Uncategorized

HABIBI DA’IMAN 21-40

 

          *Page* *21* *~* *25*

 After one year 

     Wani farin dogon saurayi na gani wanda bazai wuce shekara 23 ba, amma baya da k’iba, fuskarsa d’auke take da dogon hanci kamar biro, sai girarshi da take a cike, gashin kansa kamar na larabawa ga fuskarshi sumul ba alamun yana da saje.

 Matsawa nayi k’adan naga ashe Jiddan ne yake tahowa cikin farin ciki, sauri yake yaje wurin habibati d’inshi.

 

Yana isa ya lallab’a ta bayanta, tare da dafa hannayenshi,

 

Hakan yasa khadijah ta juyo da sauri da niyyar  yin ihu

 

Kawai saiya kama yi mata dariya, hakan yasa tafashe da kukan shagwab’a tana cewa

 

“wallahi yaya sai na rama” biyo shi tayi da niyyar ta buga mashi book d’in dake hannunta

 

Kamata yayi tare da zaunar da ita ya had’e hannayenshi ???????? yace “i’m sorry, ke d’ince ai baki da k’iba shiyasa nike maki wasan yara”

 

“uhmmm amma dai ba ramamma bace”

 

Yace “shiyasa nake ce maki everthing about you is moderate”

 

Kallanshi tayi tace “ya exam”

 

“fine, kefa?”

 

Nima lfy lau

 

Yace “my princess yakamata in tashi in tafi inshirya, don inason la’asar tayi mani a kaduna”

 

Raurau tayi da ido alamar kuka tace “Allah ya kiyaye hanya”

 

Tsugunnawa yayi agabanta yace

 

“pls khadijah menene na kuka gobe kamar yanzu kema kina kaduna.

 

Pls dan Allah karkiyi kuka kinsan bana so yana tada mani hankali”

 

Yadda taga duk ya birkice mata yasa taji tausayinshi tace “toh yayana na  daina” tare da yin Murmushi”

 

Saida yakama hannun ta ya murza zoben hannunta tare dayi mata kiss sannan suka tafi.

 

 

Washe gari da wuri su khadijah da Mama suka wuce, safwan ne yayi driving d’insu, don Baba baya gari sai ranan d’aurin aure xaije.

 

Ihsan dake gaban motar ta ishi ya safwan da surutu yace

 

“idan bakiyi mani shuru ba zan sauke ki a daji kura ta cinyeki”

 

Aikuwa shuru tayi bata k’ara magana ba har bacci yayi gaba da ita.

   Suna isa kaduna khadijah ko abinci bata tsaya ciba, ta fito da niyyar zuwa wurin Maman su Jiddan, cin karo tayi dashi shida muhsin suna tahowa, hakan yasa muhsin ya wuce yana “cewa taje ta dawo akwai labari”

 

Ita kuma da Jiddan suka wuce wurin Mama.

 

 

  Ummi ce zaune a palour, s.s yayi sallama ya shigo

 

Tace “yauwa dama suleman kai nake jira don kasan gobe da wuri zamu wuce kaduna”

 

Dama nima nazo ince maki ku shirya k’arfe 8:am zamu tafi don haka su seema suje su kwanta da wuri”

 

 

  The following day, bayan antaso daga sallar juma’a dubanan mutane suka shaida daurin auren Saudat Aliyu da Inspector Kabeer k. Mashi.

 

Su muhsin da Jiddan ne suka k’araso inda mutane suke suna gaisawa daidai lokacin da Jiddan ya mik’ama s.s hannu ya dago suka hada ido, hakan yasa Jiddan yayi wani kala, Batare da yanuna ba yabasar sai bayan suntafi ne yake cema

 

“Muhsin nida naga wancan guy d’in wallahi hakanan naji gabana ya fad’i, i don’t no why”

 

Muhsin yayi Murmushi yace “kada kadamu dama sometimes mutum najin irin haka.

 

 

Amarya Saudat ansha kyau angaji su Asiya da Rabi’atu duk sun zo, khadijah kuwa sai hidimar biki akeyi, amma abinda ke damunta bai wuce yadda kowa yake ganin kamar tana korar samari bane wai don ta auri mai kud’i, don taga tana da kyau, ita kuwa a ganin ta bazata tab’a soyayya da kowa ba sai Jiddan don akanshi tasan so kuma akanshi zata k’are

 

Yanzu gashi ana bikin Saudat kowa na cewa ita tak’i aure.

 

Haka akasha shagalin biki, da dare kuma aka wuce Arabian nyt.

In tsaya fad’a maku kyan da Amarya da ango sukayi zai d’auke mu lokaci bamu gama ba, amma sunsha kyau ba k’arya.

 

An k’awata wurin da komai white and black inda maza sukayi shigar white d’in dress da black d’in hula, mata kuma black gown and white shoes.

 

Can na hango s.s ya keb’e shi kad’ai yana latsa phone d’inshi, ‘yan mata kuwa sai kallon shi suke don sunga hansome guy “ni halima nace to fah!!”

 

 

Ihun Rabi’atu dasu mimie naji shiyasa na juya don ganin me suke ma ihu

 

Jiddan da khadijah ne suka shigo, ni kaina dana ke d’auko maku rahoton saida na firgita saboda kyau da dacewar da sukayi ga wani red lipstick da khadijah tasa, sunyi kyau kamar wasu couple.

 

Hakan yasa s.s ya d’ago don ganin me akema ihu!!!

 

Kawai sai ganin khadijah yayi da wani kyakyawan saurayi wanda kamar yasan face d’inshi, Aikuwa baisan sadda yamik’e cikin fargaba da faduwar gaba ba yace “what”

 

Hakan yasa nai saurin Kallanshi nace toh ????, shi kuma wannan lafiya????

 

 

 

 

          Mrs Abdul Sule

[1/17, 10:46 AM] Halima Mk: ????????????????????????

*HABIBI* *DA’IMAN*

 

 

 

*WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*

 

 

*DEDICATED* *TO* *SA’ADATU* *ALIYU* *KABUGA*

 

 

 

DABAZARMU WRITERS ASSOCIATION

 

             Page 26 ~30

 

 

 

 

 

    Gani nayi kwashi keys d’in motarsa da wayoyinshi ya fita a fusace ba tare da ya kalli inda suka khadijah suke ba, hakan yasa na maida kallona gunsu Jiddan dan kada abani labari

 

Jiddan nagani yana jan habibatin tashi, ita kuma tana turjewa yana cewa

 

“yau sai kinyi rawa”

 

Hakan yasa yajanyo ta jikinshi tare da rik’e mata hannu d’aya yana rawa da ita a hankali

 

Ita kuwa sai faman sunne kai take alamar jin kunya.

 

Can na hango ‘yan group d’in Mk na mata xallah suna ta kwasar shoky????????, su mairo Usman sai tura take away ake cikin jikka, birchi ko cewa take banshi haka ana kallanmu, ke basu ganin mu shoky suke kwasa????

 

 

Haka aka sha shagalin arabian nyt

 

Anyi biki ank’are lafiya anci ansha, gobe ne za’a kai amarya gidan mijinta domin itama a katsina zata xauna sannan ta ida karatun ta.

 

 

Washe gari haka su khadijah da sauran k’awayen amarya suka shirya tare da amarya sai katsina ta dikko d’akin kara kunya gareku badai tsoro ba.

 

Jiddan kuwa baiji dad’in tahuwar ta ba, saboda shi sai hutu yak’are zaidawo

 

Direct gida su Mama suka wuce da saudat kasancewar sai bayan ishsha’eh zaa kaita

 

Mama da ummi ce dasauran yan uwa suke ma amarya nasiha kan zaman takewar rayuwar aure da abinda ya k’unsa

 

Shikuwa s.s bayan fitarsa daga wurin dinner, tafiya yayi masaukin su, shigarsa d’akin baixarce ko ina ba sai toilet yasa karma kanshi shower tare da tunanin meyasa yakejin haushi don yaga khadijah da wani

 

Hakan yasa the following day da safe yakoma katsina

 

Su khadijah dare nayi Misalin k’arfe 8:00pm  suka kai amarya gidanta

 

Saidai kuma a can gida s.s yaje yana neman khadijah ta dafa mashi abinchi bai tadda taba hakan yasa ya biyota gidan saudat

 

Sukawa bayan sun aje amarya, ita dasu Asiya suka fito da niyyar amaidasu gida

 

Sai kawai taga motar s.s, shikuwa da yaganta saiya fito tare dayi mata alama da tazo,

 

Tana zuwa taga ya shiga cikin motar tare da bude mata gaban motar alamar tashi ga

 

Hakan yasa ta shiga Batare da musu ba

 

Jan motar yayi suka tafi

 

Tafiya suke amma ba wanda yace ma d’an uwansa komai

 

Can ya daure yace “waye naganki dashi jiya?”

 

“tace ina?” harararta yayi yace “wurin dinner”

 

Murmushi tayi tace “au ya Jiddan”

 

Kallanta yayi “dama kina da wani yayan bayan safwan”

 

Kallan mamaki tayi mashi sannan tayi fari da ido tace

 

“Aishi wannan na daban ne”

 

Batare da ya kalletaba yace “kamarya”

 

Batayi shayin komai ba tace “saurayi na”

 

Bata ida fad’in maganar taba dai-dai lokacin sun iso kusa da k’ofar gidan yaja wani mugun birki, cikin tsawa yace

 

“fitar man a mota”

 

Hakan yasa ta fita tana kuka, wai yau itace na miji yacima mutunchi Batare da tayimashi komai  ba!!

 

Haka ta shiga gida tana kuka,

 

Yana daga cikin motar yana hangeta da yadda take kuka sai yakejin bai kyautama zuciyar shiba da yayi mata haka

 

Toh amma shima baisan dalilinshi nayin Hakan ba

 

Abinchi da baa dafa mai ba kenan ya koma gida ya kwanta cikin tsananin damuwa

 

 

           ********

 

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya s.s kullum yana cikin tunanin har abokinshi Adnan ya gane sannan ya tabbatar mashi da son khadijah yake shiyasa yake shiga duk wani hali idan yaganta da wani

 

Take yafara tunanin ta ina zaifara shiga rayuwar ta bayan ya fahimci tana da wanda take so

 

Sannan shibai masan ta yaya zaifara tunkararta ba, hasalima baitab’a soyayya ba

 

Baisanma yadda akeyima ‘yan mata ba gashi baison abinda take so da wanda bataso ba

 

Kuma bama yajin zai iya kaskantar da kanshi wurin ta yace yana sonta gudun kada tarenashi.

 

 

  A bangaren khadijah kuwa bata k’arasa s.s a idon ta ba tunranda abin ya faru, sau d’aya ya shigo ya gaida Mama, tana jin sallamarsa tayi sauri ta shige d’aki dan wani irin haushin shi da tsanarshi takeji, kuma tayi alwashi sai ta rama abinda yayi mata duk daran dad’ewa

 

s.s da Adnan kuwa sungama shirya yadda zasu billoma al’amarin domin shi s.s yace bayason a cutar da kowa ko Jiddan ko ita khadijah

 

Hakan yasa suka fara bincike akan yanayin soyayyar tasu

 

 

 

 

 

                Mrs Abdul Sule

[1/17, 10:46 AM] Halima Mk: ????????????????????????

*HABIBI* *DA’IMAN*

 

 

 

*WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*

 

 

 

*DEDICATED* *SA’ADATU* *ALIYU* *KABUGA*

 

 

 

DABAZARMU WRITERS ASSOCIATION

 

 

           Page 31~35

 

 

 

*Wannan* *shafin* *naki* *ne* *my* *lovely* *sis Asiya Mk* *Allah* *ya* *jib’anci* *lamuranki*

 

 

 

 

 

 

 

 

Sannu sannu abin yaci gaba da damun S.S hakan yasa ya kasa jurewa yaje ya samu safwan da maganar yanason ya bashi number muhsin yayan saudat

 

Safwan yayi mamaki ya akayi ya sanshi? Amma sai ya share yace “lafiya dai ko?”

 

No ba wani abu bane kawai na hadu da yaron ne a wurin bikin saudat kuma nayi mantuwa a wurinshi”

 

Batare da wani tunani ba yabashi number

 

Bayan S.S yakoma gida ne yazauna a d’akinshi yayi dialing number muhsin saida yabashi 2 miscall, ana ukkun ne yayi Receiving call d’in tare dayin sallama

 

Sannan S.S yace mashi “zaka iya tuna wani wanda kuka gaisa a ranan daurin auren saudat?”

 

Shuru muhsin yayi na d’an wani seconds sannan yace mashi “gaskiya a’a”

 

Da farko suna na Dr suleman shehu matazu mune neigbour d’insu khadijah”

 

Muhsin yace “am sorry kasan bansaka a face ba saidai labarinka nakeji a wurinsu safwan”

 

S.S yace “alright ba damuwa, amma mungaisa dakai ranan daurin auren saudat.

 

So dama nakiraka ne inji when are you free inzo muyi wata magana da kai”

 

“No problem dama ranan saturday Mama zata aiko ni katsina so in nazo sai muyi maganar inba damuwa? “

 

S.S yace “Ok nothing” tare dayin hanging up

 

 

Daga ranan wednesday zuwa saturday S.S jiyayi kamar anshekara saboda k’agara da yayi su hadu da muhsin don jin abinda yakeson sani game da khadijah

 

Amma saboda tsabar miskilanci bai yadda wani ya gane halin da yake ciki ba

 

Ranan saturday kuwa da wuri yagama duk wani abinda zaiyi gudun kar muhsin ya kirashi yana busy

 

Da misalin k’arfe 2:15 pm muhsin yakira shi yace su had’u soli centre

 

Batare da b’ata lokaci ba ss ya isa wurin, bayan sun gaisa ne yayi gyaran murya sannan yace

 

“dama akwai wani guy fari sosai wanda naganku tare ranan daurin aure ance neigbour d’inku ne, shine nakeson naji miye alak’arshi da khadijah?”

 

Cikin mamaki muhsin yace “amma lfy kake tambaya akanshi?

 

“No bakomi kawai dai yadda naga ya rik’eta ne ranan dinner hankalina bai kwanta ba, so kasan Yaran wannan zamanin sai a hankalina, a matsayina wanda nake ganin tamkar yayanta wanda suka fito ciki d’aya”

 

Muhsin yace “kuma fa haka ne, amma da kasan tarihin su bazaka ce wani abu bane duk da wannan ma abun dubawa ne”

 

S.S yace “inason kagaya man waye Jiddan don  hankalina  ya kwanta?

 

Tun anan muhsin ya harbo jirginsa saidai ya share yace bari ya tabbatar sannan

 

Sunan mahaifin Jiddan Abubakar sai mahaifiyarshi Fatima wanda auren zumunci ne shida ita, Jiddan shine d’a na biyu a wurin su

 

Soyayyar Jiddan da khadijah tasamo asaline tun muna da shekara 9 lokacin ita kuma tana da 5 years

 

Wata rana muna zaune a k’ofar gidanmu suka fito da gudu ita da yara suna wasa, ganin muna k’ofar gidan zaune ita kuma ba kallabi akanta yasa ta koma ta d’auko kallabinta, sanadiyar hakan ne yasa yaji ta burgeshi tunda daga ranan yake mutuwar son khadijah don akwai wani lokaci data dad’e bata zo hutu ba har rashin lfy ya kwanta

 

Lokacin da yakai kan gab’ar balagarsa da khadijah yafara mafalkinshi wanda ni kad’ai nasan da haka saboda bama boye ma junan mu damuwar mu

 

Saboda haka ina da linking akan Soyayyar su domin ni na rink’a tusa ma khadijah sonshi a ranta tun bata son kowaye ba”

 

Asirtacciyar ajiyar zuciya S.S yasaki tare da fad’in

 

“Allah ya tabbatar da abinda yafi zama alkhairi”

 

Sannan yatashi cikin mutuwar jiki yayi mashi sallama sannan ya wuce gida

 

Shikuwa muhsin a lokacin ya tabbatar da zarginsa akanshi saboda yadda ya hango tsananin son khadijah da kishin ta fuskarshi, hakan yasa ya tab’e bakin shi alamar shiya sani, sannan yatashi ya tafi.

 

“nikuma nace oh ni Mk haka zakuyi ma ss ????

 

Bayan komawar ss gida yakira Adnan yake fad’a mashi yadda sukayi da muhsin

 

Sannan yake ce mashi “ni gaskiya bazan iya raba wannan Soyayyar ba domin zan shiga hakk’insu, saidai inshi Jiddan ne yajanye da kanshi

 

Don haka zanyi kok’arin b’oye abinda ke raina har lokacin da Allah zai yaye mani sonta”

 

Take Adnan ya goyi bayan shawarar abokin nashi tare da mashi fatan alkhairi.

 

 

 

 

 

 

 

         Mrs Abdul sule

[1/17, 10:47 AM] Halima Mk: ????????????????????????

*HABIBI* *DA’IMAN*

 

 

 

*WRITED* *BY* *HALIMA *Mk*

 

 

 

 

*DEDICATED* *SA’ADATU* *ALIYU* *KABUGA*

 

 

 

 

DABAZARMU WRITERS ASSOCIATION

 

 

 

      Page 36~40

 

 

 

A yanzu hutun su khadijah yak’are sun cigaba da zuwa school

 

Tana zaune a class ita kad’ai kasan cewar damuwa tayi mata yawa, sai ga Iman da zee sun shigo da yake a hostel suke zaune

 

Ganin khadijah cikin damuwa yasa Iman ta dafa ta tace

 

“Aminiyata miye damuwarki”

 

Nan take tagaya masu abinda Mama tace mata

 

Zee tace “toh me zai hana idan Jiddan yazo kigaya masa”

 

Nima shi nake jira ya fito daga class kinsan yau ya dawo kuma bamu haduba”

 

K’awaye nagari suke baka shawara maikyau nan take suka fara kwantar mata da hankali akasin mimie da Rabi’atu suna iya yi mata dariya, shiyasa bata cika gaya masu damuwarta ba

 

Da yake iman da zee iyayensu masu kula ne basu barin su yawo shiyasa ko bikin saudat basu jeba saidai fatan alkhairi dasuka yimata

 

Jiddan na hango yana ta sauri yaje wurin hrtcon d’inshi bcos tun bikin saudat raban shi da’ita

 

Ya kuwa yi sa’a ita kad’aice don su zee suntafi nan suka barta a class

 

Tun kafin ya k’arasa inda take ya fuskanci tana da damuwa ga wani Haske da tak’ara

 

Ita kuwa shuru tayi ta kura mashi ido tanajin sabuwar k’aunarsa nak’ara ratsa tah

 

Zama yayi tare da rik’o hannunta yasaka mata wata leda yace

 

“canko menene anan ciki”

 

Kallonshi tayi tare da fad’in “yayana ya za’ai nasani”

 

“Ok bari na bud’e kila ki tuna”

 

Kwance ledar yayi tare da zazzage abinda ke ciki sai gawasu beads guda ukku sun fad’o

 

Dasauri naga khadijah ta d’auko su tana cewa

 

“yayanah ai banmata lokacin da suka cire daga kitsona ba nace kamaida mani kace baka iyaba nace toh ka aje mani ashe haryanxu suna nan”

 

“khadijah kenan ai duk abinda ya shafeki ina mutuwar sonshi kamar!!! 

 

Bai ida fad’in abinda zai fad’a ba ya dafe saitin zuciyar shi”

 

Ita kuma hakan da yayi kawai sai yasa tafara dariya

 

Hakan kuwa yayima Jiddan dad’i ganin ta fita daga damuwarta

 

Saida yabari tagama dan kanta sannan yace

 

“khadijatu” yanda taga ya kirata yasa ta maida natsuwarta kanshi

 

“Na’am”

 

“menene damuwarki?”

 

Nan take wasu hawaye suka zubo mata, tare da gaya mashi yadda sukayi da Mama

 

Shuru yayi na wani lokaci Batare da yace mata komai ba

 

“kada kidamu khadijatu nasan iyayenki bazasu bari har saina gama karatu nasamu aiki ba sannan muyi aure, musamman yadda suke son suga kinyi aure da wuri

 

Amma karki damu zan fad’ama Mama halin da ake ciki domin tayi mani alk’awarin aurenki”

 

Da haka yasamu ya kwantar mata da hankali

 

Da Jiddan ya fad’ama Mama tace “kabari zanyima mahaifinka maganar”

 

Bayan tayi mashi maganar yace shi baisan da wannan xance ba saboda shi yafi son d’anshi yayi ilmi mai zurfi

 

Sannan idan ma ya aure ta dame zaiciyar da yarinyar mutane don shi bazai yima d’anshi auren gata ba

 

Kuma yarinyar da yakeso ba wani nisa ke tsakanin suba ballantana ta jirashi don haka ni banyadda da ba.

 

Haka Jiddan yayi ta Damun Mama data taimaka mashi da jari yafara sana’a kafin lokacin da zai gama makaranta ya auri khadijah

 

Mama kuwa tunani take tabashi ya fara kasuwanci kafin lokacin auren koko tabi shawarar mijinta?

 

Duk da dama yace bai amince da auren ba

 

Take ta yanke shawarar goyon bayan mijinta shiyasa ma tacema Jiddan yayi hak’uri

 

Tundaga wannan al’amari da yafaru Jiddan yashiga matsananciyar damuwa daga shi har khadijah karatunsu yaja baya saboda tsananin damuwa da tayi masu yawa kullum cikin neman mafita sukeyi amma abin ya gagara

 

A b’angaren khadijah kuwa kullum Mama fad’a take mata data dunga kula samari ga wani faisal abokin safwan da yadad’e yana sonta amma tak’i kulashi harya hak’ura ya fara neman wani auren

 

Sakamakon haka khadijah ta k’udir ta aranta koma wa yazo zata fara kulashi don ta fidda kanta  daga zargi

 

Duk wannan wainar da ake toyawa ss baisani ba

 

Amma yakasa fidda son khadijah aranshi gashi ummi da daddy sun isheshi da maganar aure

 

Jiddan kuwa duk wata sana’ar hannu da yasan zaiyi ya samu kud’i yanayi saidai yasan bazasu isheshi ya auri khadijah ba balle yarik’eta

 

Shiyasa yake ce mata tarink’a bin maganar Mama kila hakanne yafi zama alkhairi.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button