Uncategorized

SAMEEHA K


 *_????SÂMÊÊHÂ????_*

            (K)


Banda gun jin kuka da Sameeha keyi babu sautin komai a fallon,duk ƙoƙarin ta na ƙwace kanta abin yaci tura har Sameer yasa mu abinda yake da buƙata ya mike jikin sa a sanyaye ya faɗa ɗakin sa,yana shiga ɗakin kansa ya sara ga wani nauyi da idanuwan sa suka chanja launi daga fari zuwa jajjaye,banɗaki ya shige ya sakarwa kansa ruwa tun daga kwanyar kansa har zuwa ƴan ya tsunsa daga bisani ya fito ya sanya kaya mara nauyi ya faɗa kan makeken gadonsa bacci me nauyi ya ibeshi.


     A hankali Sameeha ta miƙe a daddafe ta ƙarasa bayi ta gyara muhalinta ta sake fitowa ta shige ɗakin ta,kwanciya tayi a kan gadon ta idanuwan ta gaba ɗaya a lumshe a zahiri kuma a buɗe suke tunanin abubuwa dayawa suka dawo mata ga baccin da yake ƙoƙarin ɗauke ta tsoro da fargabar yinsa ya hana ta sakin jiki soboda tsoron abinda mafarkin ta zai nuna mata a haka har bacci ɓarawo yai awon gaba da ita.



“Tsintar kanta tayi cikin wani sirƙuƙun jeji ba gida gaba babu a baya ga wata narkekiyar baƙar kura data tunkarota a ƙasaice idanuwanta jajir bakin ta a buɗe sai dilalar da wani irin yawu takeyi me yauƙin gaske daga cikin dajin wata kakkausar mirya ta furta””


“”Ki tashi ki shiga duniya, idan kika sake baƙar kuran nan ta damƙe agarar ki ina mai tabbatar miki zaki ɓata ɓat daga doron duniyar da kike ciki ki shilla inda babu wani mahalukin daya isa ya raɓe ki…………..


    chan aka sake cewa


“”Maza tashi ki ambaci Allah bacci ba naki bane Sameeha magauta zasu yi nasara akan ki………Sameeha!!!Smeeha!!!Sameeha ki tashi ki ambaci sunan Allah nasara kar ta kasance akan kiiiiiiii…………………..


Firgigit Sameeha ta farka haɗe da miƙewa cikin hanzari ta fito daga dakin da gudu sukayi kiciɓus da Momy,hannu momy tasa ta funciko Sameeha daga bakin ƙofar ɗakin ta turata jikin kujerar fallon tana mata wani irin kallo daya ƙara rikirkita Sameeha jikinta gaba ɗaya ya ɗauki rawa bakin ta na ƙoƙarin ambaton Allah kamar yanda taji muryar ta umarce ta dashi sam ta kasa furta ko kalma ɗaya banda rawa da bakin yakeyi babu abinda takeyi momy kuma sai binta take da wani mugun kallo wanda tabarwa kanta sanin dalili yin sa,baki momy ta buɗe ta ce”


“Ina Sameer?


Sameeha tayi shiru ta rasa me ma zata furta tsabar rikicewa chan ta saki kuka me ƙarfi da yayi sanadiyar farkawar Sameer daga bacci ya miƙe da sauri ya fito daga nashi ɗakin yan murza ido,kayan jikinsa momy tabi da kallo ta sake duban Sameeha dake durƙushe tana kuka ta ce”””


Son ba dai bacci kakeyi yarinyar nan ta tasoka ba,juyawa tayi ta dubi Sameeha,”Na faɗa miki ki dena kukan nan ki fawwalawa Allah komai insha Allahu komai zai wuce baga Sameer ɗin a gida ba kika ce mun ya daɗe da fita.


Me?


Haka matarka ta shaida mun wai ka jima da fita yau ko abincin ta baka saka abaki da zumar ci ba dalilin yin kukan nata kenan haba son meyasa kakeyin haka ne.


Wai momy wace ce wannan ɗin,na faɗa miki ki dena haɗani da ita na tsaneta na tsaneta momy bana son ganin ta wallahi zan iya nakasa ta,ya taku daf da inda Sameeha ke durƙushe ya haɗe hannuwan sa biyun waje ɗaya.


“Dan Allah ki fita a rayuwa ta na tsaneki kin takura mun kin hanani sakat,kizo min a mafarki kizo min a zahiri me kike so dani,momy duk abinda nayiwa wannan abar wallahi kar kuyi mun magana daf nake da ɗaukar mummunan mataki akan ta idan bata dena bibiyar rayuwa ta ba.


Haba son ba dole mace ta bibiyi rayuwar mijin taba.


Ni ba mijinta bane ban santaba momy.


idan ba mijinta bane kai me yasa kake zaune da ita har kuke haɗa inuwa ɗaya da junna.


    Babu wata inuwa danake ciki tare da wannan baƙar kurar……….da sauri Sameeha ta dubi Sameer da har yanzu hannunsa yake nuni da inda take wani hawaye me zafi ya gangaro kan kuncin ta,murmushi momy tayi tace”


Baƙar kura kuma son.



Wallahi momy kullum sai tazo min da suffarta daga baya kuma sai jikin ta ya koma na kura.


ya dawo inda momy take ya durƙusa gwiwarsa a ƙasa ya ce”””


“””pls momy kice mata dan Allah ta barni ta dena bibiyar inda nake.


To ai kai ne kake bibiyar inda take dolle ne sai ka zauna da ita har kuke haɗa innuwa tare.


Nace miki babu wata inuwa da muka haɗa da ita nida ban santa ba sai a cikin mafarki sai yanzu dana ganku ni yanzu zan kwashi kayana na koma ɗakina na da momy dan Allah karki hanani.


Bazan hanaka abinda ranka yake so ba,amma daka rabu da ita gaba ɗaya ka huta muma mun huta my Son.


Ni dai ɗakin zan bari tun yanzu na koma chan da zama,kisa jalolo yazo ya kwasar mun kayana ya maida min chan momy.


bama sai na saka jalolo ba ni da kaina zan farantawa ɗa na rai maza jeka masoyiyar ka na chan tana jiran ka yanzu zan haɗa maka inaka inaka amma naso ka raba igiyar dake tsakaninku da wannan abar son.


Gaba Sameer yayi kamar an janyoshi ya fito daga ɓarin zee ya hango ta saka riga da wando sun bala’in kamata yaji wani farin cikin dai bai taɓa shigar shi ba sai a yau har wani sauri sauri yake yi ya ƙarasa wajan abar ƙaunar tasa????


Ta kowa momy tayi tazo daf da kan Sameeha ta tsaya daga bisani tayi kwafa ta ce””””


“”Yaro man kaza,bai san wuta ba sai ya taka,mu zuba ni dake muga wanda zai ci riba.

ta wuce ɗakin Sameer kai tsaye,har ta ibe kayan Sameeha na durƙushe tana kuka a inda tabar ta har bugeta momy take da gangan idan zata wuce da abu tagama kwashe komai ta fita daga ɓarin.









_*By*_

_*Maman Dr*_

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button