Uncategorized

SAMEEHA H


Real Maman Dr✍️_*


*_????SÂMÊÊHÂ????*_

              (H)


*”Ruwan* tsafin sarkin hatsabibai ya iba ya watsashi kan Sameeha dake kwance tana nishi da ƙar,yana watsa mata ruwan tayi wani irin miƙa chan kuma jikinta gaba ɗaya ya saki yayi laƙwas suka jiyo takun Sameer na nifo ɓangaran cikin sauri sarkin hatsabibai ya ce””


“Ki saurari zuwan da dawowar” cikin ƙanƙanin lokaci zata jita a inda bata taɓa tunani ba,ta ta yau ta riga da ta ƙare sai kiyi yadda kike so da jaririn amma ki lura da sharaɗin da na gindaya miki ,yana gama faɗin haka ya ɓace daga ɗakin kamar walƙiya,,sameer ya faɗo ɗakin kai tsaye,yana shigowa ya ji wani abu kamar mashi ya soki kansa da sauri ya dafe kan yana ƙoƙarin faɗuwa ya miƙa hannu ya dafe jikin bango cikin hanzari,Momy na tsaye ƙiƙam tana mai da murmushin jin dadi da tunanin an jima kaɗan burin da ta daɗe tana tanadin sa daf yake da cika.

          A matuƙar riki ce momy tayi kan Sameer da ya ɗago da ƙyar ta ce.


“lafiya my son me ke faruwa me ya sameka,ina ka baro zee ɗin”babu komai momy ta ce gatanan zuwa yanzu yanzu.


Aa ka faɗan abinda ke damun ka karkaje ka ɗorawa kanka ciwon da zamuyi jinya biyu gaka ga Sameeha insha Allah zata samu lfy cikin sauƙi ka dena damun kan ka kaji my son…..,duban momy Sameer yayi a furgi ce ya jefa mata tambaya.”


“Momy wace kuma Sameeh??


Ran momy tas ta kwaɓe baki tace.


Na shiga uku sameer lafiya kake kuwa wannan wace iri yar tambaya ce,shin wace wannan a kwance,,momy tayiwa sameer nuni da inda sameeha ke kwance,buɗar bakin sameer sai ciwa yayi.


Ban san taba,ban taɓa ganin taba sai yau dan Allah momy wace nan ɗin kuma ina ne ?……..


*YA HAYYU YA QAYYUM.*


     Duk Sameer ya jefawa momy tambaya,cike da farin ciki momy ta sake cewa,””


“”Sameehar ce yau baka sani ba,matar taka halak malak Sameer meyake damun ka haka kamar ka zauce.


Babu wani zaucewa da nayi ban santa ba ban taɓa ganin taba,yaushe nayi auren da zaki ce wai matata ce,a ina aka ɗaura mana aure,ni wallahi Allah zee nake so na rantse da Allah zan iya mutuwa idan baku auran zee ba momy dan Allah ku bani Zainab ko zuciya ta zata samu salama,hon ɗin mota ce ta karaɗe gidan gaba ɗaya momy tayi saurin fashewa da matsanan cin kuka ta fito daga ɗakin Sameer ya biyo bayanta yana magiya,inda motar ke tsaya momy ta nufa tana zubda hawaye kashirɓan ta ɗora hannayen ta dukka buyi akai tana.


“”Na shiga uku Alhaji Sameer yayi gamo da matarsa duk an jefe mana su cikin bala’i, ina zan saka rai na, *Alhaji bukar me fata* bai jira masu tsaronsa sun buɗe ƙofar motar ba tsabar firgici yafito da sauri yana.


“Lafiya Momy Sameer, me yasa ki hawaye haka,waye ya taɓa minke yaga gatanki a garin nan gaba da baya,Alhaji bukar ya riƙo hannun momy dake kuka kamar ranta zai fice,cikin kukan momy ta dubi Alhaji bukar ta ce”

“Gashi nan zakaji abinda yake furtawa,bata kai ga rufe baki ba Sameer ya kama hannun Alhaji Bukar ya ɗora akan ƙirjin sa,hankalin Alhaji bukar ya tashi nan da nan jin bugun zuciyar Sameer dayayi kamar zai fasa ƙirjin sa ya fito,kuka Sameer ya sakawa Alhaji  bukar yana…….


       “Abba zuciya ta zata fashe,son Zee haɗe yake da gangar jikina Abba ka cewa momy tabani zee ta aura min zee kar sonta ya kasheni Abba kaji yanda zuciya ta take bugawa kunnuwa na da gaɓoɓina jikina gaba ɗaya zee suke kira dan Allah dan Annabi Abba kasa yau a ɗaura aurena da Zee ko zuciya ta zata huta……


“””kaji ko Alhaji tun ɗazu nake fama da Sameer wallahi gaba ɗaya baya cikin hayyacin sa narasa yanda zanyi ga ƴar mutane a kwance ko motsin kirki batayi wannan wani irin abu mukayiwa maƙiya akan Ɗan nawa guda ɗaya tilo zasu ƙare Innalillahi wa inna ilaihirra”un ina ma ina ma ban kai ga ganin wannan ran….   Maza ki furta Astagafirullah,komai dakike gani muƙaddari ne jarabawa ce momy ki dena wannan tunanin,


Alhaji dolle ne nayi tunani kuwa yanzu na soma,zagi da mummunan kalamai sun ishe ne yanzu Allah kaɗai yasan mutanan da zasu zageni akan yaran nan,momy ta sake fashewa da matsanan cin kuka,Alhaji bukar yayi ƙasa da murya ya ya ce…..


       “””Haba ASMA’U,kina son karya min zuciya daga sauka ta Najeria,idan har zaki biya ta mutane to bakiji ko mai ba,Allah yagani kuma ni shaida ne akan yadda kika riƙi Sameer da zuciya ɗaya ko mahaifiyarsa datasha naƙuda da laulayin sa bazata nuna miki komai akan Sameer ba,tun bai san kansa ba kika sa ya sani ki dena kawo wannan maganar aure tsakaninsa da Zainab kamar anyi an gama tunda yana da damar riƙe mata ɗai ɗai har guda huɗu,kar ki kuma zubda hawayen ki a kan wannan ƴar matsalar,ba dai dangi na ne da sauran jama’a ba to ki kwantar da hankalin ki babu wanda zai gayan naji ko ya hanani aikata abinda naga dama bare shi da kansa Sameer ɗin yace ya gani yana so ba takurashi akayi ba….


Haba Alhaji yanzu biye masa zakayi ita matar tasa kayi yaya da ita,cikin zuciyar momy fes abinda ta daɗe tana nema yau gashi cikin ruwan sanyi ta samu da bakin Alhaji bukar ya amsa romon dumukuraɗiyar Zee yau ya hau cikin Family BMF,Alhaji Bukar ya ce su shiga daga cikin gidan magana anan bazata ƙare ba,idan sun nutsu sa ƙarasa tattaunawa gaba ɗaya suka ɗunguma suka shiga ciki……







……Sameeha dake kwance akan gado kamar an zare laka a jikin ta taji ana ce mata,”””Ki tashi da sunan Allah ki karanta Ayyatul kursiyu da ƙarfi Allah zai taimake ki cikin ikon sa da amincewar sa,cikin ikon Allah da ƙarfin zuciya Sameeha ta ambaci sunan Allah ta fara ƙoƙarin karanta Ayyatul kursiyu,kamar da wasa taji jijiyoyin jikinta gaba ɗaya na saki kamar wace aka ɗaure ƙara bolum ɗin muryar tayi tana yi tana ƙoƙarin miƙewa shi kansa gadon datake kai rawa ya somayi yana jijjiga ta kamar zai karye………………








_*Ina miƙa godiya ga masoya da abokan arziki,Allah ya biya ya saka da dubun Alkhairi,na gode sosai godiyar mara iyaka*_






_*By*_

_*Maman Dr*_

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button