UBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK 43

 ************

Washe gari latti ta farka daga bacci 

Ta motsa ahankali tana bude idanuwanta gabaki daya tana duba kan makeken gadon data ganta ita kadai bayanan, ta tashi zaune tana gyara daurin towel din data 

kwana dashi tana miqewa tsaye tana kallon kofar toilet saidai Jin Babu motsi ta tabbatarda baya cikin dakin ta nufi toilet tayo alwala tazo tayi sallah tana 

idarwa ta miqe ta koma ta kwanta sai lokacin tafara tunanin maganar kisar da akece mum dinsu afia tayi 

Ta tashi zaune tana shiga sabuwar damuwar tausayin afia da farhat musamman afia da sai yanzu take tunanin halin datake ciki,

Yaya zata iya daukan wannan mummunan al’amarin sbd tasan yanda Afia takejin mahaifiyarta cikin ranta wannan al’amari abune me tsananin wahala da azabar 

dauka Dan Haka afia na tsananin buqatanta akusa da ita gaskia.

Tashi takuma Yi tareda saukowa kan gadon ta janyo kayanta na jiya ta maida jikinta tareda fitowa Palon tana gyara rufar kanta da qaramin gyalen datazo dashi 

daure akai 

Babu kowa palon da Alama dai fita yayi gaba daya Dan Haka Kai tsaye ta nufi kofa ta fice kofa kofa ta palukansa harta Kai kofar ficewa gabaki daya ta fito 

Dayake safiyace sosai Sosai Babu mutane tsit koina sai securities din maleek dake koina tafiya daya biyu saika gansu bayi ma na can kowa na aikin gyara da 

aikin abincin uwayen dakunansu kafin su tashi tasamu ta ‘dan rufe fuskarta tana Dan sauri sauri harta Isa sashen Babu Wanda ya ganta tana shiga ta zare 

rufarta tareda nufar ciki Kai tsaye daga Palo bedroom din afian ta wuce ta shiga hankalinta na tashi dajin shiru a palon.

Zaune take kan dadduma tunda tagama sallah Bata tashi daga gurinba  idanuwanta sun kumbura sosai sai fuskarta datai jajir ta dago ta kalli NURUn da duk 

hankalinta yasake tashi ganin yanayin afian take idanuwanta suka ciko da hawaye ta qaraso da sauri ta rungumeta da tsananin sanyin murya da kulawa tace”

Sorry baby.

Sai yanzu afia tasamu me lallasarta tunda wannan baqin labari ya sameta ta zube jikin NURUn tana sake sabon hawaye tana son magana tana kasawa sbd nauyin 

Baki dana zuciya 

NURU ta girgiza Mata Kai tana tsoyayo hawaye ahankali tace”

Karkice komai kiyi shiru Ina Nan

Gani tareda ke.

Shiru sukai ahaka tsawon lokaci NURU na shafa bayanta ahankali ahankali tana Dan lallashinta tareda tunatarda ita tana tareda ita komai zaizo da sauki 

inshallah har afia din tasamu Dan sauki tanata sauke ajiyar zuciya akai akai.

Miqar da ita NURU tayi suka nufi gado ta zaunar da ita tareda Dora Mata kafafunta kan gadon ta ja bargo ta Dan rufe Mata Rabin jikinta ta kalleta da nata 

idanuwan dasuka sauya cikin kulawa da sanyi tace”

Bari nasa akawo Miki wani Abu kici 

Jikinki ba qwari.

Fita tayi zuwa Palo takira masu aikin sashen tace akawo abinci Mara nauyi sosai da tea me zafi Sosai na lemun tsami da Zuma.

Da sauri cikin tsananin girmamawa suka amsa da to suka juya da sauri Dan ciko umarninta ita Kuma ta juya Takoma dakin taqaraso ta zauna gefen afia tana 

shiga nazari da tunanin asalin abin dayake faruwa kokuma yafaru sbd haryanzu takasa sanin takamaimai abindaya faru zancen guntu guntu kawai ta samunsa 

Ta kalli afia ahankali tanason taga Bata cikin halinda zata iya tambayarta wani abun a yanzu 

Gashi dad dinsu afian ma batajin zata iya tambayarsa Dan kuwa tambayar maleek kaman rashin girmamawa ne garesa saidai shi ya tambayeka Dan Haka bazata iya 

tambayarsaba saidai ko jekadi, idan tafita Takoma sashenta zata tambayi jekadi komai inshallah idan harta dawo daga delah daga Kai padima gida.

Da kanta ta bawa afia tea da ‘dan flat filled bread guda daya ta taimaka Mata Takoma ta kwanta cikin kulawa tace”

Kiyi bacci kina buqatan hutawa Kona awa biyu zuwa uku ne ke likitace kinsan kina buqatan hutu kafin kisamu nutsuwar yin wani tunanin ok?

Lumshe ido tayi tana gyada Kai

NURU ta juya tana cewa”

Zankoma Nima nayi wanka naci abinci…..riqe hannunta daya afia tayi tana kallonta da idanuwanta dasuka sauya take suna neman cikowa da hawaye ahankali ta 

bude Baki tace”

Karki barni Ni daya NURU wlh ina buqatan wani atare Dani sbd zuciyata da shedan na ingizani kaman na kashe kaina na huta da wannan rayuwar,

Bana tareda soyayya ta uwata danake tsananin buqata da kwadayin samu Amma bantaba samuba tun Ina qanqanuwata mahaifiyata Bata taba zaunawa tabani soyayyar 

uwaba,

Mahaifina haryanzu Banda masaniyar ko fushin dayake Dani ya sauka Dan haryanzu bansamu ganinsaba bare yasan halindanake ciki,

‘yar uwata ta jini yarinyace qarama da banama fatan taji abindayake faruwa,

Kakanni na mulki da rayuwar mulkice kawai agabansu banida kowa saike Dan Allah ki zauna taredani.

Kallonta NURU keyi cikin yanayi na damuwa da tausayi jikinta nayin sanyi tadawo ta riqo hannun afia din ta tayar da ita zaune tana cewa”

Muje can sashena zakifi samun nutsuwar hutawa farhat ma na can jekadi na kulawa da ita inshallah..

Da sauri afia ta dago ta kalli NURUn bakinta na rawa da mamaki tace”

Jekadi Kuma????

Ganin yanda Afia din ta firgita da Jin jekadi yasa NURUn Dan dakatawa da Mata kallon mamaki tace”

Lafiya dai ko??

Girgiza Kai afia tayi da sauri tace”

Mum da jekadi sune abin yafaru dasu ta Yaya jekadi zata dawo??…

Mummunar faduwa gaban NURU yayi tana yiwa afia kallon tashin hankali jekadi aka kashe kenan ko me???

Innalillahi wainna ilaihirrajiun..

Juyawa tayi tana neman ficewa afia tayi saurin biyota ta riqota tana cewa”

Ta Yaya akai Baki saniba bayan kin kwana a sashenki kinkuma ga bakiga jekadin ba,

Shin tadawo ne?

Gabaki daya NURU kasa amsa tambaya daya tayi sbd toshewar Kai 

Harga Allah jekadi tamkar uwa ko Kaka take agurinta wadda takejinta Kamar jininta sbd a rayuwarta bayan iyayenta jekadi tafara nuna Mata qauna tamkar ta 

jini Dan haka bazata iya daukar zancen mutuwar jekadi Kai tsaye daga sama ba tana buqatan cikakken bayanin abinda yake faruwa ta dago jajayen idanuwanta ta 

kalli afia da itama itan take kallo cikin zaquwar Jin da gaske jekadin tadawo tace”

Kimin bayanin abinda yake faruwa

Acikin duhun komai nake akan al’amarin, shin meya samu jekadin da mum dinki Ni komaima bansaniba

Meyake faruwa”” zuwa lokacin hankalinta yafara mummunan tashi sbd Jin take al’amarin toko yayane ya shafeta sbd yanda rashin nutsuwa da tsoro dayake 

shigarta.

Afia ma sake rikicewar tayi tana kallon NURU zatai magana saita fasa ta koma ta janyo jallabiyarta me hula ta saka ta fito ta fice sbd dad dinta kawai zata 

iya gani yanzu kanta neman kuncewa yakeyi ta tsaya gaban NURU data kasa cewa komai tace”

Muje sashen naki Ina buqatan ganin Mr Omar Dan Allah.

Da ido NURU kawai ke binta sbd ita idan tashiga shock kasa komai takeyi Kamar Mara tunani Haka takama hanya suka Isa sashenta tun a palon ta tsaya tana 

kallon sauran masu aikinta dake tsatsaye suna jiran isowarta tun jiya Bata isoba gari na wayewa sukai ayyukansu suka Gama suka sake dasa jiran isowartata 

Ko gaisuwarsu Bata samu amsawa Kai tsaye ta kalli Akira wadda take matsayin babbarsu idan Jekadi Bata Nan tace”

Akira menene yafaru akan matsalar mum dinsu afia??

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button