NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

UBAYD MALEEK
(Royalty versus love)
Mamuhgee

Bismillahir-rahmanirraheem

1
Qoqarin sauke kayan dake kan jakinsa yakeyi fuskarsa cikeda annuri da farin cikin jikinsa ma na nuna hakan sbd yanda yake sauke kayan da kuzarinsa da dukkanin himmarsa.,
Fitowa bayi matarsa Kuma uwar yayansa tayi tana kallonsa cikin tsananin mamakin ganinsa adaidai wannan lokacin,
Kallon sama tayi tana son kwatanta lokaci idan ta kwatanta daidai zata Kira lokacin da guraren uku zuwa hudu na yamma,
Duban uban kayan daya shigo dasu da jakin tayi tana sake bayyanarda mamakinta a fili na ganinsa Rana tsaka batareda lokacin zuwansa ganinsu yayi sbd a qaidancen aikinsa sai bayan sati bibbiyu yake zuwa ganinsu yayi kwana daya ya juya sai Kuma bayan satin biyu,
Yau kwanansa shida da komawa Amma gashi tana ganinsa harda kaya haka,
inda yake ta fito tsakar gidan tana ajiye butar hannunta tana Dan sake fuska kadan ta qarado tana karban qaton akwatin qarfensa dayake qoqarin saukewa daga kan jakin tana Dan nishin nauyin akwatin tace”

Abal Kaine yanxu?

Kallon kayan data sauke tayi tana maido kallonta kansa tace”

wannan dukannin kayan fa??
Fatan dai lafiya?

Yana qarasa aje daurin karshe dake kan jakin ya jasa zuwa wata rumfar dake can nesa da dakunansu wadda sukai daure dabbobinsu lokacinda suka taba kiwo yakaisa ya dauresa yadawo Yana zama kan saqin data shimfida Masa Yana cewa”

Alhmdlh ya ubangiji.

Ruwa taje tadebo Masa a qaton kofi me nauyi takawo gabansa ta ajiye tana zama gefensa cikin sauke ajiyar zuciya tana sake gaishesa wannan karon cikin yarensu na amheric tace”

Dehina metahi
(Barka da dawowa)

Shan ruwan yayi sosai Yana jinjina mata Kai Yana cewa”

Yawwa barkanku da gida,
Nasameku lafiya?

Alhmdlh”tace tana sake Masa kallon tambaya sbd gabaki daya hankalinta baa kwance yakeba da ganinsa gida yanxu sbd tafi kowa sanin tsanin qarfi da ikon masarautar delah take dashi akan ma’aikatansu Dan shekarunta ashirin harda yan Kai batareda mijinta ba saidai yazo yaganta duk bayan sati biyu yakoma saidai idan tace takai Masa ziyara wadda kafin tagansa ma aikine saiyanzu da shekaru sukaje saidai yayansu suje sugansa duk bayan kwana biyu saigashi yanzu tana ganinsa kwatsam haka ba tsammani.

Sauke numfashi tayi ahankali zatai mgn ya rigata da kallonta cikin tattara Yar nutsuwa a fuskarsa ta dattijantaka yace”

Jamila nasan hankalinki ba’akwance yakeba da ganina adaidai wannan lokacin,
Ki kwantar da hankalinki lafiyace tasanyani dawowa,
Babu wani abu daya faru kamar yanda kike tunani,
Nadawone gida wannan karon gabaki daya da yardar Allah shikenan zansamu yancina zanyi rayuwa taredaku cikin iyalina,cikin nutsuwa.

Wani guntun numfashi ta sauke wannan karon dukkanin jikinta nayin sanyi dajin abinda yake fada Wanda tasan ba iyakacin maganar kenanba akwai babbar maganar dake gaban wannan daya fara ta dago murya a sanyaye tana kallonsa tace”

NEGES?

‘Dan dauke kai yayi ahankali cikin ‘Dan jin nauyinta ya jinjina Kai ahankali yace”

Eh negestati.

Sama numfashinta yayi cikin wani irin yanayi na tsoro da muguwar bugawar da zuciyarta tayi ta sunkuyar dakai idanuwanta suka fara qoqarin cikowa da hawaye
Ya kalleta Kai tsaye yace”

Mahaifina yayi bauta a delah tun yanada kuruciya har tsufa ya kamasa Saida yakai baya iya wata bautar Ni yabayar ya yanci kansa a bautar dela,
Nayi bauta a delah tun Ina qaramin saurayina harna zama cikakken saurayi harna aureki muka Tara yaran dake gabanmu,
Nayi shekaru sama da talatin Ina bauta a delah,
Kinyi shekaru kusan ashirin ko fiye kina zaman kadaici batareda mijikinba,
Yarana sun taso Basu zauna da mahaifinsuba suka samu dukkanin kulawarsa,
Shin kina ganin bai kamata ba Nima nasamu yanci nadawo gidaba na huta ‘daya daga cikin yayana ta fanshi ‘yancina?
Jamila kinfi kowa sanin daganan har lokacinda Rai zaiyi halinsa ba barin delah zanyiba matuqar ba Wanda zan bayar maimakon yancina
Da inada ‘da namiji bautar da mahaifina yayi haryabar duniya Nima nayi Shima ita zaiyi da haka zuriarmu zataita tafiya fa Amma yanzu daga kaina inshallah wannan gadon bautar yaqare sbd nine me ‘yaya mata su ba bauta zasuje yiba NEGESTATI zasu zama.

Rintse idanuwanta tayi ahankali tana maida hawayenta sbd kada yaga rashin hakurinta ko rashin hankalinta ta dago batareda ta kallesaba tace”

Neges?
Acikinsu biyun waccece kazaba data zamo din?

Numfashi tasauke ahankali tana bayyanarda dukkanin damuwarta afili muryarta tayi tsananin sanyi tafara cewa”

Abal, dukkaninsu su ukun nice na haifesu,
Na rainesu,
Na zauna dasu nasan halin kowacce daga cikinsu,
MERIYAM bata cikin lissafi sbd itace qaramarsu gabaki daya shekarunta goma cif,
PADIMA da NURU sune ake magana akai.

Wani tsananin sanyi murya taqara zuciyarta tayi nauyi tanaji tun yanxu dukkanin burikanta da fatanta akan ‘yayanta yana rushewa tareda dukkanin kuzarinta,
Hannu tasa ta dauke hawayen dasukeson sauko mata ta dauke kai ahankali tace”

Dukkaninsu inada burin ganin aurensu Kamar wanne ‘yaya,
Nayi tanada da fatattaki akan rayuwarsu da aurensu,
bantaba kawo wani tunanin inda mahaifinsu yakeba zai iya juya qaddarar daya daga cikinsu daga zama Matar aure kamar kowace ‘ya zuwa neges wato MACEN SARKI KO ‘DAN SARKI KO JIKAN SARKI WADDA IYAKACINTA DASHI KWANCIYA DA HAIHUWANE,
Bantaba tunanin acikin yayana akwai wadda batada rabon igiyoyin aure su rataya akantaba saidai tazama Negestati (Kings mistress/kwarkwarah/abokiyar kwanciyarsa/abokiyar nishadin shimfidarsa).

Kasa riqe hawayenta tayi wannan karon dukkanin jarumtarta saidai tanajin nauyi da kunyar bayyanarda damuwarta akan wannan hukuncin nasa sbd idan tayi Masa adalci ya cancanta ya huta Shima sbd ya bautu,
Ya hidimtu,
Ya wahaltu duk Dan qari sbd su da farin cikinsu baikamata ta nuna damuwarta afili ba duk da tasan aikin gama yariga Yagama tunda harya baro tasan yariga ya karbo shedar musayan yanci.

Abal kayi hakuri.

Girgiza mata Kai yayi Yana gyara zama yace”

Karki bani hakuri Jamila Dan dama dole zakiji ba Dadi saidai duk kuyi hakuri hukuncin Dana yanke kenan,
Maganar rashin jin Dadi anan dayace wato ta rabuwa da ‘danka Amma kinsan irin rayuwar jin dadin da negestati keyi a daular nan banbancinsu da matan sarautar aurene Amma nawane suka sauya kaf zuriar danginsu daga talakawa zuwa attajirai.,
Banda burin ‘yata tashiga delah dan ta maidamu attajirai saidai inada burin samun yancina Nima na huta daga bauta idan arziki yazo takawo Mana bazan qiba sbd kowa nason arziki kowa nason hada jini da delah dan haka Nima bazanqi naso samun jikoki daga delah ba sbd tabbaci ne na har abada da yardar Allah zuriarmu tagama bauta tashiga Kuma cikin littafin tarihin delah.

Murmushin qarfin hali tasaki tana qoqarin miqewa takawo Masa kunun madarar nonon raqumi da sabuwar danyar shinkafarsu tace”

Allah yasa hakan ne mafi alkhairi abal.

Amin” yace Yana gyara zama ganin ta dauko tasar kunun Yana hango haskensa tun daga hannunta.

Aje Masa tayi tafara kwashe kwayan dayazo dasu takai daki tadawo kenan su NURU din na shigowa gidan kowacce sanye da dogayen rigunan asalin yadin kuta,
Padima ce agaba kyakkyawar asalin brown/chocolate kalar fata,
Doguwace tanada jiki kadan musammn kirjinta acike yake Wanda yasa bayyanarda shafewar cikinta.
NURU ce abayanta hannunta riqe dana meryam,
NURU doguwace itama kyakkyawa me yellow brown skin asalin kyakkyawar amhara,
Batai jikin padima ba Amma tafi padima bajewar qugu Wanda yasa tafi padima suturta jikinta da kaya masu Dadi da rashin kamawa sbd boye irin kalar siffar da Allah yayi mata ta Jan hankali,
Tafi padima manyan idanuwa da fuskar marasa hayaniya sbd koyaushe fuskarta is simple sabanin ita padima da daka ganta zakasan tanada rawan Kai da jiji da Kai tareda jin kanta sbd kyawunta datake alfahari dashi duk da dai NURU da meryam sunfitashi haddama hasken fata sbd su kamarsu daya sosai da sosai sbd su mahaifinsu suka dauko shine asalin amhara wato asalin Ethiopian sai ita ta dauko mahaifiyarsu asalin hausa data surka da amhara din.
NURU da meryam kusan halinsu daya na rashin karauniya kuma meryam tafi shaquwa da NURU sbd itace Bata dukanta ko mata fada sabanin padima da Bata daukar raini ko kadan fada take mata musamman akan yanayin yanda takeson gudanar da rayuwarta.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button