Uncategorized

HABIBI DA’IMAN 41-60

    Page 41~45

 wannan shafin na kune masoyan *habibi* *da’ima* ina jindad’in comment d’inku musamman ‘yan team *ss* ???? lol.

 Kwanci tashi asarar mai Rai yau gashi su khadijah sungama makaranta Shikuwa Jiddan yayi_ yayi da iyayen shi su sama mashi aiki don ya auri khadijah, amma sunce karatu zaiyi bazasu yima d’an 24 years aure ba

 

(abinda wasu iyayen basu sani ba Namiji baya kad’an Na Aisha Ali Garkuwa)

 

 

Ita kuwa khadijah tana ba samari dama saidai duk wanda yazo bada niyyar aure yake zuwa ba

 

Duk wannan hali da suka shiga ba abinda ya ragu  daga soyayyar Jiddan da khadijatu don koda yaushe suna mak’ale a waya tare da ba junan su kulawa  da manta damuwar su

 

 

         ????????????????  

 

Ummi ce zaune tare da ss tana mashi nasiha tace

 

“kaga yanzu kagama ginin gidanka don haka wannan ce magana ta tak’arshe da zan maka akan aure

 

Kallonta yayi cikin girma mawa yace

 

“Ummi na baki zab’i ki nemo mani Matar da kikaga tadace dani”

 

Murmushi tayi tace “ko kaifa suleman kuma insha Allahu zakaji dad’in zab’in da zan maka”

 

Bai k’ara cewa komai ba yatashi ya nufi part d’in shi yayi wanka ya fita zuwa majalisarsu duk da ba fira yake ba yana zuwa su gaisa sannan ya shiga gidan su khadijah

 

Ita kuwa Ummi harta kira Mama a waya ta shaida mata yadda sukayi da d’an nata da ganin dacewar a had’asu da khadijah

 

Mama tace zata tambayi khadijah taji ko akwai wanda take so idan babu? sai in fad’a mata yadda mu tsara dake”

 

Ummi tace bada muwa ko mai ake ciki kingaya mani”

 

Tare da hanging up d’in call d’in

 

Bayan fitar ss majalisarsu ya zaune yake jin gulmar dasu Nazeer keyi akan khadijah na cewa

 

Yarinyar gidan su safwan d’incan tacika wulak’anci, wani daga cikin su yace “ai wani d’an iskan saurayi ta lik’emawa ya hanata aure Allah kad’ai yasan abinda suke aikatawa”

 

Ss jiyayi zuciyarsa na tafasa, yasa yatashi Batare da yaji k’areshen zancen ba ya shiga gidan su khadijah

 

A dai_dai lokacin da Mama kema khadijah maganar in akwai wanda ta tsayar toh ta fad’i, dai-dai lokacin ss yayi sallama ya shigo hakan ne ya haddasa ma Mama yin shuru tare da amsa sallamarshi

 

Bayan sun gaisa, Mama ta tashi da niyyar shiga toilet tabarsu su biyu

 

Kallonta yayi yace “ke baki iya gaisuwa ba”

 

“Ina yini”

 

“lafiya, dama inason inyi magana dake ne”

 

Kallonshi tayi da kyau don har yanzu tana jin haushin korar ta da yayi a motarshi

 

Shikuwa bai kulataba ya cigaba da cewa

 

“dan Allah idan Jiddan sonki yake yakamata ya fito ya aureki kinga mutane sun samaki ido”

 

Idon tane ya ciko da kwalla tad’ago cikin takaici da jin haushin maganar shi tace

 

“to yaya ya akeson nayi, duk wanda yazo ina kulashi amma bada niyyar auren suke zuwa ba!

 

Toh koni zance azo a aure ni, ko kuwa kai zaka aure ni?”

 

Duk wannan maganar tana yinta cikin kuka da tsantsar b’acin rai!!!!

 

Batare da tsoron komai ba yakalleta cikin ido yace

 

“yes I will marry you and i promise to love you, take care of you till the end of my life”

 

Cikin firgici da kalamanshi khadijah ke Kallonshi tana girgiza kai

 

Duk abinda ss yace a kunnen Mama saboda ta dad’e tsaye batare da sunsani ba

 

Al’amarin da yasa Mama cikin farin ciki marar misaltuwa

 

Khadijah kuwa tashi tayi ta ruga d’aki tana wani irin kuka wanda nakasa gane ko na minene shi?

 

Ss jiyayi kamar yabita ya lallasheta amma kunyar idon Mama bazaisa yayi hakan ba

 

Mama zama tayi tace “dama suleman  kanason khadijah shine baka fad’aba kayi shuru”

 

 

 

Mama don naga tana da wanda take so shine yasa banyi maganar ba, kuma ko yanzu bana son kurabata dashi,

 

Shiyasa nace ma ummi tazab’a mani mata”

 

Murmushi Mama tayi tace banda abinka aishi wanda takeson iyayen shi sunce bazasu yi mashi aure yanzu ba

 

Kuma dama Ummi tayi mani maganar, har mun yanke shawarar had’aka da khadijah

 

Toh sai gashi fad’uwa tazo dai-dai da zama kaima kana sonta”

 

Ss yace “But Mama she can wait for him tunda naga she is 20 years”

 

Ajiyar zuciya Mama tayi tace

 

“suleman baka ganin bakin mutane,  saudat na gidan mijin ta ai itama yakamata tayi auren”

 

Kiran sallar magrib ne yasa ss yayi mata sallama ya wuce masallaci

 

 

 Ko ss zai Auri khadijah ?????

Ina Jiddan? Wane hali yake ciki?

 

 

 

 

 

 

 

         Mrs Abdul Sule

[1/17, 10:47 AM] Halima Mk: ????????????????????????

*HABIBI* *DA’IMAN*

 

 

 

*WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*

 

 

 

 

*DEDICATED* *SA’ADATU* *ALIYU* *KABUGA*

 

 

 

 

DABAZARMU WRITERS ASSOCIATION

 

 

 

           Page 46~50

 

 

 

 

 

 

 

 

Bayan kwana biyu da yin haka

 

Mama takalli  khadijah dake yankan a kaifa tace”yakamata kije gidan saudat kinga tun d’azu tayo waya bata jindad’i”

 

Hakan yasa tayi saurin gamawa tare da shiryawa cikin wata yellow d’in gown sai kwalar wuyan rigar ne bak’i don haka tayafa black d’in veil sai takalmi hills suma black sai wata k’aramar pose yellow

 

Tayi kyau sosai saidai wata rama da tayi

 

Har tafito zata tafi Mama tace ta shiga ta gaida ummi sannan ta wuce

 

Tana shiga gidan ummi dayake gidan babba ne saika wuce parking space sannan kashiga main palour gidan

 

Tana shiga taga ss zai shiga motarsa da alama fita zaiyi

 

D’auke kai tayi tamkar bata ganshi ba tare da sauri ta shige palour

 

Shiko ganin hakan yasa yafasa tafiya tare da zama cikin motar batare da yatafi ba

 

Tana shiga taga ummi cikin palour, sallama tayi sannan ta gaisheta

 

Bata wani jima da shiga ba tayi mata sallama zata tafi

 

Ummi tace “tun yanzu zaki tafi bazaki bari sai zuwa yamma kitafi ba”

 

Ummi gidan saudat zan wuce dayake batajin dad’i shine Mama tace inje na dubata da jiki”

 

Assha kice ina gaisheta da jiki Allah yabata lfy”

 

Ameen ummi zangaya mata

 

Rakota tayi  har harabar gidan, hango suleman tayi tace

 

“ashe kai baka tafiba mekake jira”

 

Shuru yayi dan baisan mezai ce mata ba

 

Ummi taci gaba da cewa “toh aishikenan saika aje k’anwarka gidan saudat”

 

Dama haka yakeso cikin ranshi batare da b’ata lokaci ba yayima motar key, ita kuwa khadijah bata iya yima ummi musu hakan yasa ta shiga

 

Bayan ta shiga ne yakalleta yace “fauziyya estate ko? Tace “eh”

 

Hakan yasa yafara driving batare da kowa yai magana ba har suka isa gidan

 

Kama murfin k’ofar motar tayi ta bud’e da niyyar fita sai taji ta a lock hakan yasa tayi saurin kallon shi

 

Murmushi yasakar mata sannan yace “khadijah meyasa kike gudu nah”

 

Kallon banza tamashi “meyasa zaka auri ne,? Kodan ka cutar danine, wanda bansa darajar mace ba shine za’ace mijina, don haka ina mai shawar tarka tun wuri kaje kace masu baka son wannan auren don ba zaman lafiya zamuyi ba”

 

“Ni bazance bansan abinda iyayena keso ba saidai ke ki fad’a masu bakya son zab’insu,

 

Kuma da kike cewa bansan darajar mace, ni kuwa nasan darajar mace don bantab’a wukanta wata ‘yan mace a rayuwa tah ba”

 

Murmushin takaici tayi tace

 

 

“shiyasa ranan nan da kad’au koni ka ajeni ahanya lokacin kuma gashi dare yayi”

 

Jiyayi gaba d’aya baida amsar da zai bata yasa yayi unlock d’in k’ofar

 

Ita kuwa ganin hakan yasa ta fita batare da tak’ara cewa komai

 

Saida yad’auki kusan 15 minute baitafi ba yana tunanin ita batason kishi ne yasa yayi mata hakan ba

 

Kuma batason yana maturk’ar sonta ba har take tunanin yajanye don shi yana ganin kamar Allah yahanata auren Jiddan ne don shi ya aure ta, saboda shi kad’ai yasan lokacin da yafara sonta

 

Amma yayima kanshi alk’awarin zai koya mata yadda zata soshi

 

Tana shiga gidan saudat taganta kwance akan kujera bayan tayi mata ya jiki ta tashi ta gyara mata gidanta tsab ta kunna mata turaren wuta har tad’auko roomfreshner zata saka, saudat tayi saurin hanata tace

 

“kada kisaka amai yake sani”

 

Murmushi khadijah tayi tace “kufa masu ciki tsiyar ku kenan”

 

Saudat tace “kema kin kusa zuwa lokacin”

 

“Dama nasan haka zaki fad’a, baki kojin haushin yadda aka rabani da Jiddan”

 

“ba haka bane kuma Jiddan iyayen shine keda matsala, ina mai tabbatar maki da nafi kowa jin zafin hakan”

 

Nan take kwalla ya cika idon khadijah, saudat na lallashinta suna cikin haka ne

 

Wayar khadijah ta fara ringing ganin Jiddan ne yasa ta dai-dai ta natsuwarta tare da pickin call d’in

 

“hello” Jiddan yace “khadijah meke faruwa naji muryarki kamar kinyi kuka”

 

Tace “bakomai”

 

“pls don Allah meyafaru” tace wallahi ba abinda ya………………………

 

Tarinda da yafara ne yasa bata idaba ta tsaya tana mashi sannu, sai kuma taji shuru nan take ta fara cewa

 

“yayana! yayana!! yayana!!! gashi kuma baiyi hanging up ba sai ta fara kuka”

 

Ita kuwa saudat sauri karbar wayar tayi takashe da niyyar ta k’ara kira.

 

Ko miyasami Jiddan?

 

 

 

 

 

     Mrs Abdul Sule

[1/17, 10:47 AM] Halima Mk: ????????????????????????

*HABIBI* *DA’IMAN*

 

 

 

 

*WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*

 

 

 

 

*DEDICATED* *TO* *SA’ADATU* *ALIYU* *KABUGA*

 

 

 

 

*IQRA* *WRITER’S* *ASSOCIATION*

 

 

 

              page 51~55

 

 

 

Wannan shafin na kune masoyan *habibi* *da’ima* ina jindad’in comment d’inku domin shike k’arfafa mani k’warin yin rubutuna #Ana tare#

 

Tana fara ringing aka d’aga sai naga tayi Murmushi sannan tamik’ama khadijah, ita kuwa har kyarma take don takarb’a tana sawa akunne taji Jiddan nacewa “lafiya” Ajiyar zuciya tasauke tace “yayana meyafaru naji muna waya kayi shuru? “Network ne saboda ni inajinki” Murmushi tayi tace “ilove you” yace “llove you too, ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameni don nasha gaya maki insha Allah atare zamu mutu koda kuwa bama tare” “toh yayana Allah ya yarda, amma fa wannan tarin naka yakamata kafara sha masa magani ” ” insha Allah” cikin ranshi kuwa yana cewa don baki san yadda nake jin tarin nan ba.

 

 

Bayan two weeks da faruwan haka akasa bikin khadijah da S.S abinka da masu hannu da shuni two month kawai akasa bikin

 

Tunda akasa ranan bikin khadijah tafara ciwo domin jin abin take kamar a mafarki, a b’agaren Jiddan kuwa saidai muce Allah yasawak’e don kullum cikin lissafin kwanakin yake iyayen shi kuwa basu da masaniyar abinda ke damunshi ba alhalin ciwo na nan nacinshi cikin rai

 

 

Sannu – sannu lokaci na k’ara tafiya kwanaki suna raguwa inda bikin ke k’ara kusantowa a yayinda zuciyar masoyan guda biyu sukejin kamar mutuwarsu ke tahowa, shikuwa ss har yana tunanin kamar baiyima masoyan adalchi ba musamman yadda yaga khadijah tarame ko kallonshi bata sonyi ga rashin had’in kan da bata bashi saidai dasu Iman suke ta shirye-shiryen su.

 

Su miemee ne sukayi sallama suka shigo tare da ankonsu da suka amso wurin d’inki da sauran kayan khadijah, zama sukayi miemee tace “amarya ga kayanki”  shuru tayi bata ko kalletaba sai Rabi’atu ta amsa tasamata cikin wardrop sannan tace “Ni ina mamakin khadijah ace nice na samu handsome guy kamar ss ga kud’i ai wallahi sai kunga k’arya”  mimie tace “ai ita kinsan bata wayeba shiyasa kikaga tana haka”  Ita dai khadijah har suka k’araci surutunsu suka tafiya batace masu komai ba don ita abinda ke damunta ya isheta, ihsan ce ta shigo tana cema khadijah “yaya khadijah ina d’inki na? ko kallanta batayi ba ballantana ta amsa mata, hakan yasa taje wurin Mama tana gayamata, Mama tace “taje yana d’aki ta dauko harda nasu seema da samrah  da yake kusan a can gidansu take yini saboda sune k’awayenta gashi yanzu sunfara zama ‘yan mata don yanzu jss two suke.

 

 

Yau takama wednesday inda ake ta shirye-shiryen bridelshower amma amarya tana cikin d’aki zaune tayi shuru kamar wata kurma, iman ce keta ta lallashinta tund’azu da tatashi tayi wanka amma tak’i suna cikin haka ne saiga saudat tashigo cikin ta kuwa har yatasa don yanzu yashiga five month, ta kalli khadijah tace “Mama tace kitashi kiyi wanka kafin tazo ta iskeki a wurin” jin hakan yasa ta tashi taje tayi wanka, kafinta fito iman ta fiddo mata kayan da zatasa, nan take naga tayi kyau tun kafin tayi kwalliya, koda yake bakasafai tacika yin kwalliya ba, haka aka gama bridelshower zuwa yamma kowa ya tafi gida duk abinda akeyi khadijah kallon kowa take don ko magana bata sonyi sai dole, dare nayi ta wuce d’aki ta kwanta tana tunanin Jiddan saboda yanzu Mama ta kwace wayarta ballantana ta kirashi taji sanyi aranta

 

Tana cikin tunanin haka maman salma tashigo ta zauna tace “khadijah kinga har yanzu baki ida shan magungunan kiba kuma gashi yanzu nadafa maki kaza don Allah kiyi kokari kiciyeta tunda  mazan yanzu kinsan dole mace ta had’a da gyara

 

Tashi tayi batare da tace komai ba saboda ita duk wannan abin da ake mata kallansu kawai take domin ba gyaran bane agabanta, aranta kuwa cewa take “Dama ace Jiddan ne da sainasha abinda yafi wanda kuke bani” amma yanzu data sha da kokartasha wannan ba damuwarta bane

 

Haka ta zauna taci kazar badan ranta nasoba, harta gama sannan maman salma tasa tashiga cikin toilet tayi wanka yaji had’in turaruka masu sanyi qamshi, dama tunjiya aka gama mata dilka sai wani kyau dafatarta tayi sai sheki take da laushi tare da wani irin sihirtaccen kamshi dake tashi daga jikinta.

 

Bayan angama tayi shirin kwanciya saiga ihsan da waya a hannunta tashigo tacemata “gashi ya muhsin nason magana dake inji Mama, har kyarma take ta amsa saboda a tunanin ta Jiddan ne tana d’auka taji muhsin ne nacewa “hello khadijah”  “Na’am ya muhsin ina jinka”

 

Dama sonake muyi wani sirri dake” “Ok”  “wallahi khadijah Jiddan yana cikin wani hali kuma gobe naji Mama nacewa zamu taho, toh shima yace gobe tun k’arfe 7:00am zai taho kuma yace yana son yaganki ko ta halin k’a-k’a” fashewa da kuka tace “ya muhsin tayaya zai ganni bayan gobe kamu za’ayi duk da sai k’arfe biyar na yamma amma nasan ba wanda zayabarni na fito”  “pls khadijah kitaimaka sannan kuma inason kigaya mani inda zai jiraki sannan ki kiyaye ki kula da kanki pls”

 

“toh kace ya jirani a GRA bayajidda road misali k’arfe 11:00am zansan yadda zanyi in fito”

 

Yace “toh amma ki kiyaye”  “to yanzu babu yadda za’ayi mugaisa”  “aibamu tare dashi” “Ok”

 

Bayan sun gama waya ta kwanta da tunanin yadda zatayi ta fita

 

Washe gari da misalin k’arfe 10:30am tace ma Mama tana so taje shagon da akayi mata saloon ta manta wasu kayanta da kud’i aciki Mama tace “ki aika ihsan da driver su amso maki mana”

 

“ai baxata basu ba saboda sai na mata bayani kuma kinga ni tasani batasan ihsan ba”

 

“toh aishikenan, amma ihsan tarakaki” toh amma bada musa zamu fita ba don naji d’azu abba ya aike shi kuma bana tunanin yadawo” to aisaiku hanzarta, cewar Mama”, zuwa tayi tayima ihsan magana suka tafi,suna fitowa get suka hango su samrah sun taho, “yaya khadijah kinga su samrah sun biyo mani muje wurin kunshi ko” khadijah tace “kutafi kawai amma inkun dawo kijirani gidansu seemah idan nadawo zankiraki” suna tafiya itama khadijah ta shiga napep, misalin k’arfe 11:20am ta isa wurin batasha wahala ba ta hango motarshi yayi parking a wurin wata bishiya dayake Unguwar shuru take sai akashe ma mutum batare da ansani ba bakajin motsin komai sai kukan tsuntsaye dake ta shawagi sararin samaniya saboda yanda area take shuru

 

Tana zuwa taganshi back seat ya d’an kwanta, ganin k’ofar a lock take yasa tad’an fara yima shi knocking ashe bacci yafara ita kuma bata saniba saboda yasa eyeglesses mai duhu saida tak’ara knocking sannan yatashi ya bude mata ta shiga

 

Tana shiga ta zauna tare da rufe k’ofar tace mashi “miyasa kazauna a backseat?”  “gajiya nayi da zama shine nadawo nan bansa sadda bacci ya d’auka ni ba”  eyeglass d’in dake idanshi tacire tare da kama kumatunshi duka biyun ta girgiza, sannan shima yakama nata ya girgiza sukayi Murmushi domin wannan itace d’abi’arsu insun had’u sukeyinta sannan tace “daga gani baka bacci shiyasa” Hakan yasa ya matso kusa da ita yana rik’e hannunta d’aya yana murzawa tare da d’aura gudan saitin zuciyar shi sannan yakalleta cikin ido yace “toh khadijah ya xanyi inyi bacci, yanzu dagaske rabuwa zamuyi?” cikin muryar kuka tace  “toh ni yayana ya xanyi……………………bata k’arasa fad’in abinda zata ceba sanadin tarin da yafara ba kaukautawa

 

 

 

 

 

 

        Mrs Abdul Sule

[1/17, 10:47 AM] Halima Mk: ????????????????????????

*HABIBI* *DA’IMAN*

 

 

 

 

*WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*

 

 

 

 

 

DEDICATED TO SA’ADATU ALIYU KABUGA

 

 

 

 

 

 

    Page 56~60

 

 

 

 

Kuka tafarayi sosai ta fad’a saman kirjinshi tana buga-buga bayanshi, a hankali tarin yafara raguwa saidai ita takasa barin kukan da take kuma takasa tashi a saman kirjinshi, gashi har veil d’in da tayi rolling kanta dashi ya cire, hakan yasa Jiddan baisan lokacin da yasa hannun shi ya fara shafa gashin kanta ba musamman yadda  yasha gyara ga wani sihirtaccen kamshi dake tashi daga jikinta

 

D’agowa yayi da fuskarta yafara lashe hawayen da ke zuba daga idaniyarta

 

Ita kuwa jin abinda yafara matane yasata daina kukan da take ta shiga duniyar tunani, batayi aune ba taji ya had’a bakunansu yana tsotsa kamar yasamu sweet, da kyar tayi nasara zare nata bakin daga nashi 

 

D’ago idonta tayi a fusace da niyyar yima shi magana kallo d’aya tayi mashi ganin yadda idanuwanshi suka koma sai taji tausayinshi sosai

 

Shikuwa ganin ta kwace bakinta yasa ya fara shinshinar wuyan ta sanadin doguwar rigace jikinta shiyasa yakai hannu ya zage zip d’in rigar, baisan sadda ya k’ara rikicewa ba duk ya fita hayyacinshi  wani irin romancing d’inta yake sosai

 

Kamar a mafarki yake jin kukanta hakan yasa yadawo cikin hankalinshi tare da rufe mata jikinta yakuma  yimata rolling veil d’inta

 

K’ara rungumeta yayi tare da sauke numfashi a hankali sun d’auki kusan 5 minute babu wanda yace komai

 

Jiddan ne yayi k’arfin halin cewa “khadijatu kiyi hak’uri wallahi bansan sadda hakan tafaruba kuma kinsan wannan ba hali na bane”

 

D’agowa tayi da niyyar yima shi magana sai ganin hawaye tayi a fuskarsa tace

 

“yayana miyasa kake kuka” yace

 

 

khadijah abubuwa da yawa gashi gashi zan rabu dake ga kuma abinda nayi maki yanzu ina zansa kaina”

 

“yayana nasan ba halinka bane harda zafin rasa ni da zakai ne” yace

 

“kinyarda badan sha’awa yasa nayi maki haka ba?”

 

“eh yayana” zoben dake hannunsu suka jera yatsun dake jikin zoben, ya kalleta yace “khadijatu inasonki har gaban Abada”

 

Lokaci d’aya suka sake fashewa da wani kuka nazafin rabuwa da abinda kakeso sun d’auki lokaci mai tsawo a haka

 

Da kyar suka lallashi junansu sanna khadijah tayi mashi sallama zata tafi, har ta bud’e murfin motar da niyyar fita ya k’ara jawota ya manna mata kiss sannan yace

 

“Khadijatu promise me kada ki manta dani”

 

Murmushin da yafi kuka ciwo tayi tace “I promise you yayana” yanzu bazan sake ganin kiba ko khadijatu?

 

Ganin kamar zaiyi kuka yasa tace “a’a munanan tare har Abada, kuma da anbani waya ta zankira ka”

 

Bud’e k’ofar motar tayi ta fita batare da tak’ara kallanshi ba domin bata son taga yanayin damuwar da zaishiga

 

Haka takoma gida bayan ta kira ihsan suka shiga gida, tana zuwa d’aki ta k’ara fashewa da wani kukan saboda yadda ta tuna Jiddan da kuma halin dayake ciki na rasata da zaiyi dakyar tasamu ta tsagaita kukan gudun kar asan halin da take ciki domin ‘yan biki ne cike da gidan

 

Maraice nayi aka fara kamun amarya a zanbrush inda akayi decorating d’in wurin da komai ash and yellow sai chairs d’in white, suma ‘yanmatan amarya yellow d’in kaya suka sai head ash

 

Amarya naga anshigo da ita cikin hall d’in tasaka wata had’ad’iyar gown yellow sai sharar k’asa take, da yake akwai layi layin white a jikin gown d’in sai tasaka white head tare da wani white d’in mayafi da ya rufe duk jikinta harda fuska

 

Can naji ‘yan group d’in Garkuwan fulani nacewa “Ina ango yake yazo ayi bud’ ar kai ko munga fuskar amarya”  Aikuwa kamar dama jira yake suyi magana, saiga S.S da abokanan shi anshigo suna ta washe baki

 

Nan take bada wani b’ata lokaci ba abokan ango suka sayi fuskar amarya akan naira dubu d’ari sannan aka fesheta da turare kafin ango ya bud’e fuskar amarya

 

Muguwar fad’uwar gaba ss yaji a lokacin da yabud’e fuskar khadijah saboda baiyi tunanin kyanta yakai haka ba amma ba wannan ne yafi damunshi illah yadda yaga khadijah ta k’ara ramewa ga damuwa a fuskarta

 

Matso wa yayi dai-dai kunnanta yace “pls khadijah ki d’aure ki saki fuskarki kada mutane su fahimci wani Abu” kwalar dake cikin idonta ta had’iye sannan tayi Murmushi da yafi kuka ciwo batare da tace komai ba

 

Ganin haka ne yasa Iman tayi saurin tahowa wurinta don bata nan aka fara bud’ar kan tana can wurin ba ‘yan group d’in pherty novel’s seveniors gudun kada suyi rigima lol ????

 

K’ara sauri take taga ta isa wurin khadijah jitayi tayi karo da mutum taiyi baya zata fad’i shi kuma yayi saurin rik’ota da sauri gudun karta fad’i

 

Tace “am sorry banganka ba ne” daga haka bata sake cemai komai ba ta wuce shikuwa ganin hakan yasa ya bita

 

Tana zuwa, ahankali tace ma khadijah “don Allah karkiyi kuka kinji”  d’aga mata kai kawai khadijah tayi, saiga Adnan da yabiyo bayan Iman sallama yayi Iman ta amsa mashi yace “baiwar Allah wurin ki nazo”

 

“amma ai nabaka hakuri”

 

“ba shine damuwa taba”

 

“to ina jinka”

 

“taimako ne zakiyi mani kidaina tafiya da sauri don gudun kada wata rana kiyi mani asara, sannan kuma inaso kibani number wayarki”

 

Murmushi Iman tayi tace “bani da waya” daga haka ta tafi bata kara cewa komai ba, shikuwa ss binsu kawai yake da kallo

 

 

Haka aka gama taro aka tashi lafiya, amma Adnan saida yasan yadda yayi ya amshi number Iman

 

Ana dawowa daga kamun wani irin zazzab’i mai zafi ya rufe khadijah har saida Mama ta kira ss tagaya mashi

 

Bayan ya dubata ne yace ma Mama “malaria ce, data sha magungunan nan insha Allah zata sauka”

 

Anty fa’iza ce tace gaskiya a sanar da mutane gobe ba wata dinner da za’ayi abarta ta huta

 

 

Bayan sallah juma’a,dubun nan jama’a suka shaida d’aurin auren Dr Suleman Shehu Matazu da khadijah Usman Abdallah akan sadaki naira dubu hamsin, wanda manya yan kasuwa da k’usoshin gwamnati suka halarta

 

Ango nata gaisawa da mutane ya hango muhsin hakan yasa yamatsa suka gaisa sannan ya mik’ama na kusa dashi hannu d’agowar da zaiyi sai yaga ashe da Jiddan ne suka gaisa baisani ba

 

Jiddan ne yayi k’arfin hali yace “ina tayaka murna Allah yasa alkhairi”

 

A yanayi da yayi maganar da kyar ya ida shiyasa ss yaji matukar tausayinshi, dafa kafad’arshi yayi yace

 

“Jiddan kayi hakuri bawa baya samu sai rabonshi, don har ga Allah banso rabuwarku ba kuma nasan harna mutu bazan daina zargin kaina akan rabuwarku ba”

 

Da kyar Jiddan yace “Na sani kuma ina godema Allah da khadijah ta fad’o hannunka don nasan kai mutunan kirki ne, abinda zan rokeka shine ka rike khadijah amana pls, don Allah kayi hak’uri da ita kada kabata mata rai nasan zaka sha wahala kafin ka shawo………………….bai ida maganar ba tarin shi ya sark’eshi ss ne da muhsin keyi mashi sannu sada yalafa da tarin sannan ss yace

 

“nayi maka alk’awari insha Allah zanrik’eta amana”

 

Kiran da akayi mashi ne yasa ya tafi shikuwa muhsin yaja Jiddan suka shiga mota, sai kuma tarin shi yatashi har yana zubda jini cikin rud’u muhsin yace “Jiddan kaga abinda nake gaya maka kaje asibiti kak’iya yanzu gashi nan” don haka da sauri yaja motar zuwa Asibiti

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button