Uncategorized

WAYAFI SONTA 1

????WAYAFI SONTA ?????

Written by mmn fareesa

It’s true life story????????

WANNAN LABARIN NA KUDINE…gamai bukata zata biya naira 300  kachal ta karanta ” tahanya mafi sauk’i Zaki siya Zaki tura kudin ta account number 0089110527  suwaiba Hussaini zakirai  access bank…    saikiyi screen shot kituro shaidar kin biya ko kuwa kituro MTN ta wannan number na naira 300″ 08100084251

Gargadi…banyarda wani ko wata yacanzamun wani Abu dg cikin wannan novel”sannan inkinsan Zaki fitarmun da book pls Kar siya”ada nace bazan iya siyar da novel ba Amma yanzun nacanza tsari akan wasu dalilai game da readers…

 

Godiya…. Alhmdllh ALLAH nagodemaka daka bani ikon Fara wannan novel tsira da amincin ALLAH su tabbata g shugabanmu annabi Muhammad da ahlayensa d sahabbansa…

 

K’orafi….gsky banason k’orafi ko dama kaza akayi ko kaza beyiba duk yadda kuka gani hakan yake badaga gareni bane”Abu 2 nacanza sunayen mutanan dake littafin dakuma garuruwa…

 

BISMILLAH IR RAHAMANIR RAHIM….

Free page

 

p1″

 

…..tsatstsaye suke sunjingina da bishiyar mangaro dake gaban gidansu”zainab ta dubi saurayin dke kusada ita Wanda akalla bazai haura shekara 24 ba aduniyar” kyakykyawa ne Masha ALLAH abin sai son barka yahadu bbu laifi”ahankali zainab dabaza wuce16 years ba tace Wai da gske Yaya gobe zaka koma skul?”murmushi yyi yace eh Mana zee tah! lumshe ido tayi sbd tanason yakirata da wannan sunan”banason kina nuna…damuarki akan tafiyata nasha fad’a Miki ninakine ke d’aya kinki ki kwantar da hankalinki sai kishi da kkeyi kina zaton zankula y’anmata askul ko?”

    Ehmana tafad’a tana turo d’an bakinta.”

F uskantarta yyi sosae yasaka idanunsa anata murya can k’asa yace yanzun fad’a mun zakiyi kewata ko kuwa?” Murmushi tayi ta rufe fuskarta alamar kunya ,Wanda hakan nak’ara Masa tsantsar k’aunarta”sarkin kunya Kinga marece yyi sosai kishiga gd ,nima Inna ta aikeni zanshigo cin abincin dare mun Ida maganar Kuma atare zamuci abincin kin yarda?”murmushi tayi ta d’aga Kai alamar eh.

    Yace to kishiga gd Ina kallonki kafin inwuce nima…kafin tayi mgn goggo haule kishiyar mamanta tazo zata wuce dg shi har zainab Saida sukaji faduwar gaba” wani mugun kallo take watsa musu kafin t amsa gaisuwar dasuke Mata ta shige cikin gd”UMAR yagirgiza Kai ,yanunawa zainab tashiga  gd.kafin shima yashiga gdnsu dake kusada gdnsu zainab din da katanga yaraba kasancewar d baban zainab da baban Umar yayane d k’ane…Cikin gdnsu yashiga yasami Inna mahaifiyarsa ,tana kwashin tuwo”na dare yyimata sannu da gd kafin yasanar Mata aikensa datayi karbo kud’i yace Mai adashen Bata nan”tagumi tayi tace dama Wai Dan insamu abinda zaka k’ara kayi siyayya tunda gobe zaka koma makaranta ” murmushi yyi na tausayin mahaifiyar tasa sbd yadda take fad’i tashi akan karatunsa yace karki damu Inna insha ALLAH za’asami mafita “to shikenan ALLAH ya shige Mana gaba”yace ameen kafin yadauki buta yanufi bayi dan Kama ruwa yyi alwallah…Inna tabi d’annata da kallon tausayi tana girgiza Kai”tasan halin mlm (mijinta) dason abin duniya da kwadayi bazai iya bashi komaiba inkuma wani Abu yasamu to dashi acikin masu cii… sallamar mlm din ce ta katse Mata tunani”ta amsa tana Masa sannu da zuwa”ya wuce dakinsa”Umar yyi alwallah byn sungaisa da mahaifinsa yasanar Masa gobe zaikoma skul…Mlm yace uhumm to ALLAH ya kaimu yabada sa’a Amma gsky ni bazan baka komaiba sbd kasan halin rashin da muke ciki”uwarku itace da kilbibin saikunyi karatu da baffanka”yo Ni inza’abi nawa miza’aibda Boko ‘bokon banza…. murmushi Umar yyi yace Abba za’atada Sallah! bejira cewarsa ba yafice Yana mamakin halin mahaifinsa…

 

    Zainab kuwa tana shiga gd tasami mamanta har taga girki d sauri ta taimaka Mata suka Raba ” akabawa kowa nasa sbd sunada Dan yawa jama’ar gdn nasu… goggo haule ta fito da buta zata shiga bayi danyin alwallal magrib” tafara sakarwa mama habaici kamar yadda tasana na nuna tsantsar hassada da k’iyayyar mama da yaranta…uffan mama batace ba har abbansu  zainab yashigo dawowarsa dg kasuwa kenan…mama ta amshi kayan hannunsa tana Masa sannu da zuwa kasancewar girkintane…goggo haule ta ja tsaki had’e da cewa aikin banxa kisisina ankoyama y’a iyayi d abariki…uffan bbu Wanda yace Sarai baba yajita….Bayan angama isha’i” Umar yanufi gdnsu zainab “sanye yake da jallabiya Fara”kannan nasa sai sheki yake yasha gyara Umar kyakykyawa ne ,Inka kallesa bazakace talaka bane kodan talaka yanada wadatar zuci…can ciki yyi sallama bynsun gaisa d Abba dake soro”khalifa ne atskar gdn ya amsa “yyinda zainab ke zaune kan tabarma d xunbulelen hijab nata har k’asa suna had’a ido yasakar Mata tattausan murmushi,tayi saurin sunkuyadda Kai…mama ce t fito da kular abinci ahannunta fuska sake suka gaisa d Umar ta aje Masa kular tana kallon zainab tace kije ki kamasa plate d cokali…kafin mama t koma d’aki” goggo haule dake lab’e bakin kofa tana kallonsu ta tabe Baki…byn zainab ta ajiye plate din ta zubamasa “tana d’ago Kai taga ita yake kallo”ahankali tace Bismillah Yaya! Yace to muci Mana kinsan haka nace d’azun ko?” Uhumm nifa naci abinci”zeetah nasan kin fad’a be”Amma kunya kkeji”yanxun inbaki Fara sakin jikinki daniba sai yaushe zaki Fara?” nafiso musaba cin abinci tare tun yanxun harmuyi aure ko”? Murmushi tayi ta rufe fuskarta,yyi dariya kafin yafara cin abincinsa suna fira jefi jefi har ya idar”yadubeta matata wane labari Zaki bani?” Ahankali tace bbu lbri” muga wayarka” ok tuhuma za’amun to gata ai da gsky ta… yafad’a Yana murmushi had’e da mik’o Mata wayarsa spak2 wacce pic din zainab din ne ascreem din wayar,sunanta ne password d’in wayar… hannu ta mik’a Dan karba yahad’a da hannunta da wayar ya rik’e” murya can k’asa yace saikin had’a ido Dani kince mun ILOVE U tukum nacikaki ….zaro Ido tayi cike da tsoro Dan tasan k’ila goggo haule na lab’e na kallonsu kada ta musu wata fassarar…. y’ar k’ara tasaki tace wayyo Yaya cinnaka yacijeni da sauri ya cikata,Yana cewa Ina Gurin da cijetan duk yarude sbd beson abinda ka tab’ata…adede nan goggo haule ta fito da niyar ta kulla musu wani sharrin to Kuma sai taga yasakar Mata hannun…taja tsaki had’e da hararar su ta koam d’aki…. zainab tayi Masa gwalo had’e da cewa nifa bbu wani cinnaka dama danka cikamun hannu nasan goggo na lek’enmu kada ta Mana wata fassarar…ajiyar zuciya yyi yace hakane zeetah kinyi kyan Kai kinji ,bazan koma tab’a Miki hannuba…

 

Latse latse taitayi da Yan dube dube awayar bataga komai…ta dubesa taga yahade Rai”cikin shagwaba tace fushin me kake Yaya?” hararar ta yyi yace zeetah Mesa bakida yadda kishinki yyi yawa kinki ki yadda Dani WHY?”nifa bahaka bane yaya!kasan matan jami’a bbu tarbiyya amma aikasan na yarda dakai ko?” hmmm yanzun kingama binkicen kiban wayar”mak’e kafada tayi had’e da cewa um um aguna zata kwana” tashi tsaye yyi yace to shikenan duk abinda kkso shinake so “nasan kina zaton ko wata zata kirane ko?” Inma ansamu nasanki Baki iya fushiba kimata tas! yafad’a Yana dariya har fararen hakoransa suka bayyana….turo Baki tayi had’e da cewa to Kuma inaso kafin inkwanta muyi waya naji muryarka” cikin jin dad’in kalamanta yace zankira ki da wayar Inna ” ok tace ..kafin yafito da biscuits da cheewingum da chocolate yabata (Yana yawan Mata irin wannan kyautar sbd tanada yawan son zak’i) godiya ta Masa cikeda jin dad’i…kafin sukayi sallama yafita…asoro yasami abban zainab yanjin labarai aredio…Baffa Saida safe “Umar yafad’a cikeda girmamawa”yauwa Umar zo muyi mgn” rissinawa yyi kansa ak’asa “yanajiran jin me kanin mahaifinsa zaice.. hannu Abba yasa a aljihu yafito da kud’i 10K yace gashi kaje kayi siyayya ,d’azun rakiya kesanarmun gobe zaka koma makaranta(maman zainab) kayi maneji bbu yawa ai Abu ma yazo karshe tunda baifi wata 4 kagamaba sai bautar k’asa ko?” Amsa Umar yyi da hannu 2 Yana murmushi had’e da zubawa baffan nasa godiya da sanarmasa eh saura 3 month yagama sai service….kafin suyi sallama ransa fall farinciki…

 

   

      Ajiyar zuciya Abba yyi byn Umar yafita” shidai Yana k’aunar yaron sbd kyawawan halayensa gashi Yana Masa biyayya tamkar shine yahaifesa, biyayyar dayake Masa ko hamisu d’ansa na (fari) baya Masa ita, shiyasa yafi kowajin dad’in soyayyarsu da zainab yasan zai kula Masa da tilon y’arsa mace guda aduniya duka yaransa mazane itace mace….

 

Asalin su…Asalinsu sun fito dg sokoto bayan iyayensu sun rasu suka koma kaduna da Zama isyaku shine babba sai rabiu da kanninsu sule,byn wasu watanni dafara kasuwancinsu ,akaduna  suna fannin aikin gine gine ” har sukasiyi fili suka Gina kafin kowane yyi aure, Banda sule..sbd shi yarone …bbu abinda ke kaisu sokoto sai inwata hidima ta tashi sbd danginsu nacan” ….

 

Mama ( rakiya ) itace matar rabiu mace ce ita maisaukin Kai da hakuri… Iyayenta na nan cikin garin kaduna mahifinta malamine sosai na addini  ….itama zulai(Inna) matar isyaku…hakan yasa suka had’a kansu ,sab’anin mazajensu, isyaku ALLAH yyishi dason abin duniya da hange kansa kawai yasani…yyinda rabiu bashida had’ama ga kyauta ga girmama makotansa… shekaran zulai 2 tahaifi yarta mace ,amam rakiya ,shiru …zulai tasake haihuwar mace bbu Rai ,Amma rakiya shiru Bata haihu ba,dukta damu , yyinda, rabiu bashida damuwa yasan komai dg ALLAH ne” har zulai tayi haihuwa t3 haihuwar Umar Amma rakiya ko batan wata hakan yasa akayita cewa juyace…

 

Akwai wata bazawara haule , kasancewar rabiu yadena gini yakoma kasuwancin siyarda kayan awo akasuwa suka hadu da ita bbu kunya tafad’a Masa tana sonsa ,yace ah ah bashi da ra’ayin mace 2 yanada mata….hakan yasa haule ta fantsama bin malamai Saida aka Bata kwalli tashafa suna had’a ido da rabiu yaji sonta ….cikin fahimta yasanarwa rakiya zai k’ara aure..

     Hankalinta yatashi Amma ta daure Bata nunaba tamasa fatan alkhairi…ahaka akayi aur ko wata haule batayiba tafaa laulayi…taso kawowa rakiya raini rabiu yatakamata birki..Habaici da yada mgn shine aikin haule Wai rakiya juyace…duk abinda takeyi rakiya Bata kulata hidimar gabanta take domin tasan insha ALLAH zata ga k’wanta aduniya…sbd baba mlm mahaifinta yasanar da ita…lokacin da rabiu zai auri haule ,yace kiyita hkr kifauwala wa ALLAH lamirranki insha ALLAH Zaki haihu nayimiki istihara Zaki haihu ALLAH ya nunamun…hakan yakwantar Mata da hankali…

 

Saida haule ta haihu 2 duka maza alokacin Kuma zulai yaranta5 sannan rakiya tasami ciki…murnabgun rabiu ba’a mgn tamkar haihuwar fari za’amasa… Tuni haule ta nuna hassadarta k’arara….haihuwar fari umma tahaifi nmj Ahmed t2 mace zainab sai autanta khalifa Mai sunan mahaifinta…alokacin Kuma haule haihuwar ta8 biyu sun mutu…hamisu ,tanimu,Musa, isah, Usman ,Aliyu..tun zainab na karama suka shaku da Umar sosai yake rainonta da kulada ita harzuwa girma abin yakoma soyayya…. goggo haule duk cikin Yayan mama tafi tsanar zainab sbd ita kad’ai ce mace abbansu yanaji da ita sosai ko gabanwa nunawa yakeyi sannan gata da kokari askul d islamiya… zainab nada farin jini had’e da kwarjini,tun tana y’ar 14 years maza ke nuna suna sonta saidai ita tafison yah Umar nata maiyimata son dabayawa kansa ,dukda masu son nata akwai masu kud’i sosai….tun lokacin data Kai SS3 alokacin 16 years gareta …inhar tafita bbu nik’ab sai ansami Wanda yabiyota yace yanasonta “hakan yad’agawa yah Umar hankali…zainab kyakykyawa ce Amma ba irin mugun kyau din nàn ba saidai akwai sura hakan yasa Bata cika saka gyaleba”wankan tarwad’ace itaba doguwa b Kuma gajeriyaba,daidai daidai take sannan Bata jiki sosai saidai akwai k’ugu d gashi…Koda iyayensu suka lura maza nata sintiri kanta sai aka aje mgn da yah uwar ya Ida karatunsa yyi service za’amusu aure alokacin ita Kuma ta Ida SSCE dinta Dan befi 4 month tayi candy ba…yah Umar shima hand some guy ne Masha ALLAH gsky ta yanada kyau..farine dogo Amma ba k’al din nanba….yanada kokari sosai a skul nasu gifted ne……

 

Wannan kenan….

 

Bayan yah Umar yagama abinda yakeyi ya karb’i wayar Inna bacin yamata karyar bayada caji zai Kira a skul nasune….tayi calling din number insa dake wayar innah…

 

 

Share….

 

BY MMN FAREESA????️

[9/7, 5:39 PM] Mmn fareesa: ????????????????????????????????????????

 

 

 

????WAYAFI SONTA ?????

 

 

????????????????????????????????????????

 

 

 

Written by mmn fareesa

 

 

It’s true life story????????

 

 

WANNAN LABARIN NA KUDINE…gamai bukata zata biya naira 300  kachal ta karanta ” tahanya mafi sauk’i Zaki siya Zaki tura kudin ta account number 0089110527  suwaiba Hussaini zakirai  access bank…    saikiyi screen shot kituro shaidar kin biya ko kuwa kituro MTN ta wannan number na  

  Naira 300 08100084251

 

 Domin karanta books namu

 

Y’AR SADAKA book2 na mmn sultan dakuka Dade Kuna nema danjin yazata kasance …naira 300 ne gamai bukata yatura kud’in t wannan account 0089110527

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button