Uncategorized

MATAR UBA 19

????????????????????????????????        *MATAR UBA*

????????????????????????????????

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*????MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION????????️*

                   *M. W. A*

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

 “`NOT EDITED“` 

 “`CHAPTER 19“`

Murmushi tayi Tace ” Yau Ina break sai gobe” da taimakon Dr Badiyya Asiyah tayi wanka sannan ta d’auko Kaya daka cikin kayan da ta kawo Mata.

????????????????????????????????

…………..Yau kwanaki uku Kenan Hashim kullum yana zaryan zuwa gidan su Asiya,Amma baya samun ganin safiya,hankalin sa kullum a tashe take,har Saida mahaifiyar sa ta kasa gane kansa sashi tayi a gaba akan ya fad’a Mata abinda yake damin sa,ansa d’aya ya ke Bata “Ba komai” Dole ta hakura ba don taso ba.

Nana kullum cikin istigfari da nafilfili take, tana da na sanin abinda da aikata,sannan tayi Allah wadai da qawa irin Baraka sabida itace ummul aba’isin abubuwan da takeyi, sosai Abban Yesmin yaji dad’in ganin yanda ta canza a cikin kwana biyu.

ASIBITI

Dr Badiyya na gani tana tsaye ta hard’e hannun ta tana kallon Asiyah dake bacci tun d’azu,iska ta hura Mai zafi kana tace “Allah ka kawo Mana mafita.”

Hannu tasa a aljihun lab coat dake jikinta ta zaro wayarta wayar Hashim ta Shiga kira, wayan na hannun sa yana ganin kiranta yayi taking ta kashe wayar a fili yace “idan always Kiran da nake jira to na Safiya ne,ban San dalilin da yasa ta ki kirana ba, yau kwanaki uku Kenan Amma shiru.”

Tsaki ya jaa Mai tsawo ya shafo kansa Rai a d’an b’ace yace “Dole naje gidan su,Sam ban yarda da Safiya ba maybe ma sun cutar da ita ne.”

Dr Badiyya Murmushin takaici tayi Tace “Allah sarki Hashim,wannan karon ba abunda kake tunani bane ba,idan bai d’aga call dina ba har gidan su zanje” tana kaina ta fice daga d’akin tana goge hawayen da suka zubo Mata.

Safiya ita kanta tana son Kiran Hashim,Amma taki kiran sane sabida ta jaa Masa Rai Had’i da son cika wata mummunar munufar ta Akan sa.

Hashim tunda ya kashe wayar sa sai da yayi sallar Isha ya kunna wayar,kunna wayar da yayi ke da wuya yaga Kira da private number, hannu na rawa yayi picking, ya Kara a kunnen da ba tare da yace komai ba, Murmushi tayi Mai d’an sauti hadey da fad’in “Malam Hashim ka wuni lafiya?”

Ya amsa da “Lafiya lau” Yana kokarin gano muryar Amma ya kasa ganewa Tace “Baka gane Ni bako?”

“Eh please Wace ce?”

Yar karamar dariya tayi Tace ” Sunana Safiya” tashi yayi ya zauna a d’an razane yace “Safiya kece? Safiya meyasa Zaki min haka? Haka mukayi dake?”

Dariya tayi sosai kana Tace “Duk wa’an Nan tambayar Ni kad’ai ce zan amsa su? To eh nice,nayi hakan be sabida wayata ta samu matsala,sannan ba haka mukayi da Kai ba.” Murmushi yayi yace ” Okay Ina sauraron ki a wane asibiti take?”

” Haba Kai kuwa Babu gaisuwa babu komai sai maganar ta?”

” Am sorry,am sorry ya kike, ya gida?”

” Lafiya Lau ya Jin d’adin ka?” Tana maganar tana karya murya hatda wani fari da Ido yake kamar a gabansa take,ya amsa da “Alhamdulillah”

“Zan fad’a maka inda take Amma da sharad’i”

” Sharad’i Kuma Safiya? Wane irin sharad’i ne haka a wannan lokacin?”

” Sharad’i ne Mai sauki idan ka d’auke shi da zafi Kuma yana da wahala”

” Ina sauraron ki”

” So nake ka turo gidan mu ayi maganar aure”

Murmushi yayi yace ” Safiya Kenan wa yake ta maganar aure bayan Amaryar bata da Lafiya, please be serious Mana”

Rai a b’ace Tace “Ni nace maka amarya bata Nan?”

“Eh man da bakin ki kikace min tana asibiti”

“eh munyi haka” Amma a zuciyar ta Kuma Tace “Aikin banza Ni ban ma San a wane asibiti take ba, ko tana da Rai ko ta mutu oho.”

Maganar da yayi ne ya katse Mata tunanin da takeyi murya na rawa Tace “Me kace?” 

“Cewa nayi a wane asibiti take?”

“Hashim Ina so ka saurare Ni da kyau kaji abinda zan fad’a maka,idan kana so kasan inda Asiyah take to ka tabbatar ka turo iyayen ka gidan mu ayi maganar aure na da kai,idan kayi haka zan fad’a maka inda take,idan ka amince ka Zo gidan mu gobe bayan sallar Isha” tana Kai nan ta katse wayar ba tare da ta ji abinda zai ce ba,Jin ta kashe ya bi wayar da ido yana jinjina hali irin na Safiya.

Shiru yayi har motsi ya kasa yi, chan sai yayi saurin dialing number Faisal, Faisal na picking yace “Toh manyan gari Hala mantuwa kayi ko Kuma kuskure kayi ka kirani?”

“Ba kuskure nayi ba sannan Kuma ba mantuwa bane ba?”

” Tooooh ya akayi lafiya ka kirani?”

” Ji yanda kake magana kamar da bana Kiran ka”

“Kana kirana Mana Amma idan Naga Kiran ka a wannan lokacin bazai wuce  maganar yarinyar Nan bane Asiyah,when last ka Kiran?”

” Look Mr man, kana ina ne? Ina so muyi magana”

” Nasan za’a Zo Nan ai,kayi sa’a Ina gida babyna tayi tafiya da wallahi Ni da Kai sai dai gobe”

Bai bashi amsa ba ya katse wayar.

Yana Isa gidan su Faisal Kai tsaye side din sa ya nufa Bai tsaya b’ata lokaci ba ya kwashe komai ya Sanar dashi, “tirkashi,lallai Abokina kana ganin jarrabawa,to Amma Kai me ka yanke?” Faisal ke magana Yana kallon abokin nasa cike da tausaya.

Cikin murya Mai sanyi yace “I don’t know Faisal,I don’t know gani nake kamar sun cutar min da ita, wallahii wallahi idan suka Mata wani abu sai Naga Wanda ya tsaya musu a garin Nan” ya karasa maganar Rai a ‘bace.

Faisal dafe kafad’ar Hashim yayi yace “calm down ina da shawara,me xai Hana ka amince da bukatan ta kaje gidan nasu gobe sannan muyi was hajiya magana kawaii aje gidan nasu,in yaso ko da anyi aure sai ka sake ta”

” Haba Faisal Kai da nazo neman mafita a gun ka Kuma kace na aure ta, gaskiya shawarar Nan ba tayi ba,ka canza wata”

” To Ni gaskiya shine kad’ai shawarab da zan iya baka ka je ka sake tunani a Kai”

Iska ya hura Mai zafi kana yace ” Na amince zanje gidan nasu Duk yanda ake ciki San Sanar da Kai.”

Sallama sukayi ya fice ya shige motar sa ya nufi gida.

ASIBITI

” Dr mutumin Nan yau kwanaki kisan hud’u Kenan Bai tashi ba,ko dai ya mutu ne kake b’oye min”

Yar karamar Murmushi yayi yace ” Yana Raye kawaii dai ya Shiga comma ne.”

Abban Yesmin dafe kansa yayi Yana ambatan sunan Allah “Comma Kuma Dr? Yanzu yaushe zai tashi?”

“Gaskiya I can’t tell Amma zai iya tashi at anytime Haka Kuma akwai wa’anda suke Kai shekara Basu tashi ba”

Abban Yesmin Maida kallon sa yayi ga Nana yace ” kinji Ina ga Dole na tafi na barku anan zan koma Zaria,sai ki rika kula dashi please”

Bata so hakan ba Amma babu yanda ta iya da to kawaii ta amsa.

????????????????????????????????

Pls kuyi comments sannan kuyi sharing

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button