako leƙo ba tana lafe a ɗaki tana faman dirzar kuka. Ko sahur ɗin kirki ranar babu wanda yayi a gidan. Kiran sallar asuba yasa Baba Nafi fara  roƙona malam Dauda akan ya fita massallaci shi dan ALLAH ko hakan zai kawo masalaha. Shawararta yasa shi fitar yana faman huci, duk da ba yaune karon farko da suke irin wannan faɗan ba, sai yakejin zafin Asabe a yau fiye da koyaushe. Ji yake tamkar ya saketa ya hutama ransa.

   Koda aka idar da salla maimakon yaƙi dawowa gidan sai shaiɗan ya dinga tunzurasa akan ya shigo yaga ƙarshen haukan Asaben. Yaran kawai ya samu suna kiciniyar alwala a tsakar gida. Dan Baba Nafi da su Fatisa sun lallaɓa Asabe da ƙyar ta shiga ɗaki itama bayan tayi alwala. Tana ɗaki zaune tana rusar kuka ya dawo, dan ko sallar ma haka tayita tana kuka. Wani irin ɗaci da zafin Malam Dauda takeji yau fiye da ko yaushe a rayuwarta.

       “Haba Malam mi kuma ya dawo da kai gidan nan a yanzu?”. Baba Nafi dake tattare kayan wanke-wanke ta faɗa lokacin da malam Ɗan-azumi ke shigowa gidan zuciyarsa tamkar zata kama da wuta. Zuciyar tasa dama a kusa take, dan haka cikin masifa yace, “Na dawone dan naga ƙarshen isakancin Asabe yau a gidan nan!!”.. 
       “Kai ɗin banza daka isa kaga ƙarshen iskancina Dauda. Kaima kasan ni nafi ƙarfin kanwar lasarka, dan ina dai-dai da wandama ya fika balle kai ɗin ƙaramin shegen bariki”.
     Da wani irin rawar jiki malam Dauda ya cacimi taɓaryarsu ta daka yayi kan Asabe gadan-gadan. “Aiko yau zan tabbatar miki da ni babban Shege ne….!”
        Baba Nafi datai saurin shan gabansa ta riƙe taɓaryar da sauri. “Haba Malam waini kam mike damunku yau haka ne? Yanzu akan ƙaramin abu dabai taka kara ya karya ba zance yaƙici yaƙi cinyewa domin ALLAH!”.
      Hankaɗe Baba Nafi yayi, cikin matuƙar sake harzuƙa ya fisgi taɓaryar yana ƙoƙarin sake nufar Asabe da itama ta rarumo kujerarsu ƴar tsugunno ta nufosa, su Fatima suka riƙeta. Sake riƙesa Baba Nafi tayi dan taba duk ta gama cinyesa a tsaye ba wani ƙarfin kirkine da shi ba. Cikin matuƙar sake harzuƙa yake nuna Asabe da ɗan yatsa yana faɗin,
“Kije na sakeki Asabe. Na sakeki saki biyun daya rage tsakanina da ke!! Bana son sake ganin fuskarki, Idan ba hakaba wlhy yau sai na kasheki a gidan nan da hannuna”.
      Da sauri Larai ta shige ɗaki wani irin ɗan karen daɗi na saukar mata a rai da zuciya, har ji take tamkar ta daka tsalle ta dire dan yau burinta ya cika. Itako babu abinda zatace da malam ɗan-kande sai godiya. Gashi ya mata aikin da taketa kashe kuɗi tsahon shekaru a cikin ƙanƙanin lokaci. Gwatsar wayarta da tasha ɗaurin ƙyauraye ta ɗauka ta shiga laluben ƙanwarta Haƙila danta guntsa mata wannan daddaɗan labari haka da farar safiyar nan ta juma’a.

       A tsakar gida kuwa duk yanda Baba Nafi take ƙoƙarin ƙwaɓar Malam ɗan-azumi yaƙi saurarenta sai sake maimaita kalmar saki yake ga Asabe da gaba ɗaya jikinta yay sanyi kuma a lokaci guda. Dan yana ambaton ya saketa duk zafinsa da takeji kuma sai taji ya kau baki ɗaya. Da wani irin sanyin jiki ta saki kujerar hannunta jin hajijiya na neman kadata ƙasa. Riƙota su Fatisa sukayi suma jikin nasu na rawa.
         Raudha dake cikin ɗaki zaune tana karatun Al-qur’ani tai saurin miƙewa tana dafe ƙirji, dan kalmar sakin nan tajita tamkar sukar mashi a ƙahon zuciya. Tuni ta nema kukan da takeyi ta rasa. Da gudu ta fito tsakar gidan, taje gaban Mahaifin nasu ta zube gwiwa a ƙasa tan roƙonsa akan yayi haƙuri karya saki Mommyn su dan ALLAH. Duk hukuncin da yakejin zai mata ita yayi matashi dan ALLAH duk zafinsa zata ɗauka.
     Hankaɗeta yayi cikin rufewar ido yay waje yana cigaba da kunfar baki. Raudha ta miƙe da gudu ta bisa tana kuka amma ko waiwayenta baiyiba………✍️

Tofa yau dai da alama auren zobe ya ɓalle? Ko asabe zata yarda tabar gidane? Duk da kuwa saki uku ne a kanta idan aka tara da guda ɗaya na baya. Shin auren Raudha da Alhaji Maude Dallatu zai yuwu kuwa?. To minenen ma ma’anar BAƘAR INUWAr? Suwaye BAƘAR INUWAr? Mizai biyo baya a gundarin labarin BAƘAR INUWA? Dukan amsoshinku na cikin Littafin BAƘAR INUWA da nakeda tabbacin ya taɓo muku inda ke muku ƙaiƙayi. Karku ɗauka a gidan su Raudha kaɗai cakwakiyar zata ƙare. Sam ba haka bane, akwai wasu rikicin da gidajen a gaba. Sanin alaƙarsu da Littafin BAƘAR INUWA sai ka mallaki naka ankai har ƙarshe da kai. Masoya ba’a fara komai ba, dan kuwa a paidpages ne kawai zaku san minene gundarin labarin BAƘAR INUWA😉⛹🏻‍♀️🥰🥰🙏🏻

Ku kasance da ZAFAFA BIYAR domin karanta daɗaɗan labaransu guda biyar dake tafe da salo na musamman masu ƙayatarwa.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button