HABIBI DA’IMAN 101-120

*page 101~105*
*k*walwarshi ke neman juyewa don tana neman tallafin rasa tunaninta saboda yadda yake jin muryar Uncle d’in nashi naratsa har cikin zuciyarsa dake k’ok’ari wurin ganin ta daina bugawa a hankali yakejin murya Uncle d’inshi nacewa “haba yaya zakazo da irin wannan zancen da nasan zaiyi wuya mahaifinka ya yarda ka auri yarinyar da bata cikin hankalinta, toh idanma ka aure tah miye makomar soyayyarka da auranku duk ranan data tuna komai?
Sannan dake cewa so kake ka aureta yanzu don kanason kazama sanadin warkewarta kamanta da aikin kane? Don nasan ko yanzu hutunka ya kusa k’arewa”
Wani irin d’aci yakeji cikin bakinshi, zuciyarshi natafasa data haddasa jin zafin da yakeji a jikinshi, dakyar ya iya bud’e bakinshi “zan’iya barin aikina saboda khadijah” sannan yamik’e yatafi badon yana ganin gabanshi ba don har yana bangaje Rafeeq batare da yasani ba
Shigowa yayi yazauna, Uncle d’in yagaya mashi duk abinda Jiddan yace dangane da auran khadijah dayake son yayi cikin weak d’innan
Neman mafita kawai yake halboma rayuwar Jiddan don yana tsoron tarihi ya maimaita kanshi don wannan karin idan akace za’a hanashi auranta, tabbas zasu haifama kansu D’A mara ido
Ajiyar zuciya ya safke “toh kai Uncle mekace game da haka?”
“ina ganin kamar yaya bazai amince ba shiyasa nace yayi hak’uri da batun auren yarinyar yanemi wata kawai ya aura, in auren yakeso”
Girgiza kai Rafeeq yayi “wallahi Uncle nike tare da Jiddan tunda wannan k’addarar tafad’a mashi, ina tsoron halin dazai jefa kanshi ciki idan aka hanashi aurenta akaro na biyu, duk da nasan iyayenta dakyar su amince, toh amma halin da zasu shiga za’a duba”
“to amma bank’i zancenka ba don gaskiya kafad’a, saidai abinji shine mahaifin Jiddan”
“karkaji komai kabarni da Abba nasan yadda zanyi na fahimtar dashi, Momy kuma kasan batada matsala kan maganar”
Nisawa yayi yace “toh Allah yashige mana gaba, kushirya zuwa anjima muje wurin mahaifan khadijah muji abinda zasu ce kafin in sanarda yaya abinda ake ciki”
“toh shikenan Uncle bari ingaya mashi”
Tund’azu take matsa mata da zancen school duk tarasa yadda zatayi mata ta fahimta, tunaninta ne yakatse jin yadda tadage tana kuka saboda tana son komawa skull
Dafata tayi tace “khadijah” shuru tayi tana saurarenta, kafin daga bisani ta cigaba dacewa “inaso kinatsu ki fahimci abinda zangaya maki” d’aga mata kai tayi alamar tana saurarenta “khadijah kin dad’e baki da lafiya hakan yasa muka dakatar da karatunki har abokan karatunki suka gama, bakiji nace maki Jiddan zaitafi wurin aikinshi ba? Kinga kenan kindad’e kwance baki da lafiya, don haka inason kicire damuwar komawarki makaranta yanzu har muga abinda Allah zaiyi”
Wani farin ciki taji ance Jiddan na aiki, kafin damuwa mai tsanani ta lullub’e kambun zuciyarta wanda yayi sanadin jefata cikin kwaryar tunanin da saida Mama ta fiddota ta hanyar fad’in “khadijah kinaji nakuwa?”
Daga kanta tayi sannan tace “wace irin rashin lafiyace nayi da harta d’auki lokaci maitsawo irin haka?”
Nunfasawa Mama tayi kafin tabata amsa “kindad’e acikin hali na ciwo wanda yayi sanadiyar tab’a kwakwalwarki da kuma rashin gani”
batasan lokacin da wasu zafafen hawaye kebin fuskarta wanda Mama keta k’ok’arin share matasu ta hanyar lallashinta dayi mata nasiha komi yasamu bawa mujarrabi ne daga gareshi, tare da k’ara lurar da’ita kan d’aukar k’addara maikyau ko akasinta
* * *
Tabbas dagaske idan khadijah ta farfad’o daga wannan gushewar tunanin na tah, me zatace dangane da soyayyarshi da kuma aurensu, idan ya aure ta tana cikin wannan halin?, wani gutsure ne na zuciyarshi yace kasan bazata tab’a k’inkaba don ko kaita keso, rawa yaji zuciyarshi nayi daya tuna yadda ta firgice sanadiyar mutuwar ss abinda yak’ara jefashi cikin kokwanton cewa anya khadijah bata shafe shi cikin babin rayuwar taba?
Tsayuwar da motar tayi shiyayi sanadin tsayawar tunaninshi, fita sukayi su duka ukkun tare dayin sallama a harabar gidansu khadijah
Abbansu khadijah ne yafito tare da amsa sallama ganin Jiddan da Rafeeq saidai wannan karon harda bak’uwar fuska yasa yayi masu iso zuwa cikin palourn saukar da bak’i
Bayan sungaisa Uncle ya gabatar mashi da kanshi a matsayinshi na kawun Jiddan tare da tambayar jikin khadijah
Gyara zama yayi yacema mahaifin khadijah “Jiddan ne yazo mani da babbar magana nason aure khadijah, shiyasa nima banyi k’asa a gwiwa ba nazo nema mashi tun da addini bai haramatan hakan garesu ba shiyasa nazo naji tabakinku”
Nisawa Abbansu khadijah yayi sannan yace “bazan yanke hukunci ni kad’ai ba don haka bari in kira abokina kuma mahaifi ga tsohon mijinta” nan take yakira Daddy ya shaida mashi yana neman shi
Duban Uncle d’in yayi yace “bari akawo maku ruwa kafin zuwan Alhaji” Bayan yashiga yayi ma Ihsan umarni datakai ma bak’i ruwa yakuma shaidama Mama kawunsu Jiddan ne yazo
Miyan bakinshi ne yakatse baisan sadda yahad’e shiba har saida Jiddan ya waigo ya kalleshi saboda jin k’arar “kwat” da yayi
A hankali tazo ta’aje masu kayan motsa baki batare data kalli ko suwaye ba tagaidasu sannan ta tafi
Kyarma yaji zuciyarshi nayi a hankali batare da kowa yasan yayi maganar ba yace “oh Rafeequ be strong mana”
Shigowar Daddy tasa kowa ya maida hankalin shi kan sallama da yakeyi, don lokacin har Abbansu khadijah ya dawo bayan Mama tasanar dashi cewa khadijah bata da magana sai yaushene bikinta da Jiddan?
Bayan Abbansu khadijah ya fayyace ma Daddy komai kan buk’atar dasu kawu sukazo da’ita
Daddy ya cigaba da cewa “Ni aganina wannan bawata matsala bace tunda shi yana sonta a haka kuma itama rashin d’aura matashi yana iya jefata cikin wata matsalar, duk da munsan abinda muke shirinyi yana da hatsari, musamman lokacin dazata tuna komai yaya makomar aurensu take a wurinta? To amma idan kukayi la’akari da lokacin data auri suleman bashi takeso ba Jiddan d’in takeso, biyayya ce kawai yasa ta aure suleman ta zauna dashi lafiya”
Ajiyar zuciya Abbansu khadijah yayi yace “toh shikenan na amince Allah yasa haka yafi zama alkhairi”
Murmushi Uncle yayi don yaji dad’i ba kad’an ba sannan yace “muna neman wata alfarma da a d’aura auren cikin satinnan”
Abbansu su khadijah yace “badamuwa duk yadda muka yanke da ‘yan uwana zakuji ni”
Godiya sukayima junansu kowannen ya wuce gida banda su Rafeeq dazasu gaisa da khadijah
Zaune suke a palour, sai ganinta sukayi tana dafa bango tare da kiran sunan Jiddan, da sauri yatashi yarik’o hannunta yace “pls andeejanah kidaina tahowa ke kad’ai kada ki fad’i”
Cikin shagwab’a ta turo baki “Dama da ban lafiya harka gama karatunka kana aiki shine baka gayamani ba?”
D’an langab’e kai yayi alamar yayi laifi yace “i’m sorry nayi laifi” dariya tayi “toh yaushe?” ya fahimci metake nufi yasashi cewa “cikin weak d’innan” shidai Rafeeq yagaji da yadda suka manta dashi shiyasa ya katsesu ta hanyar cewa “khadijah ina sister d’inki?”
Juyawa tayi inda takejin sautin muryashi tace “Ihsan” “eh” “tayi bacci” ba haka yaso ba sai ganin bayadda zaiyi yasa ya fiddo wayar yabata yace “ta mantata a mota dazu da muka dawo asibiti” da haka yatashi ya fita ya basu wuri
* * *
Yanzu ya za’ayi yaron nan yace wai bazawara kuma wacce bata da hankali bata gani zai aure, koda yake kawun nashi daya biye mashi shine babban mai laifi suma iyayen nata basa tunanin abinda zaije yadawo idan ta tuna duk abinda yafaru a rayuwarta”
Momy ce tadafashi cikin sigar lallashi “haba Abban Afnan kamanta irin wahalar da mukasha a baya? Ko kamanta halin da yaron nan ya shiga wanda har yanzu bawai warkewa yayi ba, gaskiya bana tunanin idan muka hanashi auranta a karo na biyu zamu samu kwanciyar hankali, idan a wancan lokacin muna da hujja a yanzu banajin muna da’ita koso kake murushe rayuwarshi mu binneta da kanmu, kada mukasa yi… ”
Bata idaba kukan da take tarewa ya kufce mata saboda ko cikin ‘yayanta Allah yasani tafison ta gina rayuwar Jiddan don yazama uba ga k’ annenshi tunda ita jiddah mace ce hasalima yanzu a k’ark’ashin wani take, da sauri tafita don batason mijin nata yaga halin data shiga
Zaune yayi a inda tabarshi yana tunanin magangunanta gaskiya ne danko jiya bayan k’anin nashi yayi mashi bayanin yadda sukayi da iyayen khadijah, ya kira jiddah itama har kuka take akan kada yace zaihana k’aninta ya auri wadda yakeso
Wani b’angare na zuciyarshi ke gaya mashi kada yazama mai cutar da gudan jininshi tunda su iyayenta sun amince meye nashi na hanawa?
Da wannan tunanin yasamu yasaita zuciyarshi inda tafi rinjaye akan….
Mrs Abdul Sule
[1/17, 10:48 AM] Halima Mk: ????????????????????????
*HABIBI DA’IMAN*
*WRITED BY HALIMA Mk*
DEDICATED TO SA’ADATU ALIYU KABUGA
*page106~110*
*L*umshe idanuwanshi suke yana tunani saboda bashi ke driving d’inba kamar daga sama yaji muryar Jiddan na cewa “kana sonta kagaya mata mana”
Bud’e idanuwanshi yayi yanajin wani irin nishad’i naratsa k’ok’on ranshi yace “itace na dad’e ina nema” da mamaki ya kalleshi yace “kamarya?”
Da sannu Rafeeq yafara bashi labarin yadda akayi yaganeta har yazuwa yanzu da yakejin bazai iya rayuwa babu itaba, dariyar mugunta Jiddan yafara mashi shikuwa Rafeeq sakin baki yayi yana kallonshi saboda yana son yatuna yaushe rabon da yaga yana dariya irin haka, saida yayi ta isheshi sannan yad’agama Rafeeq gira d’aya yace “guy amma ka raina ni”
“kamarya yafa” “inason ya kanason k’anwa” saramashi Rafeeq yayi tare da cewa “sorry yaya jamilun Jiddan” hararar shi yayi yace “niko” tare da nuna kanshi
Kashe mashi ido d’aya Rafeeq yayi yace “friend” yace “For Ever” kasancewar wannan ce sararsu insun kad’aice su biyu,d’aya yace friend d’aya kuma yace for ever
Bayan sunci abinci sun huta saiga Abba yashigo dayake Momy na wurin shima sai yasamu wuri yazauna
Gyaran muryar yayi yace ‘Jiddan naji komai daga wurin Uncle d’inka saidai a gaskiya… Tsayawa yayi da maganarshi yana kallon cikin idanun Momy, hakan ya tabbatarma Jiddan Abbanshi bai amince da buk’atarshi ba
Wani irin tsalle zuciyarshi tayi a hankali yafara jada baya iskar dake d’akin tayi mashi zafi inda harshen wutar dake babbaka cikin zuciyarshi ke k’ok’arin tabo kwakwalwarshi don a dole ta bashi amsar meyasa k’addara da tsautsayi suke zama abokan gaba a rayuwarshi da khadijah,
Kullum fad’a suke inda k’addara ke k’ok’arin wajen ganin ta rabashi da khadijah kuma tana samun nasara saboda tsawon mizaninta ya wuce na tsautsayi dake yunk’urin had’ashi da khadijah.
Baisan ya akayiba sai ganinshi yayi a d’akinshi wannan ne yatabbatar mashi da aikin k’afafunshi ne
A hankali ya tsugunna saboda k’afafunshi sun kasa d’aukar nauyinshi, sai kuma yayi zumbur yatashi yana neman wine d’inshi don kuwa ya manta nan ba Abuja bane
Dasauri Rafeeq yaje yarik’e k’afar Abba yana fad’in “Why? Why? Why? Abba kasan halin da Jiddan zaishiga idanka hanashi aurenta ko don baka da cikakken sani akan rayuwar da yashiga baya, nasan baku saniba don dagani sai Mujaheed mukasan Jiddan nashan giya duk saboda sanadin khadijah na tabbata idan kuka hanashi wannan karin ba abinda zai hanashi neman mata, Haba Abba! Haba Abba!! Kaduba kagani ya akeson rayuwar shi tak’are”
Tsoro ne da fargabar abinda Rafeeq yafad’a ya k’udundune zuciyar Momy da Abba, a hankali cikin nadama Abba yafara cewa “baku tsaya kuka saurareni ba daga kai harshi kuka fassara abinda zanfad’a da zarginku saboda kunsama ranku bazan amince ba, alhali tunkan kuzo nagama shawara akan amincewa ta
Juyawa yayi da niyyar yima Momy magana sai yaga bata wurin hakan yatabbatar masu tana d’akin Jiddan, suma tashi sukayi suka nufi can
Zaune yake yarasa inda zaisa kanshi Momy sai bubbuga bayanshi take tana kwantar mashi da hankali, amma ina bayajinta danko yariga da yayi nisa
Sallamar da Abbanshi yayi ce tasashi d’agowa suka had’a ido, kafin yakauda kanshi gefe
Wuri Abba yasamu yazauna sannan yace “baka fahimci abinda zanfad’a maka ba kayi tunanin k’i amincewata, abinda baka sani ba tunkafin kuzo na amince, dama maganar inda zaka ajeta da yanda zakayi da aikinka nakeso inji?”
Sai yanzu yaji yasamu damar yin kuka kafin yatashi ya rungume mahaifin nashi don yakasa cewa komai saboda farin ciki ya tabbata wannan karin bazai rasa khadijah ba
D’agowa yayi daga jikin Abban yace “thank you Abba” Murmushi Abba yayi yace tunda khadijah tazama farin cikin ka dole muma mu sota don haka kaje kafara nema maku visa k’asar da zaka fita da’ita don nema mata lafiya, nikuma da kawun naka kabarmu da komai na bikin, inyaso sai rubuta takarda ka aika wurin aiki don naji Mujaheed yace cikin satin nan zaku koma”
Wayyo Allah dad’i kamar ya mutu don farin ciki yace “Dama sunsa bani da lafiya nagaya masu any time zan’iya koma check up india, to yanzu kaga shaida masu kawai zanyi”
*** *** ***
Wai haryanxu laila bazaki hak’ura da Jiddan mukoma Abuja ba?”
“Ashanty kenan, wallahi bazanyi zuwa kaduna a banza ba tunda ance yana katsina ni kuma har katsinar zan bishi donko dukiyata zata k’are akanshi, nidai muradina in mallakeshi to magana tak’are”
Kashe mata ido d’aya Ashanty tayi irin na gogagun ‘yan bariki sannan tace “ina tare dake k’awata har sai buriki yacika na mallakar Captain Jiddan”
Kuyi manage bayawa
Mrs Abdul Sule
[1/17, 10:48 AM] Halima Mk: ????????????????????????
*HABIBI DA’IMAN*
*WRITED BY HALIMA Mk*
DEDICATED TO SA’ADATU ALIYU KABUGA
Wannan shafin naku ne:
Safiya kabir{mum Iman}
Rahina Ali{sirrin mu mata}
Rahama Muh’d sani{Garkuwa fulani}
Maman suraya{HABIBI DA’IMAN FAN’S}
Queen sarah
Mrs Jmoh
Halima kangiwa
Aisha Bala Saulawa
Aisha Bala Shu’aibu
#Anatare????
*page111~115*
*A*n d’aura auren khadijah da Jiddan ayayin da komai ya daidaita su Ihsan sun koma school cikin kwanciyar hankali saidai fatan samun lafiya ga khadijah
Tafiya suke cikin mota, Mujaheed ne ke driving sai Rafeeq dake kallon gefen titi
A hankali yace “Nafara kewarshi” Mujaheed ya kalleshi yace “Allah sarki Captain J, Allah yaba khadijahrshi lafiy………..”
baik’arasaba wayarshi ta d’auki k’ara alamar shigowar kira, d’auka yayi tare da cewa “Hello little yakike?” shuru yayi kafin yace “Haba my love bamuma shiga Abujar ba amma idan mun isa zanyi maki text, don Damun isa streight office zamu wuce, so take care of your self” shuru yayi kafin yace “Ok bye bye”
Juyowa yayi ya kalli Rafeeq da ya zuba mashi na mage yace “kodai maganin mayu kafara sha wannan irin kallo haka?”
Harararshi Rafeeq yayi yace “takanka zanfara” Bayan su d’an d’auki lokacin ba wanda yace komai, Rafeeq ne yakawar da shurun ta hanya furta “Ihsannnn”
“ka kasa fad’i mata ko?”
“eh, naso ace su Abu da Ammi sunzo d’aurin auren nan ko don in gwada masu wacce nakeso kafin ingaya mata, saidai wannan uban azarb’ab’in Jiddan yasa anyi komai a gaggauce”
Kallonshi Mujaheed yayi yace “haba Abokina be strong mana kada mace tasaka jin tsoro, kagaya mata kawai, saboda ko su Abu sunzo basu zasu gaya mata kana sonta ba”
“eh nasani, kedai katayani da addu’a Allah yasa rabona ce”
“insha Allah rabonkace ma, yaushe ne tafiyarka eygpt?”
“sai munsamu wani hutun, don nayi missing d’in su Ammi, ga Rafeeqa tadame ni yaushe zanje”
Da haka suka cigaba da firarrakinsu har suka isa Abuja
***
Wani irin kululun bak’in ciki takeji da takasa had’eshi wai yazatayi ne? Ta biyoshi har katsina, amma abin haushi yayi aure harda wani tafiya india honeymoon shida makauniyar matarshi, ita yama zatayi yanzu haka zatayi ta jiranshi har sai ranar da yadawo?
Lallashinta Ashanty keyi saboda yadda Laila ke kuka saika d’auka mutuwa akayi mata
Murya irin wadda tasha kuka tagaji ta kalli Ashanty da jajayen idonta, tamkar Jiddan ne a gaban tah tace “zan jira dawowarka Jiddan da yarda Allah saina dagargaza Rayuwar shegiyar data aureka (anya zaki samu nasara akan haka????) sannan in mallake ka ko baka aureni ba saina cika burina akanka”
Nace uhmmm abinda Laila bata sani ba Jiddan ko wine ya daina sha tunda ya mallaki ruhin ranshi yayi ma mahaifinshi alk’awarin hakan bare wani guntun Romancing d’inki????
Da haka sukaja motarsu suka wuce Abuja zaman jiran dawowar Captain J
***
Ko a cikin jirgin wuri ne na musamman inda bakowa ke zama ba suke zaune
Rungume take a jikinshi ayayin da take baccinta cikin kwanciyar hankali, shikuwa sai Kallonta yake kamar ya had’iyeta don so
Hannunta ya kamo tare da murza zoben dake hannunta yana mamakin yadda akayi har yanzu bata cire shiba, wata kwalla yaji yataru a cikin idonshi, wanda nakasa gane ko tami cece,
Kiss yayi mata a kumatu yaci gaba da shafa fuskarta, tare dayi mata fatan samun lafiya
Shigar dare sukayi ma k’asar, shatar taxi ya d’aukar masu zuwa wani babban hotel, bayan yakama masu d’aki mai hawa na bakwai, ma’aikatan hotel d’in ne suka taimaka mashi wurin shigar da kayansu cikin lipter
So yake ya tashi yaje yayi wanka yai alwala don sauke farali dake kanshi kafin yayi masu order abinci, amma khadijah ta hanashi, ita’ala dole bazai barta ita kad’ai ba, saima wani k’ara mak’aleshi take, wanda ya haddasa ma jikinshi mutuwa tare da tada mashi wani mik’i, dakyar yasamu ya lallasheta yashiga, bayan ya fito ne ya taimaka mata itama ta shirya
Room service ne yayi nocking, tashi yayi ya amso masu abinci da sukayi order, bayan ya bud’e abincin ne khadijah tace “yayana naji k’anshi abinci”
“Open your mouth” batayi jinkiri wurin bud’e bakinta ba yasa mata abinci, lumshe idonuwanta tayi saboda d’and’anon girkin dataji cikin bakinta wadda ke ratsa sassan jikinta
Tsura mata ido yayi kasancewar sleeeping dress ne jikinta wanda ke nuna surar jikinta, shagalta yayi da Kallonta wanda take yaji wani abu na mashi yawo cikin kai natsuwarshi na neman barin jikinshi wata irin sha’awa ce ke fizgarshi, bayan yayi ma kanshi al’k’awrin bazai tab’a kusantar ta harsa radda ta dawo cikin hayyacin ta, ganin ya neman tadama kanshi hankali wanda batasan yanayi ba tunda baganin shi take ba yasa yayi saurin kawar da idonshi akanta, da haka suka gama cin abincin su suka bi lafiyar gado
***
*NIGERIA*
Mujaheed yayi waya da Islam yakai sau biyar tsakanin isowarsu Abuja zuwa yanzu, wanda yasa da sunfara wayar Rafeeq zaifara tsoki saboda bak’aramin takura mashi suke ba, ga damuwarshi inya kira Ihsan bata d’auka
Yanzu ma tsokin yayi tare da d’aukar wayarshi ya k’ara gwada sa’arshi ko wannan lokacin zata d’auka
Zaune suke ita da Mama suna cin tuwo, tuwon takeci amma zuciyarta na ga ‘yar uwarta ko wane hali take ciki, saida ta had’e lomar tuwon dake bakinta sannan tace “Mama kun koyi waya da yaya khadijah?”
“a’a basu kira ba tukun, dan kinsa akwai banbanci lokaci tsakanin mu dasu, may be sai zuwa anjima kiga sunkira ko kuma wayewar gari”
Kallon agogo tayi tace “Mama har yanzu Abba shuru baishigo ba”, “eh yace zaije wani wuri, kila sai zuwa anjima kiga yashigo”
Wayar Ihsan ce tayi ringing, kallon allon wayar tayi ta kauda kai, Mama ta kalleta tace “meye haka, bakiranki akeba kinaji”
“wallahi bansan ko waye ba, ya kusa wata biyar yana kira na daga yakira wrong number shikenan yanace, shiyasa ko ya kira bana d’agawa”
“Ihsan kenan,ai bakisan inda rana zata fad’i ba, ki d’aure ki d’auka kiji abinda zaice maki inkinga da shashanci yazo saiki rabo dashi, idan………….wayar ce ta k’ara d’aukar Ringing akaro na biyu
Kallon Mama tayi sannan ta d’auki wayar tare da shigewa d’aki
Baiyi tunanin za’a d’auka ba kamar yadda zuciyarshi ke raya mashi, saiji yayi an d’aga kiran, tsabar mamaki baisan sadda yasaki wata sanyayyar ajiyar zuciya ba
Sallamarta ce ta doki dodon kunnenshi, batare da bata lokaci ba ya mayar mata da aminci ya tabbata garesu
“don Allah bawan Allah kayi hak’uri kadaina kirana”…. “zandaina kiranki, amma sai kingaya mani dalili, don nasan ke bamatar aure bace………….”taya kasan ni ba matar wani bace?
“sanin hakanne yasa nace ke ba matar wani bace, kuma in kin misalta hakan kiyi mani rantsuwa da cewa kina da aure, toh nikuma nayi maki alk’awarin daina kiranki”
“naji ni ba’ita bace, to miyasa kake bibiyata?…………”saboda ina sonki kuma naji ajikina ke matata ce………….”to kayi hak’uri an tsaida mani miji”
Dammmm yaji gabanshi ya fad’i dakewa kawai yayi ya cigaba da cewa “banyadda antsaida maki miji ba” ya k’arasa maganar cike da nuna kishi
K’arya ba halinta bane yasa tace mashi “kayi hak’uri ni kawai karatuna ne agabana don haka banajin zai’iya had’a soyayya da karatu”
“shikenan pretty kibani damar ko gaisawa murink’ayi”…………..”toh naji, saida safe” tare da yanke kiran batare data saurari mai zaice ba
Ganin alamun ta katse kiran ne yasa ya kalli Mujaheed yana dariya, shikuwa ganin kallon dake mashi yasan yau andace Ihsan ta amsa wayarshi
A b’angaren Ihsan kuwa tunani take anya wannan mutumin baisanta ba? Saboda taji ya kirata da pretty, sannan tanajin muryarshi kamar ta tab’a jinta shiyasa ta yanke hukuncin bazatayi mashi k’arya ba don kar wata rana taji kunya
Washe gari Jiddan yakira su Mama ya shaida masu sun’isa lafiya gashi zasu tafi asibiti ma yanzu, bayan sun gama wayar da su Mama yakira su Daddy da Rafeeq suma ya shaida masu sun’isa lafiya.
Mrs Abdul Sule
[1/17, 10:48 AM] Halima Mk: ????????????????????????
*HABIBI DA’IMAN*
*WRITED BY HALIMA Mk*
DEDICATED TO SA’ADATU ALIYU KABUGA
*page116~129*
*INDIA*
*y*ana gama waya dasu Rafeeq ya juyo ya kalli khadijah dake zaune bakin gado tana jiranshi su tafi, tsayawa yayi yana k’are mata kallo saboda tayi mashi kyau dukda ba kwalliya tayi ba, hot pink d’in gown ce jikinta sai tayane kanta da Black veil sai takalminta ma Black mai karamin dunduniya
Matsowa yayi kusa da’ita ya zauna tare da rik’o mata hannu “khadijah mutafi ko?” zunburo baki tayi tace “yayana baka shafa mani lipstick d’ina ba”
“keda zamu Asibiti menene na shafa lipstick” yitayi kamar zatayi kuka yai saurin tashi yana cewa “sorry bari na shafa maki, haka yashafa mata pink d’in lipstick wanda yayi dai-dai da colour d’in gown d’inta
Abinka da farar mace sai tayi wani irin kyau
Tsurama D’an k’aramin bakin nata ido yayi yana Kallonta, wani irin kishi yakeji ace wani yaganta a haka
Itakuwa jin shurun yasa tace “yayana muje, ko kana wani abu ne?”
Kamo hannunta yayi “mutafi” har sunkai bakin k’ofa yaji bazai iya d’aurewa ba yabarta tafita da lipstick d’in, yasa yajawota da k’arfi ta fad’a bisa fad’add’en k’irjinshi, tallafo kanta yayi yana kissing d’inta sosai saida yagaji dan kanshi sannan yalashe lipstick d’in bakin nata
Kwat-kwata batayi yunk’urin hanashi ba don sak’on nashi nashigarta ta kowane sassa na jikinta
Jin Tsayuwar na neman gagararsu, gashi yana neman fita hayyacin shi yasa ya kyaleta, ajiyar zuciya suka saki a lokaci d’aya
K’ara gyara mata rolling kanta yayi yaja hannunta suka wuce
Ko a cikin motar tacika da tsoron shi, dan tasan ga dukkan alama Jiddan yana da buk’atar kusantarta, duk yana lura da yanayin ta amma baimata magana har saida suka isa Asibitin “khadijatu na ki kwantar da hankalinki nasan abinda kike tunani, bazan tab’a yimaki wani abuba har sai kin samu lafiya kinji ko don haka cool your mine” d’aga kanta tayi alamar ta gamsu da zancenshi
Ba’a wani b’ata lokaci ba aka k’arb’eta saboda duk wani shirye-shirye anyisu kafin su zo
D’aki ne na mussaman aka bata, bayan Jiddan yak’ara gaya masu yadda accident d’in yafaru da kuma bayanin da doctor d’in nigeria yayi mashi, duk suna maganar ne acikin harshen nasara
Take suka fara binciken musabbabin abinda yahana mata gani
Kwana d’aya rak suka d’auka suna bincike kasancewar suna da wadatatun kayan aiki, Alhamdulillah don ko sunyi nasarar ganin matsalar inda suka yimashi bayani
“Buguwar da tayi ne yasa ta manta wasu abubuwa sannan akwai wata jijiyar dake aiki tsakanin idanuwanta da brain d’inta itace tasamu matsala shiyasa ta daina gani, amma wannan ba wata babbar matsala bace akwai aikin dazamu yimata insha Allah ganinta zai dawo, sai abubuwan data manta sukuma a sannu zata tuna mussaman ma in an shawo matsalar ganin nata”
Ya kirasu Abban khadijah yayi mashi bayanin halin da ake ciki, yakuma shaida ma daddynshi komai kamar yadda su Rafeeq suka kirashi suma yagaya masu yadda ake ciki
Haka yayi ta jinyar khadijah don hatta wanka shike mata tun tanajin kunya harta hak’ura ta kyaleshi tun ranan da taga tafad’i a toilet bata k’ara yadda tashiga ita d’ayaba saidai yayi mata da kanshi
Shiko shikadai yasan a zabar da yakesha duk randa yayi mata wanka don wani irin sha’awa ce ke damunsa jiyake kamar yayi ta suburbud’arta amma bazai iya ba harsai radda ya alk’awanta ma kanshi
*NIGERIA*
waya take amsawa saiga Ihsan tayi sallama, a hankali tace “ya Muhsin sai anjima munyi waya ga Ihsan nan tazo” daga can b’angaren Muhsin yace “Ok badamuwa kigaida ta” daga haka yayi hanging up d’in call d’in
Murmushi Ihsan tayi “lalle Samrah baki karatu kin biyema ya Muhsin ko?”
“Ihsan bazaki gane ba wallahi idan kayi dace da masoyi mai sonka tsakani da Allah kadace, inma takai tamaki zance su Daddy ma sun sani”
Kad’a kai Ihsan tayi “keni rabani da wani zance soyayya ina sweety na take?”
“tana kitchen ita da Ummi wai fankasu take son ci”
“nima kuwa zanci dadina da seemah bata da k’iwa keko kina nan kin zama uwar soyayya”
Dariya Samrah keyi tana cewa “itama duk jirgi d’aya yakwasomu” Ita dai Ihsan ko Kallonta batayi ba ta wuce kitchen d’in
Tana zuwa ta tarrada da seemah na aiki lokacin Ummi ta fita hakan yasa ta cigaba da tayata suna fira, cikin firar tasu ce seemah ke gaya mata A.j yazo gurin Daddy yana son ya bashi iznin nemanta, kuma Daddy ya amince mashi
Itadai Ihsan tana jinta amma tunani take yadda mutum zaice ya had’a soyayya da karatu
Haka suka gama girkin suna fira daga baya Ihsan itama take shaida masu wanda yakirata, Seemah ce take gaya mata koma waye kila yasanta
Lokacin data koma gida take gayama Mama ashe Muhsin Samrah yake so shikuma Aj Seemah yakeso, kasancewar bata da abokiyar sirri kamar mahaifiyarta, itama Mama tajawo ‘yayanta jikinta kamar k’awayenta shiyasa duk wani abu da suke ciki suna sanar mata
Sai a lokacin Mama ta gwada mata cewa aita dad’e da sani saboda ita suka fara gayamawa kafin su sanar da su Seemah
Haka kwanaki sukai ta tafiya, saidai Rafeeq baik’ara kiran Ihsan ba tun ranan da yakirata,
Ita kanta tarasa dalilin dayasa take tunanin mai yasa bai k’ara kiranta ba, alhali bawani sonshi take ba balle har tadamu da rashin nemanta da bayyi ba
Shikuwa Rafeeq wani aiki aka turasu kullum yana busy shiyasa baikirata ba ga dalilin nabaison ya takura mata tunda ta nuna batason soyayyar, amma harga Allah yana son yakirata ko muryar ta yaji
*INDIA*
kwanan ta biyu da dayin aikin idon saidai har yau basu bud’e mata shiba, wanda yak’ara jefa Jiddan cikin wani hali na tararrabi, bai gushe da tunanin saba wani d’an tsamurmuren likitan idon yashigo tare da sauran nurses dake rufa mashi baya
Tunda aka fara k’ok’arin warwarewa bandeji da suka rufamata a ido, Jiddan ke addu’ar Allah yasa a dace don har kyarma jikinshi keyi
Saidai aka gama warwarewa bandejin gaba d’aya doctor d’in yace ta bud’e idonta a hankali karta bari Haske yashiga gaba d’aya
A hankali takeson bud’ewa saitaga wani irin haske sai tarufe, d’aurewa tayi harta samu ta bud’e su duka saidai biji-biji take ganin mutanan dake wurin shiyasa ta shiga kyafta idanuwanta sai kuma ta koma tana gani lafiya lau
Jiddan dake rik’e da hannunta duk yabi ya diririce godiya kawai yakema Allah (S. W.A)
Akanshi tafara sauke idanuwanta, saida kuma takasa kauda kwayar idanta daga cikin tashi, shima ita yake kallo saida suka d’auki kusan five minutes a haka, don haka doctor yayi ma kowa alamar da akyalesu a hakan
Itakuwa khadijah gani take kamar ta shekara goma bata ganshi ba, ga kamanninshi da suka canza mata daga yadda ta sanshi, saidai tasan shine ba wani ba
Shima yana tuna rabonda ya ganta yau shekara bakwai kenan
Wani irin sak’on soyayya idanuwansu suka shiga aikawa juna wanda bamai iya fahimtar mai suke isarwa saisu
A hankali tad’aga hannunta ta shafi sajen dake fuskarshi don ya birgeta kuma ita bata masan dashi ba, tana kai hannunta saman sajen taji wani irin shock da sauri tajanye ta cigaba da kallonshi, Jitayi kamar tana son tuno wani abu, saurin kawar da idonta tayi daga gareshi sakamakon wani irin a zababben ciwon kai da taji lokaci guda ga idonta dasuka yimata nauyi