Uncategorized

MUSAYAR RUHI 9-10

 

*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

               *NA*

      *NPEEDY A AJI* 

 _(MARMIY ZARAH CE)_

“`LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE“`

*1. NAYI RAYUWA DASHI*

*2. SANADIN ACCIDENT*

*3. SAKAYYAR CUTA*

*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*

*5. MUGUN SARTSE*

*6. FURUCI….*

*7. JUYI BIYU*

*8. HAYATUL MAHAYAT*

        AND NOW

“`MUSAYAR RUHI“`

*_____________________________________*

 *????????AINUWA ????RITER’S✍????*

*????SSOCIATION????????*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

 *Page 9 & 10*

*Y* ana fita yanufi wajan Ammin yana shiga Hanan da Ansar dake parlour sukayi saurin miqewa suna gaidashi bai kallesuba baikumace komiba abinda bahalinshiba yana shiga yasamu Ammi tsaye da’alama tana cikin tunani sosai zama yayi sannan yace ” Ammi ” saurin juyowa tayi sabida ko sallamar shi batajiba sabida tana cikin tunani saurin zama tayi agefanshi kafin tayi magana yayi saurin cewa ” shima wannan doctor yacemin bazan warkeba Ammai nikuma har yanzu bancire raiba inaji ajikina zanwarke ko Ammi? ” yaqarashe fad’ar hakan cikin rawar murya ” saurin kamo hannunshi Ammi tayi tashiga lallashin shi ajiyar zuciya yasauke mai qarfi yace 

” Ammi yaya zanyi banaso kowa yasan matsalata bayan ku shine nayanke wata shawara idan har akayimin hakan zansamu sauqin rad’ad’in zafin da zuciyata keyi idan kuma bansamu hakanba tabbas rayuwata tanacikin hatsari Ammi inaso Hammat ya’auri Hamidat amma auran Sirri batare dasanin kowaba koda ita Hamidat d’in banaso tasani koda Hammat zeje mata inaso yaje amatsayin ni bayan nasamu lafiya seyasaketa tadawo gareni idan akayi hakan shikenan babu wanda zaisan inada wannan lalurar kinji Ammi banason auran yawuce gobe sabida kinga nanda kwanaki 6 zasusake tasar da wannan banzar al’adar ” 

ajiyar zuciya Ammi tasauke tace ” haba Hassan karson Hamidat yasaka kafarayin abu cikin rashin tunani kana raye shima Hussain yana raye kuyi tarayya da mace 1 d’aya gaskiya hakan babu tsari Hassan nasan kishima bazai barka kazauna lafiya ba son dakakeyima Hamidat yakai matakin dazakayi mugun kishi akanta kagakuwa hakan zai’iyajawo muku rashin jituwa kaida d’an’uwanka bazanso hakaba kuntashi babu maijin kanku tun yarinta bazanjuri ganin akasin hakaba bayan girmanku kacanza wani tunanin kaji wannan tunanin naka baiyiba ” 

miqewa yayi zaifita cikin zafin zuciya saurin dakatar dashi Ammi tayi dafad’in ” dawo kazauna Hassan ashe akwai ranar dazakanunamin fushinka akaina Hassan karkasa naji cewa Hamidat batadace dakaiba idan har zaka’iyayin fushi dani akan lamarinta to tabbas zance bakudaceba inama hamidat tanasonka kamar yadda kakesonta datarufamaka asiri data zauna dakai natsawon lokaci ahaka dakarfin buqatar tata yagudu daga gareta sabida tsananin soyayya amma babu komi itama tanada uziri mai qarfi sabida kowace mace da’irinta naji zanyarda kasaki  Hamidat Hussain ya’aureta amma inada nawa sharad’in nafarko yazama dole kasanar ma Hamidat kalmar saki taji da kunnanta sabida sakin yahalarta dama batada idda akanta sannan kasan yadda zakayi kar wanda yaji labarin sakin sannan karubuta takardar sakin kakawomin kuma kasan yadda zakayi tajikamar kaine kasake mayar da’ita amatsayin mata sannan kuma yazama dole kakoma bedroom d’in sama sabida gujema abinda idanunka zasugani kosuji tsakanin Hussain da Hamidat sannan yazama dole kaguji ta’ba koda hannunta sabida tatashi daga matsayin matarka a lokacin sharad’i na 2 wanda kuma shine maiwuya agareka nasani amma idan kace a a tonima zance a a inaso ka’auri Hanan kuma nima agobe nikeso ” 

” zaro ido Hamut yayi yadubi Ammi yace ” ni na auri Hanan Ammi dan Allah kicanza wani sharad’in bazan iya yin wannan ba matsayin qanwa nad’auki Hanan bayan wannan babu wani kuma gata tayi yarinya dayawa Ammi kinsan banason auran qaramar yarinya batun yanzuba sannan kuma tayaya zan’iya duban Maimartaba dasauran mutane nace zanqara aure bayan kwanaki 2 kacal dayin aure na dole za’ayimin tambayoyin dabani da amsarsu sannan kinsan al’adar Family mu bakata’ba auran wadda ba nijinmuba kuma kinsan Hanan bajinimubace dan Allah Ammi kicanza wani sharad’in naji duk wanda kika fad’i akan Hamidat duk zancikasu in sha Allah amma wannan akwai matsala ” 

zama Ammi tayi tace ” duk nasan dahaka kai babu ruwanka kabarni dakomi kuma ay dakake maganar Hanan tayimaka yarinya sosai aykai yanzu yarinyar yadace dakai sabida itace bazatadamu dawani haqqi nata na auratayya akankaba hasalima tsoran lamarin zatad’ingayi idan baka kulatabama natsuwa zatasamu kaga kenan har zuwa lokacin dazakasamu lafiya bazata nuna qosawaba sannan naji kacigaba dad’aukar Hanan matsayin qanwa zanfijin dad’in hakan dan nasan bazaka tsanetaba idan kasamaranka cewa qanwar kace tun tuni nakeson ka’auri Hanan amma senaga hankalinka yanakan Hamidat kuma kazurfafa sosai shiyasa nabarka nafarayin tunani akan Hussain amma shi inajin shakka akanshi bashida yatsani Hanan sosai fiye dakima nikuma banason Hanan tasha wahala ko kad’an itad’in Amanar zuciyatace Hassan ” 

saurin kallon Ammi Hassan yayi yajinjina kai yace ” amma Ammi nifa gaskiya koda nawarke banajin zan’iya yin mu’amalar aure da Hanan gaskiya zanji kunyar lamarin qanwata wadda narena haba Ammi meyasa baki kai tunaninki kan Ansar ba shine dede ita kuma sun shaqu sosai ” 

mirmushi Ammi tayi tace ” nafika sanin haka ni zuciyata kai taza’bar ma Hanan ba kowaba sannan magana kan bazaka’iya sauke mata haqqintaba bayan kasamu lafiya wannan bayanzu yakamata kayanke hukunciba kajira zuwa lokacin sekabani amsa asannan ne zangamsu daduk maganarka idan ka’amince danawa sharad’in tonima na’amince danaka kuma zanji dakomi ” 

tashi tsaye Hassan yayi be dubetaba sabida baiji dad’in sharad’in nata na 2 ba yace ” na amince ” daga haka yanufi hanyar fita dede lokacin Hussain yashigo duban fuskar Hassan yayi yaga babu walwala ajiyar zuciya yasauke cikin zuciyar shi yace ” Allah yasa Ammi bata amince dawannan mugun tunanin nakaba ” zama yayi a’inda Hassan yatashi yace ” Ammi kinji wani banzan tunani da Hamut yayi ko hmmm tayaya zan’iyayin hakan? ” dubanshi Ammi tayi tace ” ayko yazama dole kayi sannan inaso kasa aranka cewa aure ne zakayi nad’ind’ind’in da Hamidat banawani lokaciba kamar yadda Hassan yake tunani nasan daga lokacin daka auri Hamidat kishi zaisa Hassan  yafarajin son hamidat yana raguwa cikin zuciyar shi zuwa wani lokaci zai manta da’ita  daganan semusanar dakowa komi shiyasa nabashi umarnin auran Hanan dan kar yayi 2-0 ” miqewa Hussain yayi yace 

” maine Ammi Auran Hanan ga Hamut ina Ammi zakisaka yarinya taqara renamu yarinya qarama gaskiya ni kam bangoyi bayan hakaba sannan bazan iya yin auran dindindin da Hamidat ba sabida banasonta ko kad’an kuma bazan sotaba wallahi badan karfin soyayyar danikeyima Hamut ba dabazanyi wannan auran sirrin ba amma zatagane shayi ruwane wallahi senayi maganinta kuma ni bazan iya auranta na dindindin ba yana warkewa zansaketa suqarata can koma yabar sonta nikam babu ruwana ” daga haka yanufi hanyar fita girgiza kai Ammi tayi tace 

” jeka masifafan banza kawai aykai dama ba’ataba dedetawa dakai kwata kwata bakada fahimta wannan zuciyar taka maizafin tsiya Allah yanunamin lokacin dazatayi sanyi natabbata dakaine nasakama irin sharad’in Hassan bazamu kwashe lafiya ba ni bansan ina kakakwaso wannan zuciyar banzarba da shegen taurin kai ga kafiya kayimata duk abinda kagadama ita taja dama ance idan bakayi sharar masallaciba tokayi tarumfar kasuwa dama kaine dede Hamidat d’in ” 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button