HAJNA 25-26

♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
PAGE 25-26
**********************
A ɓangaren su Umma kuwa, Baffa ya yanke hukuncin ko Hajna ta dawo ba gidan sa ba, Umma kuwa ta ja bakin ta tayi shiru, saboda itama ɗin bata da ta cewa, kuma addu’ar ta Ita ce Allah ya shirye Hajna.
ABUJA ************
A ɗaki take tayi wanka tayi kyau kamar ba ita ba, Qaseem ne ya shigo yace “Favorite one ki same ni ɗaki “, be tsaya yaji me zata ce ba ya juya, ya fita, bayan ya fita Hajna ta zauna tana tunanin yadda Qaseem ya canza, dan ta mishi magana akan Easter shiyasa yake ɓata rai ko minene, ɗakin shi ta nufa, kwance ta same shi, zaunawa tayi, yafi ƙarfin minti uku be juyo ya kalle ta ba, daga baya kuma ya juyo, duk da haka be yi mata magana ba, sunfi minti talatin a haka, kafin Hajna tace “kayi haƙuri idan nayi maka laifi, ba da njyya nayi ba, kuma in dai akan ma’aikatan ka ne bazan sake maka magana ba”, har ranshi yaji daɗi, amma sai be nuna mata ba, sai ma rufe idon shi da yayi, hannun ta, ta kai kan goshin shi, a hankali tana shafa mishi kai, cikin salon da ita kanta bata san tana da shi ba, a hankali har ta rikita shi, bata yi auni ba ta ji ya jawo ta jikin shi ta faɗo masa a jiki, lumshe ido tayi jin ta a jikin shi, wani farinciki ya cika ta, ina ma ace suna da aure, “ka haƙura? “ta tambaya tana kallon cikin idon shi, be amsa ta ba kawai ya haɗa bakin shi da nata, in a romantic mood ya fara wasa da ita, wani sound take sake duk ta rikice, ƙoƙarin haɗa jikin ta da nashi take yi duk ta rikice, ture ta yayi yace “ke miye haka, wannan salon naki be min ba, ki tashi ki bar min ɗaki, ko yadda ake sa namiji yaji daɗi baki iya ba, fitar min daga ɗaki, kuma ki kira min Trisha nasan zata min abunda nake so “ya faɗa cikin faɗa, tashi tayi ta fita, Trisha ta kira mishi kamar yadda ya ce tayi, sannan ta wuce ɗakin ta, kwanciya tayi tana me jin tsanani ciwon mara, dan dama tana da matsalar ciwon mara, gashi yanzu Qaseem yana tada mata da shi, juyi take yi kamar ranta zai fita haka take ji, ko tafiya ma bata iya yi, yadda taga dare haka taga safiya, a daddafe ta shiga toilet tayi arwala, sallah ma a zaune tayi ta, tana matuƙar buƙatar Qaseem amma miyasa zai mata haka, tana nan domin shi, bata samu soyayyar shi ba, kuma ga wulaƙanci tana fuskanta gurin shi, wasu hawaye masu zafi su ka zubo mata a kunci, kuka taci ta ƙoshi, a gurin barci ya ɗauke ta.
Misalin ƙarfe 12:30 na rana
Trisha ce ta fito daga ɗakin Qaseem, dan dama Qaseem yana jin daɗi harka da Trisha, sannan tasan yadda zata bi da Qaseem cikin sauƙi, shiyasa in ta shiga ɗakin shi tana daɗewa bata fito ba, saukowa tayi downstairs ta gyara ko ina, sannan tayi wanka, ganin har yanzu bata ga Hajna ba yasa ta shiga ɗakin ta domin duba ta, kwance ta same ta akan sallayar ta, da alama ko sallar azahar ba’a ta yi ba, dan yanzu ake kiran sallah, tada ita ta shiga yi, a hankali ta shiga buɗe idon ta, tashi take ƙoƙarin yi amma ta gagara saboda marar ta na mata tsananin ciwo, kama ta Trisha tayi ta tashi wanka tayi sannan ta dawo ɗakin, inda ta bar Trisha ɗazu nan ta same ta, shiryawa tayi, nan ta zauna tana gayawa Trisha abunda ya faru jiya, dariya Trisha tayi tace “ashe baki gama sanin halin boss ba, muddun kina nuna mishi so to kin gama wulaƙanta, kina basar dashi, yanzu kar ki bari ku sake haɗuwa har sai ya neme ki, kuma ko ya zo ɗakin ki karki kula shi har sai anyi kwana uku yana bin ki, yanzu nasan bazai neme ki ba, sai nan da kwana biyu, haka yake wa Favor, har yanzu wulaƙanci yake mata, tun tana kuka har ta saba, wai bata da daɗi “, Hajna tace “amma ni bazan iya fushi da Qaseem ba”, Trisha tace “ke kuma baki daina fuskantar baƙinciki ba”, shiru Hajna tayi tace “to ita Favor miyasa yake mata wulaƙanci “, Trisha tace “saboda tana son kwanciya da shi, da ya gane haka, sai ya riƙa mata wulaƙanci”, Hajna tace “amma ni baki ganin da bambanci, shi fa ya ganni yana so”, Trisha tace “soyayyar da Qaseem yake wa Favor ba ƙarama bace, dan ita kaɗai ce taci kuɗin Qaseem kafin ya samu tazo nan, sai dai yanzu ko naira bata samu a gurin shi, ni ce wacce ke cin kuɗin shi, dan ko hannuna bana yadda ya taɓa sai ya bani kuɗi, dama ni karuwanci na kuɗi nake yi”, Hajna tace“to yanzu miye mafita “, Trisha tace “kiyi yadda nace kawai, ke kuma zaki huta”, shiru Hajna tayi, a ranta tana jin son Qaseem ta ko ina na jikin ta, anya zata iya kuwa, Trisha da ta Fahimci yana yin Hajna tace “Hajna kar ki bari so yasa ki wulaƙanta, ko kinyi a banza dan Qaseem bazai aure ki ba, to gara ku casa juna keda shi “, Hajna tace to shikenan.
A ɓangaren Qaseem kuwa yau ne ranar da zasu yi summiting aikin su, gashi Farween ya ɓata musu, shiga suka yi gurin taron, inda aka kira su akan suyi summiting aikin amma suka gagara, Farween kuwa tashi yayi yana murmushin munafurci ya wuce zuwa gaban shugaban su, miƙa mishi file yayi yace “yallaɓai wannan shine aikin da Qaseem ya gagara gamawa”,, karɓa shugaban yayi cikin murmushi yace“Farween kayi abunda Qaseem bazai iya ba”, Qaseem kuwa haushi ya kama shi, wai miyasa kullum burin Farween ya ƙuntata mishi ne, tashi Qaseem yayi ya bar gurin taron.
Anan zan dasa aya……..
Wayyo Qaseem bawan god????????????Farween ya samana kai gaba, kayi haƙuri
Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️♻️????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
????????️ *ZAMWA* ????️????
( _Zamfara writters_ )