Uncategorized

MUSAYAR RUHI 19-20

 *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

               *NA*

      *NPEEDY A AJI* 

 _(MARMIY ZARAH CE)_

“`LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE“`

*1. NAYI RAYUWA DASHI*

*2. SANADIN ACCIDENT*

*3. SAKAYYAR CUTA*

*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*

*5. MUGUN SARTSE*

*6. FURUCI….*

*7. JUYI BIYU*

*8. HAYATUL MAHAYAT*

        AND NOW

“`MUSAYAR RUHI“`

*_____________________________________*

 *????????AINUWA ????RITER’S✍????*

*????SSOCIATION????????*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PG 19 & 20*

*W* ashe gari jirgin farko Hammat yabi yakoma zuciyanshi cike da tsananin 

Quncin hukuncin da aka zartar mashi jiyayi yakara tsanar Hanan cikin zuciyarshi yasha alwashin saitayi nadamar kasan cewa mata agareshi tundaga wannan ranar aka fara gudanar da shirye shirye bikin Hammat da Hanan Hajiya kilishi wato Ammi da Sarki Jabir suna cikin tsanani farincin kasan cewar wannan auran Hajiya kuwa sosai itama takeson auran sa’badin da data nuna bata ‘kaunar Hammat ya auri Hanan din

  

JORDAN

Tunda da wannan ranar hamut yadena shiga harkar hamidat dasafiya tayi yake shiryawa yake fita bai dawowa sai yayi sallah magrib da ishah duk da wannan matakin daya dauka bataji komai ba saima hakan yayi mata dadi sosai saima tabude wani shafin holewa akullun bayan hamut yafita sai abokinshi muhseen yashigo gd suna daukar tsawan lokaci atare hatta nau’ikan abinki girka mai take kala kala shigar banza kuwa yitake sai kace ba matar aure ba acikin ‘yan mata ma sai mara kamun kai Sosai ta sake mashi yauma kamar kullum sunatare da Muhseen taci wata irin kwalliyar qananun kaya sunyi masifar fidda surar jikinta wani irin kallo muhseen yakeyimata sefaman cizan lips dinshi yakeyi fesar da’iska yayi daga bakinshi sannan yafara dacewa 

” Baby gaskiya nifa namatsu na aureki amma inaganin bazan iya jurewaba yakamata musan abunyi ” murmushi Hamidat tasaki tace ” banganeba wane irin abunyi kenan ? ” kamo hannunta yayi yace ” abunyi kamar haka ? Yasumbaci hannun nata rumtse ido tayi sabida yadda taji wani irin yanayi yaziyarci jikinta  ganin haka yasa muhseen sakin wani irin murmushi wanda shine kad’e yasan ma’anarshi sake matse hannun nata yayi yana kashemata jiki da kalamanshi sosai yagane langonta babu zato yajawota jikin shi tafad’o saman qirjinshi rungumeta yayi sosai amma abun mamaki batayi qoqarin hanashiba sema sake lafewa datayi ajikin nashi sake sakin murmushi yayi kusada kunnanta yakawo bakinshi murya qasa qasa yace zanso ace murayu tare ahaka har qarshen rayuwata Hamidat inasonki sosai to amma nagakamar yayanki bazai bani aurankiba  nikuma iyayena bazasu yarda daza’binaba sede idan zamuyi abu 1 hakan zesa subarni na’aure ki kuma cikin farinciki baby kitaimakeni kiyarda musamu mafita ” lumshe  ido Hamidat tayi tace ” sanar dani koma maiye zanyi inde zansamu damar mallakarka matsayin miji kasanfa inasonka sosai ” cizan lips d’inshi yasakeyi akawo na babu adad’i sannan yace ” hanya d’ayace  mukasance dajuna hakan shine zaisa su’amince kinga munriga munzama d’aya zuwa lokacin dole zasuce dake nadace ” jin haka yasa Hamidat d’ago ido takalleshi  kafin tayi magana yace ” karkice komi baby bazan cutar dakeba har abada bazan gujekiba karkiyimin rashin fahimta inasonki fiye da kaina zan’iya baki komi nawa ki’amince baby dan musamu damar mallakar junanmu ” sosai yake sakar mata kalamai ganin kamar tagamsu yasa yafara wayon ta’ba jikinta hakan yabashi nasarar kashemata jiki shed’an kuwa yasamu damar cin nasara akansu wa’iyazubilla Allah katsaremu katsaremana imaninmu amin 

tundaga wannan ranar Muhseen yasamu damar morewa dajikin Hamidat duk wannan abubuwan dasuke aywatarwa  Hamut baidamasaniyar komi hasalima tun ranar farko da Muhseen yazo wajanshi baiko sakeyin koda waya dashiba ashe shi baisaniba yamaye gurbin shi awajan matar shi   

TURKEYA 

Fitowarsu daga lecture kenan wayar Hanan tafarayin ruri cikin sauri tacirota daga cikin jakarta ganin sunan Ammi yasa Hanan saurin d’aya wayar gaidata tayi cikin girmamawa had’ida seseta kanta dagacan ‘bangaran Ammi tace 

” Hanan ina kan hanyar zuwa turkiya gobe in sha Allah ina son ganin auta ta ” wani irin farinciki Hanan taji Wanda yasakata sakin ‘yar qara sosai tanuna murnarta hakan yasa Ammi sakejin dad’i marar misali hakan kuwa akayi washegari Ammi tasauka cikin qasar TURKEYA munar wajan Hanan da Fadila abun ba’ayin magana misalin 10am Ammi tamiqe tanad’e abin sallar datake kai tazauna bakin bed tadubi  Hanan dake riqe da Qur’an tana karatu tace 

” Hanan idan kin ida inasonyin wata muhimmiyar magana dake wadda sanadintane  yakawoni qasarnan ” rufe Qur’an d’in Hanan tayi tamaidashi mazauninshi sannan tadawo kwanciya tayi tad’aura kanta saman cinyar Ammi tanasakin ajiyar zuciya cikin sanyin muryarta tace 

” Allah yasa balefi nayiba Ammi ? ” murmushi Ammi tasakar mata  tace ” haba Hanan babu lefin dakikayimin kuma ayke bakya lefi Hanan inaso kifahimceni sosai kuma kiji abinda zansanar dake  da kunnan basira Hanan nanda kwanaki kad’an za’ayi auranku keda Husain h…..” wunqurawa tayi zatamiqe Ammi tayi saurin cewa ” a a Hanan kisaurareni tukun a yau zansanar dake wani sirri wanda banso kisanshiba har abada amma ayanzu yazama dolene kisani Hanan Hanan Hanan banice nahaifekiba ” dukda hanata da Ammi tayi akan kartatashi ay batasan lokacin data tashi zauneba rungumota Ammi tayi cikin taushin murya tace ” kwantar dahankalinki Hanan har abada ni mahaifiyarkice sabida banaso kizauna qarqashin wata uwar dan gudun cutarmin dake yasa mukayanke hukuncin had’aku aure keda yayanki Hammat nanda wata 1 babu abinda zai ta’ba karatunki kinji Hanan banaso kidauki wannan abun takura agareki sannan kikwantar da hankalinki in sha Allah hakan alkairine agareki  bazan cutar dakeba har abada Hanan ” 

Sosai kuka yaciqarfin Hanan cikin kuka tace ” Ammi koda banta’ba ganinkiba kin’isa kisani nayi balle ke uwace agareni har abada kodawasa banajin zakicutar dani amma Ammi suwayene iyayena ? ” ajiyar zuciya Ammi tasauke tace  ” nima banida wannan amsar Hanan dalilin auranki da Hussain yasa nasanar dake badan hakaba har abada bazakisan wannan sirrinba ” cikin kuka Hanan tace ” kenan Ammi ni banida iy…… saurin rufe mata baki Ammi tayi tace ” karkice komi Hanan bari kuyi waya da Husain din kafin Hanan tace komi Ammi tadanna kiran layin Hammat sanar dashi tayi zasuyi waya da Hanan babu yadda zaiyi amma wani irin takaici yaji miqama Hanan wayar Ammi tayi sannan tafitar daga bedroom tana fita parlour tahangi Fadila zaune saman cushion tana kallon TV zama Ammi tayi sukacigaba dayin hira 

Cikin sanyin murya Hanan tayi sallama jin muryar Hanan yasa Hammat jan tsaki tun kafin tasakecewa komi yace ” ke inaso kisaurareni dakyau kiyi gaggawar sanar ma Ammi cewa bakison wannan auran idan kikaqi to wallahi zakiyi nadama ” daga haka yakashe wayar shi wani irin kuka Hanan taji yasake tasomata cikin kuka tashiga cewa ” nashiga uku ni Hanan yayazanyi darayuwata tabbas baqinciki zaiyi ajalina 

Marmyn Zarah

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button