KWARATA 21

Cikin farin ciki muka isa bakin shagonmu wanda yasha fenti kuma aka gwagwaɗa masa tambarin kwarata , tsayuwarmu da fitowarmu shine ya jawo hankalin al’umma masu wuce da wanda suke zaune saboda munzo da sabuwar shiga mai matuƙar bada al’ajabi a karon farko da ta zama abin kallo ga jama’an gari…
Bakin shago mu mata muka koma muka jera layi amma babu wacce ta zauna tsaye muke , Nana da Karima suna daga gefe suna kallon ikon Allah ,
Waya Hafsat ta fiddo ta fara latse latse daga baya kuma sai naga ta koma gefe guda tana waya , ta ɗauki tsawon lokaci bata gama wayar ba haka nan kawai naji na tsargu da wayar , bayan ta gama sai ta goge number data kira…
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9704, ‘t’: ‘160 by 600’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Ƙurawa Hafsa ido nayi harsai data kama kanta , tabbas akwai cuta a tare da rayuwar Hafsa akwai abinda take shiryawa ko kuma take so ta aikata idan kuwa na ganota da wani laifi na cin amana babu abinda zai hana na tona mata asiri,
Yana gama waya da Hafsa ya buɗe saƙon da tace ta turo mishi , ɗan soɓaro baki yayi irin na sakatattun “ya “ya sannan ya cire vidio ya ɓoyeshi a gellery vault bayan ya gama gani…
Saman kujera ya zauna ya saka takalmi har yanzu bakinshi a soɓare yake , saida ya gama sannan ya kalli Al ‘ Ameen yace mu fara zuwa ta wurin An manta sannan mu wuce don Allah ,
Al ‘ Ameen yace mai gida da Allah ka fita hanyar yarinyar nan , murmushin Dikko yayi sannan yace wallahi sai anje idan baza kuje ba sai ku jirani ina dawowa , yana faɗin haka yayi gaba , Al ‘ Ameen biyo bayanshi yayi ƙaramin yaron daya girma kawai zai riƙa juya su dandai suna ƙasansu…
Da sauri ya wuce Dikko ya buɗe mota , ɗan ɓata rai Dikko yayi sannan ya shiga ya zauna tare da kwantar da bayanshi saman lallausan kujeran motar , wayarshi ya ciro yayi mata kyakkyawan riƙo da duka hannayen shi biyu , sannan ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya yake faɗawa Hafsat yana zuwa yanzu babu daɗe wa zaizo mata bankwana !
Wata irin kururuwa Hafsa tayi ta farin ciki sannan ta koma motarta da gudu , ƙara barbaɗa powder tayi tare da ƙara shafa turare sosai , sannan ta gyara ɗaurin kallabinta ta fito…
Kallon mamaki nake ta bin Hafsa dashi anya yarinyar nan bazan zameta daga harkata ba ? Tafiyar nan kuwa zata tafi kodai in fita inyi harkata ni ɗaya ? Ina wannan tunanin zuƙa zuƙan motocin Dikko sukayi parking a ƙofar shagon mu…
Cikin rawar kai Hafsa ta tashi tayi wurin motar Dikko , ƙafarshi ya ɗora saman murfin motar , kafin Hafsa ta isa wurin ya zura hannunshi aljihu ya ciro cingom , a daidai lokacin da Hafsat ta isa wurin motar , ko inda take bai kalla ba ya cire cingom inshi a cikin takaddar shi ,
Tahowa ya farayi zuwa wurina tare da ɗora cingom in saman “yan yatsunshi na hannun haggu ya daki tafin hannunshi na haggu da hannun shi na dama , buɗe bakishi yayi cingom in yayi tsalle ya shige ,
Ɗan tsuke bakinshi yayi kamar zaiyi kiss sannan ya lumshe idanuwanshi tare da nuna yanayin kamar abin harin sumbatar nashi yana kusa dashi , muah ya saki kiss a daidai lokacin daya tsaya gabana yaja kujerar rober ya zauna , sai yanzu ya fara tauna cingom ɗin cikin izza da nuna shi wani isashshe ne , ɗago ƙafarshi yayi ya biyo da ita ta saitin fuskata kamar zai takamin fuska naɗan ja baya , murmushi yayi tare da ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya :•
Robar ruwa Al ‘ Ameen ya miƙowa Dikko bayan ya zauna , ɓalle murfin robar ruwan yayi yakai bakinshi yana kallona , shan ruwan yayi sannan ya cika bakinshi dashi ya miƙawa Al ‘ Ameen robar ruwan , murmushi yayi da gefen bakinshi sannan ya fara bultso ruwan daga bakinshi suna watsowa saman fuskata…
Ƙoƙarin tashi na farayi dan banda lokacin Dikko a yanzu sai bayan shekarun dana iba , ina ƙoƙarin tashi ya maidar dani ya zaunar da ƙafarshi nayi na tashi na kasa saida ya gama watsa min ruwan sannan na buɗe idona daya cika da hawaye na kalleshi ,
Murmushi yayi sannan yayi magana cikin sigar lallashi haba ke ko an mata komai saurin kuka ke baki san wasa ba ? Karfa ki ɗauki abin da zafi albarka na saka miki , kin zageni tass amma zagin yamin daɗi bayan shekaru biyu idan muka fara farautar juna a ranar zaki gane Dikko ba zakin roba bane , zakin gaske ne farin ciki mafarauta , maganar dana faɗa mishi jiya, cewa zakin roba dana sanin mafarauta, ci gaba yayi dacewa dani dake duk wanda ya fasa , ya jinjina kainshi tare da nunani da hannu ,
Tura kujerar da nake zaune yayi da ƙarfi da bango bai tareni ba babu abinda zai hanani faɗuwa , Al ‘ Ameen ya kira da sauri yazo tare da miƙo mishi wata “yar ƙaramar jaka tashi yayi ya duƙo kusa dani sosai lumfashin shi yana sauka saman jikina , saman jikina ya ɗora tare da cewa ga cingom nan zai isheki amfani daga nan har zuwa lokacin da zamu fara wasa , ɗan taɓe baki yayi tare da kallon wani wuri daban sannan ya juyo ya kalleni da magana zaiyi kawai sai fasa…
Miƙewa yayi ya juya ba tare daya sake cewa komai ba , bayanshi Hafsa tabi saida ya shiga mota ya zauna sannan yasa Al ‘ Ameen yayi rabon kuɗi wa duk wanda muke tare dashi har “yan dabana saida Dikko yasa aka basu kuɗi amma nidai bai bani ba kuma ban damu ba saboda dama ni basu nake jira ba !
Al ‘ Ameen yana gama rabon kuɗi ya koma mota , har yanzu Dikko ni yake kallo gilashin saitin shi Al ‘ Ameen ya ɗage zuwa sama sakamakon da yake ƙasa , bai daina kallona ba har Al ‘ Ameen yaja motar suka tafi ,
Goge fuska ta nayi da hannu na , sannan na buɗe jakar da Dikko ya ajiye a gabana , irin cimgom in da yake amfani dashi ne sai farar takarda da akayi rubutu a samanta , suke nan a cikin “yar jakar , ban buƙatar dubawa sabona nasan gani kawai zanyi bazan iya karantawa ba, kuma babu wanda zan ba ya karanta min saƙon Dikko daga nan har lokacin da zan iya karantawa da rubutawa….
Tunda Dikko yayi min wannan wulaƙancin ban sake magana ba har aka gama raba takardunmu muka koma gida ban sake magana da kowa ba , kuma tunda nayi wanka na shiga ɗaki ban sake fitowa ba saida gari ya waye ‘
Bayan na gama duk abinda nakeyi na fito tsakar gida na zauna saboda ba yau zamu fara fita ba sai an fara kira a waya lokacin zamu tabbatar da cewa tallarmu ta samu karɓuwa a wurin jama’an gari,
Nana na gani riƙe da kwalar rigar mijinta tana zazzaga jikinta irin abin nan da yara keyi idan suna faɗa , zama nayi ba tare dana kalli inda suke ba amma hankali na da kunnuwa na suna wurin su , wallahi sai ka sakeni kalmar da naji ta fito daga bakin Nana kenan kuma har yanzu bata saki rigar mijin ba.
Audu yace ba ƙin sakinki zanyi ba amma sai kin faɗamin abinda nayi miki wanda yasa kike so na sakeki ! Nana tace lallai bama ka da kunya da har kake tambayar abinda kayi , tou na gaji da zaman cida kaina zaman wahala zaman kunci kullin muna can barbaɗe kayanmu a saman kai bama ƙerau bama sabuwar anguwa zama gidan haya , tou wannan aure dai a sahalewa juna uban kowa ya huta…
Daga inda nake zaune nace Audu wai duk meya haɗaku ne wai ? Ku kullum faɗa ke Nana kamar kece kaɗai matar aure a gidan nan ? Duk wadda kika gani da mijinta haƙuri takeyi ko suna wani saɓani basa fitowa tsakar gida ke kullum dake da mijinki kamar abokan faɗa ? Gaskiya ki daina wannan rayuwar kece ƙasan Audu dole sai kin kiyaye idan har kina san ganin daidai a rayuwarki.
Sakar mishi riga kizo kiji wata magana, babu musu ta sake rigar mijinta ta taho wurina, shi kuma Audu fita yayi ba tare daya sake cewa komai ba,
A ƙofar gida kuwa A ` i ce ta tare Audu bayan gaisuwa tace mishi naji shiru ya kamata kayi wani abu don Allah , zama Audu yayi a saman dakali sannan yace ki ƙara haƙuri , murmushi A ` i tayi tare da cewa ba komai Allah ya tsare ya dafa maka akan duk lamuranka , da amin ya amsa sannan ya wuce ita kuma ta shigo cikin gidanmu…
A ƙofar ɗakina A ` i ta samemu ina bawa Nana shawara , amma tana zuwa gaba ɗaya ta jagula komai ta ida firgita Nana har na kasa gano gabanta bare bayanta,
Ajiyar zuciya nayi tare da bin A ` i da kallo ban sake magana ba ina dai jinta tana ta ɗora Nana a hanyar banza ita kuma tana ta karɓewa dan a ganinta shawarar A ` i itace mafita a gareta ,
Ƙawar Amisty da tayi ciki suka shigo da sallama ita da wata mata , inda nake zaune suka nufo gaisawa sukayi dasu Nana sannan sukace wurinki muka zo , miƙewa nayi tare da cewa ku shigo na faɗi maganar tare dayin gaba suka biyo bayana !
Wurin zama na basu sannan nima na zauna muka gaisa , bayan gaisuwa ƙawar Amisty tace Sultana kin ganeni kuwa ? Murmushi nayi ban bata amsa ba , taci gaba da cewa idan da hali nima zan shiga ƙungiyarki , ga ƙawata itama zata shiga, kallo nabi su dashi bayan wani lokaci nace ita ƙawar taki tana da aure ne ?
Dukanmu matan aure ne , Ni suna na Fadeela inji ƙawar Amisty mai cikin shege , sai kuma ta nuna ƙawar da suka zo tare tace ita kuma sunan ta Zalifa , saida na ƙara kallesu tsaf sannan nace miye dalilinku na shiga wannan ƙungiya … ?
Wacce aka kira da Zalifa tace wato ina da wata damuwa ce ta musamman wacce bazan iya biyanta ba ko cika burina ba dole saina shiga wannan ƙungiya mai albarka , ina so na samu goyon baya da taimakon tantiran dake cikin wannan ƙungiya ,
Murmushi nayi sannan nace wannan wace irin damuwa ce ? Gyara zama Zalifa tayi tare da cewa wato ina da wata maƙociya wacce na ɗauki amana da yadda na bata , bana ɓoye mata sirrina ko kaɗan .
Wata rana ta shigo gidana sai taji muna hayaniya da mijina , bayan mun gama mijina ya fita sai take tambayana abinda ya haɗamu , ban ɓoye mata ba kamar yadda na saba na kwashe komai na faɗa mata ,
Na ƙara da cewa bansan abinda nayi masa ba duk abinda bai taka kara ya ƙarya ba sai yayi ta faɗa akanshi wani lokaci ma hada duka , sai tacemin yadda Allah ya halittani da kyakkyawar siga mai burgewa na kashe aurena zan samu wanda yafi mijina ,
Nuna mata nayi cewa bana iya kashe aure na amma zan haƙura gaskiya na zauna dashi a haka tunda ina sansa wata rana zai gaji ya daina , sai tacemin ai sai anbar zomo yake zama guza , mazan yanzu da asiri ake ladaftar dasu in bada kuɗi taje ta nemo min asiri inyi maganin mijina.
Banji wani komai ba na bata kuɗi masu yawa dan tacemin itama mijinta da yake mata biyayya malamin yayi mata maganinshi , kuma naga yadda mijinta yake mata biyayya sosai kuma yanajin shakkunta dan haka na bata kuɗin nima a samomin asirin in riƙa dawwara mijina…
Haka kuwa akayi tayi ta kawo magani ina barbaɗawa mijina a abinci ina zuba mishi a ruwan wanka da abin sha laya ƙarƙashin filo wasu layun a ƙarƙashin gadonshi , tunda safe kafin ya fita na kunna hayaƙi , shirka dai iri iri da ƙazanta nayi ta barbaɗawa mijina yana lashe wa ,
Haka tayi tamin wayau tana karɓemin kuɗaɗe , murmushi tayi tare da cewa kinsan me ya faru ? Nace mata A , a, tace kwasam sai ta tayar da fitina wa mijinta da yake aurenta , kuma yanayi mata wani irin azababben so yana ƙaunarta fiye da duk yanda zan faɗa muku , amma saida ta kunno masifa ya saketa , har wannan lokaci bata daina kawomin asiri ba ,
A daren ranar data kawomin magani na zubawa mijina a abinci yana gama ci babu laifin zaune babu na tsaye ya gwagwaɗamin saki 3 ita kuma ta aure min miji gani nan na fito bani ga tsintsu bani ga tarko kinji hukuncin da tayi min….
Murmushi nayi kaɗan sannan nace kin aihu da mijin ne ? Tacemin a , a , nace ita ubanta yana raye ne ? Tace min Eh nace ya yanayin samunshi yake ? Tace babu laifi gaskiya yana da rufin asiri , da kyau nace tare da cewa mijinki kina san ki koma gidanshi ko kuwa ya kike so ? Zalifa tace gaskiya bazan koma ba so nake kawai ku riƙe mishi wuya ku jawo shi a cikin ƙungiyarku ku ƙare duk wani tattalin arziƙinshi babu asiri Sultana ki fitar min ita daga gidan…
Jinjina kai nayi tare da cewa ni bana asiri amma sharrina da kaidina yafi asiri bala’e a rayuwar ɗan adam , waya na bata tare da cewa sakamin lambar mijinki ki ajiye min ita da lamba 4 , ansa tayi ta sakamin tayi saving kamar yanda nace , bayan ta dawomin da wayana nace babanta a wane anguwa yake ne ? Zalifa tacemin gaskiya bai cika zama ba , nace to karki damu zai zauna dan dole ki samo numbershi ni kuma nayi miki alƙawari su dukansu zamuyi musu aiki …
Zalifa tacemin ina da motar hawa idan zakuyi amfani da ita , nace tou yayi kyau mun gode , jakarta ta buɗe ta fiddo kuɗi har naira dubu ɗari ukku tace gashi taba ƙungiya tata gudumawar , godiya nayi tare da ƙwalawa A ` i kira nace ta kawo musu form su cika , Zalifa tace karki damu zan cika anjima idan muka dawo akwai inda zanje yanzu , nace tou babu damuwa sai kun dawo…
Miƙewa sukayi zasu tafi nabi bayansu dan rakiya amma ban wuce ƙofar ɗakina ba , anan na tsaya nayi musu addu’ar sauka lafiya , bayan sun fita na koma ɗaki naci gaba da “yan hididdumu na , na tattara kaya saboda zamu tashi daga gidan yau zuwa sabon gidan da na siya , kuma duk nace matan gidan subini mu koma gidana da na siya , sauran ɗakunan da suka rage zan nemo “yan gidanmu na tattara su wuri ɗaya hadashi gogon wato Babana dan nafi so nayi karuwanci a gaban idonshi ya gane cewa ba’ayiwa iskanci haye….