Uncategorized

HAJNA 13-14

 ♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️ 

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

PAGE 13-14

********************

Washe gari da safe Fahna ta shirya ta bar garin, da isar ta Gusau kai tsaye Maryam hotel ta nufa, inda suka aje zasu haɗu da Alhaji Musa.


     Kwance yake a ɗaki yana jiran Fahna, ƙofar ɗakin aka turo, Fahna ce ta shigo, faɗa mishi tayi a jiki “wash! Alhaji jikina duk ciwo yake min “, murmushi yayi yace “bari kiyi wanka in miki tausa”, tashi tayi ta shiga toilet, sai da ta share awa ɗaya tana wanka sannan ta fito, daga ita sai towel, gaban mirror ta tsaya, wata shegiyar riga ce a hannu ta, wanda da ita da babu duk ɗaya, sanyawa tayi, wanda ya fiddo da jikin ta, Alhaji Musa kuwa tuni ya rikice, tafiya take yi tana girgiza jikin ta har ta kawo bakin gado, kwantawa tayi, Alhaji Musa ya fara shafa jikin ta, yana mata tausa, sai wani lumshe ido take, daga nan labari ya canza zani, rungume ta yayi ya fara romancing ɗinta, ita ko wani sound take saki tana jin daɗi, ni kuwa na ja musu ƙofa na fita.



 Ban zame ko ina ba sai gidan Abuja????.


Qaseem ne yake waya “what! Wai shi Farween me yake so ne, how dare him”.


Masu karatu wasu daga cikin ku suna so su san asalin abunda ya kawo gaba tsakanin Qaseem da Farween.


Tuna baya.

*******” ‘

Watarana Qaseem ya fito aiki sai ya sami an kwashe kayan shi daga office ɗin shi zuwa ƙaramin office, wanda hakan yasa Qaseem jin haushi sosai ya nufi office ɗin shugaban su, a fusace yace “ranka ya daɗe mike faruwa ne? “, “da mi fa”, shugaban su ya tambaya, Qaseem yace “nazo na sami an canza min office ne “, “eh Farween yafi ka cancantar gurin”, Qaseem ji yayi kamar an daka mishi mashi, abun kamar wasa Farween ya kwace mishi duk wani matsayi, wanda shi Farween da gangan yake yi, an biya shi kuɗi ne dan yayi haka, wannan dalilin ne yasa Qaseem da Farween basa jituwa, kullum gabar ƙaruwa take yi, daga baya kuma sai Farween ya daina dan dama tun farko aikin na shekara ɗaya ne, kuma ya gama an biya shi kuɗi, amma wannan gabar bata tsaya saboda ya riga ya ƙuntata ma Qaseem.

             Wannan shine tushen gabar su, wanda hakan ba laifin kowa bane face Farween.




********************

Yanzu ma da kuka ji yana faɗa, Farween ne yayi rejecting budget ɗin Qaseem, wanda hakan yayi matuƙar fusata shi, tashi yayi wanka ya shiga sannan ya fita domin yaje ya gyara akin da Farween ya ɓata, ba abunda ke mishi ciwo irin yanzu komai ya dawo baya duk kuɗin da ya kashe, saboda haka ya kamata ya biya abunda ya aika ta.


    Office ya nufa kai tsaye, Farween na tsaye gaban motar shi, Qaseem ya fito  daga tashi motar, kallon-kallo suke yi, kafin Farween ya sakar mishi wani miskilin murmushi, harara Qaseem yayi, shi abunda yafi tsana cikin halayen Farween irin wayancewa, he always look innocent kamar baya committing crime, and it really hurt Qaseem, yes Qaseem yana da halin banza amma shi baya munafurci, idan baya sonka zai nuna maka asalin colour ɗin shi.


     Yafi awa biyar a office yana gyara budget ɗin da Farween ya ɓata musu, da ƙyar ya gyara sannan kuma kafin su cimma abunda suke so zasu ɓata shekara ɗaya, gashi kuma shugaban su yana buƙatar abun nan da wata shida, dafe kai yayi deep inside him he’s burning, ko ni kaina sai da Qaseem ya bani tausayi.



Allah dai ya raba mu da maƙiyi. ????


******************’*************


 A ɓangaren Hajna kuwa tunanin Qaseem take yi ba dare ba rana ji take yi kamar ranta zai fita dan son da take mishi, gashi bata ji komai daga ɓangaren Fahna ba, abun yana matuƙar damun ta, ko dai Qaseem ya fasa ne? Da wannan tunanin barci ya ɗauke ta. 


   A ɓangaren Qaseem kuwa Hajna na ranshi dalilin abunda Farween ya mishi ne yasa be samu ya kira Fahna ba, dan yaga miss call ɗin ta. 


   Yana zaune ya tuna da fuskar Hajna kamar ko yaushe sarƙewa yayi, sai da aka bashi kofin ruwa, wayar shi ya ɗauko ya kira Fahna, bugu biyu ta ɗaga, “hello yallaɓai”Fahna ta faɗa tana fari da ido, “ƴar duniya “Qaseem ya faɗa, “ina wuni” ya amsa da“lafiya “, Fahna tace “Hajna ta amince”, murmushi yayi tare da jin wani sanyi a ransa “yanzu ki bani number ta za muyi magana “, “yo ai bata da waya” Fahna ta faɗa Qaseem yace “that’s not a big case, Bari na turo miki kuɗi ki siya mata waya”, “ohk to shikenan “Fahna ta faɗa, ko minti uku ba’a yi ba taji alert ɗin dubu ɗari biyar, waya ta siya mata tsadadda ta zamani iPhone x, mota ta hau zuwa shinkafi, dan Qaseem ya faɗa mata yau yake so ta kai wayar kuma ta nuna mata yadda ake operating, sai da Fahna ta tsaya bakin hanya ta siye Layin waya mtn ta saka mata, da ta isa gida ma sai da tayi charging wayar sannan. 

  Gidan su Hajna ta shiga, Umma ta tarar ƙofar ɗakin ta, “ina wuni Umma”, “lafiya ƙalau, Fahana “umma ta faɗa wanda dama ita Fahana take kiran Fahna, har Fahna ta tashi sai umma tace “yaushe kika dawo ba jiya kika tafi ba”, “eh aunty Kareema ta aiko ni “, nan take Fahna ta ƙaƙalo ƙarya, ba tare da umma ta gamsu ba ta gaɗa kai, ɗakin Hajna ta shiga.. 



Mu haɗu a next chapter dan jin shin ko tsoro zai bar Hajna ta karɓi wayar. 


????????️ *ZAMWA* ????️????

( _Zamfara writters_ )



https://www.facebook.com/Zamfara-Writers-Association-zamwa-110643447448245/


Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya ????????


ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️????????????????


COMMENT plss????????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button