Uncategorized

BURIN HAFEEZ Page 31 to 40

A hankali ta murd’a k’ofan falon tashiga ciki, Hafeez tagani tsaye hannunsa d’aya sanye cikin aljihu d’aya kuma yana amsa waya ya juya bayansa, cikin tafiyar sand’a kmr wacce bata da gaskiya Meena ta nufi hanyar d’akinta tana isa bakin k’ofa dai dai nan Hafeez na gama waya.

Wani uban tsawa yadaka mata yace “keee!! Zonan nan” Meena sai da tad’an figirta a hnkli ta juya akalarta izuwa falo, Hafeez ya watsa mata wata uwar harara cike da jin haushinta yace ke gdanku ba manya ne? Kina ganin mutane baxaki gaishesu ba ko ba akoya miki bane? Meena ta turo baki a hnkli tace INA wuni, mtssw Hafeez yayi tsaki yace ” bansani get out wuce kiban waje” Meena ta juya da sauri tashige d’akinta tana gunguni.

A hnkli Hafeeez yace “Mtssw village girl gal kawai”cike dajin haushin ganinta yanufi d’akinsa.

•° •° •° •°

Yau ya kasance weekend Hafeez na nan gda sai wasu aikinsa yakeyi a system insa, zaune yake a falo sanye da farar jallabiya gabad’aya ya maida hnklinsa akan aikinshi.

A bangaran Meena kuwa a kullum bata da wani tunani da yawuce taya zata fara jawo hnklin wannan uban yan girman kan yakarka to izuwa gareta har tasamu tabashi kulawan.

       Cikin tunanin da takeyi ne wata dabara tafad’o mata dasauri ta tashi tanufi falo, dama cikin shirinta take tsaff, cikin natsuwa Meena ke tafiya har ta isa cikin falon Hafeez tagani zaune yanata aiki a hnkli taqarasa gareshi tace “assalamu alaikum” dasauri Hafeez ya d’ago kanshi Dan ganin wacece keyimishi sallama.

      Meena yagani tsaye gabansa sanye da wasu material riga da siket sun matuqar amsar jikinta tayi kyau abunta “koshi Hafeez cikin ransa sai da ya yaba wannan shiga” amma a zahiri sai cewa yayi wa’alaikissalam, nan kuma yatsaya sheqeqe yana kallonta cike da nuna isa yafara kusheta yace ke kuma fa miye hakan zaki zo kitsaya akan mutane?

Dasauri kuwa Meena ta zauna cike da sanyi tace “ina kwana” Hafeez ya amsa ciki ciki yace “lpy” Meena taqara da cewa sannu da aiki Hafeez yad’ago kanshi ya watsa mata wata uwar harara batare da ya amsa mata ba ya maida kanshi sannan yaci gaba da aikinsa, Meena na nan tsugunne Chan tasake cewa “amm kayi brkfst kuwa”? Hafeez yakawo iya wuya wani irin haushi yaji tabasa ina ruwanta da cikinsa, kallonta yakomayi ya watsar da yinta yacigaba da aikinsa.

Meena takawo iya wuya danne zuciyarta kawai takeyi dan haka dasauri ta tashi tabar gurin, d’akin ta takoma cike da jin haushin wannan izza da mulki na Hafeez. 

Hafeez na nan zaune Daniel ya had’o kayan brkfst akan tire yanufi d’akin Meena dashi, yana zuwa yafara kwankwasa k’ofar d’akin a hnkli, da sauri Hafeez yajuyo dan ganin mai k’wank’wasa kofan d’akin Meena, Daniel yagani tsaye hannunsa d’auke da abinci da sauri Hafeez ya taso dai dai lkcin Meena tabud’e kofa.

    Wani irin takaici ne ya turnuqe Hafeez “cikin zuciyarsa yace lallema yarinyan nan yaushe ma tawaye da har zata fara bada umarni ana kawo mata abinci?sannan ma tarasa Wanda zata sa ya kaimata abinci sai Daniel da irin wannan shiga nata” Meena ce ta katse masa tunanin da yakeyi, jiyayi tace sannu Daniel har ka kammala Daniel yace “yes madam” hannu tasa zata amshi abincinta Hafeez yadakawa Daniel tsawa yace “oyaa maida abincin nan kitchn” jiki na rawa Daniel yajuya da abincin ixuwa kitchn kmr yadda boss din nasa ya umarce shi.

Juyawa yayi gurin Meena fuskan nan a turbune ya nuna tada hannu yace “ke yar qauye bari kiji kinyi kad’an kidinga bada order a gdan nan wai dan akaimiki abinci daga yau irin rana tayau bana so in qara ganin Daniel kofar d’akinki danufin wai yakai miki abinci kinajina koh? Kije da kanki kid’ibawa kanki inba haka ba kixauna da yunwa” har Hafeez ya juya xai tafi sai kuma yadawo ya dubi Meena duba na walaqanci yace “ke yar qauye inaso daga yau kezakina shiga kitchn da kanki kidafa abinci, take anan kuma yashiga kiran Daniel! 

Jiki na rawa Daniel yaqaraso yace “yess oga” Hafeez yadubi Daniel yace as 4rm today inaso karka qara bin umarninta nacewa ka kawo mata abinci’ Hafeez yariqe kunnensa yana mainuna alamar warning ga Daniel sannan yace “and then daga ynxu ita zata ke dafa abincinta” Daniel yace okay oga.

Hafeez nafad’in haka yajuya yabar wajan, Meena tsayawa tayi tana binsa da kallo cikin xuciyarta tace “jibeshi da anyi magana yawani cewa mutum d’an kauye qyaatt” juyawa tayi cikin d’akinta tad’auko hijabi tanufi kitchn dan tasamu abinda tasawa cikinta domin kuwa Meena intaji yunwa bata wasa da abinci.

Sumi sumi tanufi kitchn don tad’aura wani abun,…Hafeez na nan zaune ta ratsa ta gefensa tawuce, juyowa yayi yana kallonta tsaki yayi cikin xuciyarsa yace “village gal”

Kitchen Meena tashiga nan tafara laluben abinda zata dafa, tana cikin tsaka da dubawa ne taga hango kwalin indomie da sauri ta janyo kwalin tad’auki indomie biyu nan ta kunna rishow kasancewar bata iya amfani da gas ba.

Take anan Meena tafara dahuwar indomie dinta wnda taji albasa da attaruhu, ae fa nan gda ya kaure da qamshi Hafeez kam mayen indomie take anan yajiyo qamshi na dukan hancinsa wani irin yunwa yaqarajin tashigesa kasancewar dama baiyi brkfst dinsa ba.

®NWA

[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:00PM, 8/3/2016] MUNAYâœðŸ½: 🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿

     âœ¨BURIN HAFEEZ✨

🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.

Episode3⃣2⃣

Dasauri Hafeez yamiqe yanufi kitchen din, dai dai lokacin ne kuma Meena ke qoqarin juye indomie dinta a plat, yawun Hafeez ne yatsinke sai wani had’iyar yawu yake (sbd Hafeez na mutuwar son indomie shiyasa ma kullum gdan baya rabuwa da kwalayen indomie) Cikin natsuwa Meena ta bud’e fridge din dake ajiye cikin kitchen tabud’e tad’auki exotic mai sanyi sannan taduqa tad’auki indomie dinta.

Hafeez bai tsammaci fitowar Meena a lkcin ba jiyayi kawai sunyi karo da juna, dasauri Meena tace “subahanallahi” wani irin takaicine Yakama Hafeez ganin cewa ita kad’ai ta dafawa kanta indomen, duba jikinsa Hafeez yashigayi ko allah zaisa yaga inda ta6ata masa jiki yasauqe haushinsa akanta, amma sai dai anyi Sa’a babu inda jikinsa ya6aci,dan haka dubanta ya shigayi kmr wacce tayi wani abun.

Meena kam tsaye tayi tanabinsa da kallo, Chan Hafeez yaqufula yace “ke yar qauye wannan wacce irin qaxamar dahuwa ce kikayi jibi yadda kikawani zabga tarugu sai kace wata maiyya.

Meena tazaro ido waje tace “nice mayya Kuma?”batare da Hafeez ya kulata ba yace “common get out” Meena taratsa ta gefenshi zata wuce tana gunguni Hafeez yace “magana kike ne?” Meena ta manna masa ta wucewarta, Hafeez yayi tsaki yace qyatt yar qauye kawai sai wani faman big head kike xanyi maganinki very soon. Nan yashiga kwalawa Daniel kira!

   

A bangaran Meena kuwa d’akinta ta wuce kaitsaye dukk haushi ya isheta mgnr Hafeez ce kawai ke mata yawo a kunnenya, kwafa tayi cike dajin haushi tace “tabb wato ni Hafeez zaicewa Maiya? Wlh sai yagane kurensa sai na mai dashi yazama mayen shima in yaso mahad’e muzama mayun mu biyu,..Meena sai faman cin indomien din ta takeyi wnda taji kayan had’i, tanaci tana masifa ita kid’ai a d’aki.

•° •° •° •°

1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button