BAKAR INUWA 6
Chapter Six
…………..Ƙoƙarin kauda fuskarta taketa faman yi saboda kar Yah Muhammad ya ga hawayen dake guje-gujen sakko mata akan fuska tun bayan barowarsu gida. Sai dai kuma abinda bata sani ba tuni ya fahimci kuka takeyi, yadai mata shiru ne domin bata damar rage nauyin zuciyarta.
Sai da ya ɗauka titin da zai kaisu har makarantar tasu sannan yay gyaran murya batare da ya kalleta ba. Shiru Hibbah bata motsa ba saboda zurfi da tai a tunani….
“Auta!”
Ya kira sunanta cike da kulawa. Nanma shiru babu alamar ta jisa. Leɓensa yaɗan ciza na ƙasa yana gangarawa gefen titi. Harya kashe motar gaba ɗaya ya juya yana kallonta batasan mi yakeyi ba. Cikin damuwar data bayyana sosai akan fuskarsa ya ce, “Muhibbat!!”.
A firgice ta juyo garesa tana sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya. Sai kuma tai saurin kai hannunta akan fuskarta ta shiga share hawayenta tana ƙaƙalo murmushi. “Lah Yaya banjikaba ALLAH. Ina can wajen kallon hanya har idanuna na hawaye dan ƙauyanci”.
Murmushin da bai niyyar yi baneba ya suɓuce masa. A ransa yanajin ƙaunar ƴar ƙanwar tasu da yaba halinta na manya. Duk da rawan kanta da tsiwa ita ɗin yarinyace data san yakamata. Tana da wasu nagartattun halaye da sai ka nutsu gareta kake iya ganosu. Amma a kallo ɗaya zaka iya dangantata da yarinya mai rawar kai da shirme. Ya ɗanja numfashi yana furzarwa a hankali tare da kafeta da idanunsa irin nata.
“Mi kike tunani Muhibbat!?”.
A yanda yay maganar babu wasa a cikinta ne ya sata ɗago idanunta dake ƙoƙarin tara ƙwalla ta dubesa. Sai kuma tai saurin girgiza kanta tana ƙoƙarin maida kukan dake son ƙwace mata.
“Ba bu komai Yayah”.
Ta faɗa muryarta na rawa.
Sosai ya sake kafeta da idanunsa dake canja kala zuwa ɓacin rai. Sai dai kuma cikin tausasa murya ya ce, “Kin dai san banason ƙarya ko?”.
Kanta ta jinjina masa hawayen da taketa ƙoƙarin makalewa suka gangaro a hankali bisa fuskarta…. “Yaya! Abba ne, miyasa baya sonmu? Musamman ma ni ya tsaneni bayason ganina”.
Takai ƙarshen maganar tata da fashewa da wani irin kuka mai cin rai ga ma’abocin saurare. Idanunsa ya lumshe a hankali tare da cije leɓensa na ƙasa da ƙarfi. Addu’a ya fara karantowa a zuciyarsa domin samun dai-daito daga fushi da fusatar damuwar ƴar uwar tasa. Ya kamo hannunta cikin nashi ya rumtse da ƙarfi.
Kamar jira take ta sake fashewa da wani kukan, fuskarta ta kwantar akan hannayen nasu dake cikin na juna, hawayenta suka shiga gangarowa har akan fatar hannunsa data ɗora kanta a kai. Cikin kuka ta cigaba da faɗin “Yaya miyasa Ummi ta yarda ta auresa? Bayan kuma tasan shi ɗin mugu ne. Miyasa bata haƙura ta zauna damu mu kaɗai ba bayan rasuwar Abbanmu?. Wlhy Yaya banason Abba na tsanes…….”
“Muhibbat!”. Yay saurin katseta da ƴar tsawa.
Ɗago kanta tai tana kalonsa, ganin yanda ya ɗaure fuska ne ya sake sakata fashewa da kukan.
Yaya miyasa bakwaso nace banason Abba bayan shima baya son mu. Kullum shike gusar da farin ciki a kan fuskokinku. Duk randa yazo sashenmu sai Ummi tayi kuka a ɓoye. Sannan fuskarta tana kumbura kamar wadda aka daka Yayanmu”.
A matuƙar razane yake kallonta a yanzun. Dan tabbas tun basukai hakaba suke tambayar Ummi mike samunta a fuska a maban-banta lokaci, amma sai takan ce musu wani ciwo ne yake mata haka akan fuska lokaci-lokaci, amma tana shan magani. Sunsha damunta suje asibiti amma sai taƙi yarda. Sai dai kuma yau gashi ƙaramar ƙanwarsu tazo da wani batu mai girma. Shin kodai da gaske ne da ake cewa duk ƙanƙantar ɗiya mace tafi ɗa namiji lura da maida hankali akan abu…….
“Yayanmu dan ALLAH kasa mubar musu gidansu mu koma can wani gari da zama mu daina ganinsu suma su daina ganinmu.”
Hibbah ta katse masa tunani ta hanyar girgizasa tana kuka da roƙonsa.
“Tanee! kinga nutsu muyi magana. Maza share hawayenki na tambayeki”.
Da sauri ta shiga share hawayenta da handkerchief ɗinsa. Duk da wasu nabin wasu hakan bai hanata faɗin, “Yaya na goge”.
“Auta kin taɓa ganin wani ya daki Ummi ne?”.
Kanta ta girgiza masa.
“To miyasa kikace kamar ana dukanta?”.
“Yaya nidai haka kawai nake ganin kamar shatin yatsu a fuskarta a duk randa fuskan yay kumburi. Sai kuma ranar da Abba ya kwana a sashenmu na taɓa jin kamar tana kuka na fito ɗaukar ruwa dana manta ban ɗauka ba da dare. Tana kuka sosai, ina kumajin muryan Abba yana mata kamar magana cikin faɗansan nan”.
Kallonta kawai yake ko ƙyaftawa babu, acan ƙasan ransa kuma yanama kalamanta fashin baƙi dalla-dalla. Ganin yaƙi cewa komai yasata kai hannunta akan masa ta girgiza shi.
Ajiyar zuciya ya sauke da haɗiye damuwar dake neman kufcewa akan kamilalliyar fuskarsa.
“Yaya baka yarda ba ko?”.
“A’a Auta, taya zan ƙaryataki bayan nasan ke ɗin baki da ƙarya. Kawai dai ina nazari ne akan maganar taki. Amma inaga yanzu ba shine lokacin yinsa ba. Bara na kaiki makaranta karki makara. Idan mun koma gida zamuyi magana. Amma na roƙeki bayan ni karki faɗama kowa zancen nan har cikin su Usman kinji ko”.
“Insha ALLAH Yaya bazan faɗa musu ba. Amma dan ALLAH ka tambayi Ummi kaji ko Abba yake dukanta ne?”.
Ɗan murmushi yayi a ƙasan ransa yana jinjina wautarta. “Karki damu insha ALLAH bazan manta ba.
Koba komai ta ɗanji sanyi a ranta. Dan haka ta ƙarasa share hawayenta nauyin da zuciyarta yay mata yana sauka a hankali.
Tunda ya tada motar suka cigaba da tafiya sai shi ya koma cikin yanayin shiru ɗin. Dan gaba ɗaya tunaninsa da hankalinsa sun koma akan zantukan Hibbah.
Koda suka isa makarantar sai da ya sakata tai addu’a kafin ta fita a motar, ya miƙa mata 1k tare da mata gargaɗin ta dage akan text din da yaji Ammar ya faɗa zatayi. Inba hakaba bazai kaita chaina ɗin da take burin zuwa ƙaro ilimin kimiya da fasaha ba”.
Cike da son cikar burinta ta tabbatar masa insha ALLAH zata dage wajen cinye text ɗin da maki mai yawa. Daga haka ta shiga ɗaga masa hannu har yay reverse yabar wajen. Ƙoƙarin nufar department ɗinsu tayi ranta fal saƙe-saƙe itama. Ta duba department ɗin su Zahidah a ranta tana tunanin suma sunzo tuni, dan suma sunce mata suna da text yau tun 8am.
★★★★
Koda su Hibbah suka fita a class bata nema su Hafsat ba. Dan tanason samun nutsuwar ƙarasa aikinta na jiya. Kai tsaye ɗakin dake ajiye da na’urori mai ƙwaƙwalwa na department ɗin nasu ta nufa. Dan tana ɗaya daga zaƙaƙuran yara mata matasa dake baje kolin basira da ƙwazon da ALLAH ya basu akan ilimin kimiya da fasa.
Ta samu ɗalibai irinta masu naci da ƙulafuci ɗai-ɗai a ɗakin. Bataima kowa magana ba ta zauna a table guda ɗaya
dake daga can lungu tana sauke ajiyar zuciya, tsabar yanda take nacema Computer ɗin wajen saboda daɗin da take mata har security ta ƙirƙira ta saka dan tanada ajiye-ajiye da yawa a ciki. Akwai wani yaro da suke ƴar tsama da shi, shima yanada ƙwazo matuƙa akan fannin, ya taɓa mata manaƙisar lalata mata securitys ɗin data saka domin binciken abinda take ɓoyewa a Computer daba tata ita kaɗai ba. Aiko data tashi ita sai da tai masa ɓarnar daya gwammaci da bai aikata mata ba, dan babbar ma’ajiyarsa ta Computer ɗinsa dake gida taima kutse, tare da aikata ɓarna da har iyayensa sai da suka saka police zuwa har gida domin kamata. Sai dai kasancewar tana da Yah Abubakar hakan bata faruba, sukai ƙoƙarin ganin sun rufe case ɗin.
Flash ta ciro a bag ɗinta tai connecting da Computer ɗin ta shiga abinda ya kawota cike da ƙwarewa da fatan nasara. Kusan mintuna goma sha uku tana abu ɗaya, sai faman sauke ajiyar zuciya take akai-akai. Harma ta fidda rai da nasara sai gashi cikin amincin ALLAH ta kuma dace. Wani lallausan murmushi ta saki da ambaton kalmar “Alhmdllhi” tana rungume Computer ɗin dan farin ciki. Tuno da bata sanarma Yah Abubakar bane ya sata saurin ɗauka wayarta. Batare da tunanin komai ba ta dailing number ɗinsa. Sai dai harta tsinke bai ɗaga ba. Ta tura baki gaba alamar jin haushi tana ƙoƙarin sake kiransa. Nanma ɗin dai babu amsa. Cikin takaici ta ƙara ƙoƙarin sake kira a karo na uku sai ga nashi kiran ya shigo.
Ɗagawa tai da sauri tare da kwaɗa sallama cikin karaɗinta da shagwaɓa. Daga can Yaya Abubakar ya amsa yana faɗin, “Autar Ummi lafiya dai ko? Ina cikin aiki ne fa”.
“Lafiya lau Yaya dama fa wani abu zan sanar maka. Jiya baka dawo da wuri bane har nayi barci, ɗazun kuma na manta ne saboda Abba”.
“Okay to ina jinki”.
“Uhm yauwa Yayana. Kasan wani abu? Jiya muna fitowa a school wasu masu power bike suka kusan turemu, sanadin hakan ma har Hafsat ɗin gidan aunty Kulu ta samu rauni a ƙafarta sai da akai mata gyara a asibiti. To ni kuma tun a jiyan na jefa musu agogon nan nawa, yanzu haka na gano inda suk…….”
Kafin takai ƙarshen maganar tata ma Yaya Abubakar ya miƙe a zabure da ga can yana faɗin, “Masu power bike?!”.
“Yes! Yaya. Kasansu ne?”.
“Kinga auta kina ina? Wannan maganar bata waya bace zanzo yanzu na sameki, karfa ki faɗama kowa bayan ni”.
Kafin ta samu damar cewa wani abu ya yanke wayar.
“Oh Yaya kama tsaya na gama maganata mana zaka wani yanke. To nama fasa faɗa maka sai nan da awa uku”. Tai maganar tana haɗa kayanta da fushi ita a dole taji haushi. Tana ƙoƙarin rataya bag ɗinta a baya kira ya shigo wayar tata. Ganin Zahidah ya sata ɗagawa tana kai wayar kunnenta da nufar ƙofar fita daga wajen.
Tana cikin sauraren Zahidah dake faɗa mata inda take taje ta sameta taga ansha gabanta. Takaici ya sakata janye wayar daga kunnenta ta ɗago domin ganin wane shege ne ya tare mata hanya.
Turus ta ɗanyi tana kallon zaratan mazajen dake a gabanta riƙe da manyan bindugu tamkar wasu mala’ikun ɗaukar rai. Duk da rashin tsoronta sai da taji wani abu mai kama da firgici ya gitta mata. Ta motsa bakinta a hankali idanunta na wani mar-mar.
“Bayin ALLAH lafiya kuwa?”.
Ta tambaya tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.
Ɗaya da ga cikinsu ne ya nuna mata i’d card ɗinsa da faɗin, “Mu jami’an tsaro ne da ga hukumar ƴan sanda ta farin kaya. Munzo nan ne kuma dominki Muhibbat Aliyu Hamza”.
“Wurina kuma? To ni miya haɗani da ku? Wama ya faɗa muku sunana?”.
“Duk zaki sami amsoshinki idan munje office”.
A tsiwace tace, “Hu’um ai wlhy bazan biku ba, barama na kira Yayan…..”
Zare wayar da ɗaya daga cikinsu yayi ne ya saka sauran maganar tata maƙalewa. Ya katse kiran da taima Yaya Abubakar yana kashe wayarma baki ɗaya.
Wani yawu Muhibbat ta haɗiye da ƙyar tana binsu da kallo tare da ɗalibai ƴan uwanta da hankalinsu ya fara kaiwa garesu suka ɗan fara taruwa domin kallon mike faruwa. Mota suka nuna mata. Da farko batai niyyar shigaba. Amma tuna tana dasu Yaya Abubakar aduniya ya sata shanye dukkan wata fargabarta ta shiga motar tana ƙunƙunin amshe mata waya da sukayi.
Dai-dai lokacin da suke shigewa motar suma Zahidah da aka kai mata labarin anga ƴan sanda na neman ƙawarta ta iso wajen. Hankalinta tashe ta shiga ƙwala kiran sunan Hibbah da sam batama jita ba. A firgice ta lalubo wayarta domin san kiran Ummi ta sanar mata ko zata sanarma cikin su Yaya Umar, dan ruɗewar da tayi tasa tama manta da cewar Yaya Ammar shima anan makarantar yake nasa karatun, yana a shekarar ƙarshe ne ta kammalawa..