AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 11 to 20

Ta kwana da matukar tunani a wannan daren, Rayuwar ta da Ahmed, distance relationship, hatred tsakanin ta da y’an uwan shi, musamman Khaleel, she don’t really know why, bata kaunar ganin shi, idan akwai Wanda zata nunawa tsana itace mommy wadda ta hanata sakewa a Rayuwar Auren ta, but why him? So take ta nemo Amsar takasa, juyi takeyi cikeda mutuwar jiki, idan tace bata cikin damuwa tayi karya, Ace Auren ta wata cikin na biyu ba kwanciyar hankali, batasan dadin miji ba batasan dadin zaman Aure ba infact ba Abinda ta karu dashi sai girki da gyaran gidan, Wanda anayi ne domin a kuntata mata, basusan ta horu da aiyuka agidan ubanta ba, ba aikin da zai gagare ta, tsoranta daya a rayuwa kar a rabata da mijin ta, domin duk Abinda ke faruwa soyayyar shi bata ragu a zuciyar ta ba, sai ma karuwa da tayi duk wani moment ita da Ahmed idan ta kadaici cikin farin ciki take kasan cewa, idan tana tuno su, tasani duk ranarda ta samu freedom da mijin ta zaman su zai yi d’ad’in gaske. Bata cire tunanin wata rana zatayi farin ciki ba, Wanda tana fatan tayi nasara insha Allahu. Tashi tayi tareda yin sallah ta roki Allah akan ya cire idanun ta akan duk Abinda zai faru da kuma Wanda ya faru a baya, tareda neman juriya da nasara a rayuwar ta ta yanzu da kuma nan gaba. 

Washe gari aka tashi da shagalin biki, Wanda tun da safe jikin ta yagaza dauka daka kalleta kasan tana cikin tsananin damuwa da kadaici, Ahmed ya boyewa ganin ta baki daya, Wanda batada masaniyar baida lafiya ne, Saida khaleel ya kawo mai likita batareda sanin kowa ba. 

Yana tareda d’an uwan shi har safe bai runtsa ba Abu biyu ke damun shi a zuciya, why yayan shi keda mugun hakuri? And wani gefe kuwa kanshi yake tuhuma, why why why? Domin shi karan kanshi da baida karfin zuciya cikin wata biyun nan da ya ga likitan zuciya, he is in big trouble, big mess Wanda yasani shi karan kanshi, he is a fighter domin duk Wanda ke yaki da zuciyar shi shine babban jarumi, Wanda kowa yasan yaki da zuciya Abune mai matukar wahala. 

Dafashi da akayi yasa ya dawo cikin hayyacin shi tareda kallon yayan nashi, daya tashi zaune yana murmurshi kadan, kana ganin shi kasan cikin jinya yake. “All night bakayi bacci ba khaleel, why kuma kasan yau ranar Auren kane dole ka raya wannan daren. “Yaya ya jikin naka? “Alhamdulillah inajin sauki a jikina, ya Naziya kagan ta? how is she? ” Yaya all you worried about is her? Why bayan ita bata damu da neman kaba if tasan Abinda ya dace me zai hana ta nemeka? “Kafada mata banda lafiya? “Nop Yaya. “Kaga batada masaniya, and please Khaleel take care of her, that girl deserve to be happy. “How Yaya bayan kaine zaka kula da ita she needs you more than me, kaine mijin ta. “I know khaleel. Ya Rungumo shi a jikin shi, yace “you have alot of responsibility, mommy, Fauziya and our company, I know you are stronger than me. “Yaya please stop All this you know you’re breaking my heart, Yaya I have something in mind, Wanda bai kamaci in sakashi a zuciya ta ba I hate myself please forgive me. “What is that khaleel, me kakeso I promise to give it to you koda rayuwa tace saboda kaine farin ciki na. Wasu irin hawaye masu zafi suka gangaro a kwayar idanun shi for the first time, yaji he need them, saboda sometimes tears heal some wounds.

“Noo Yaya bana son destiny din da zai zamo musayar rayuwar ka, I don’t want that destiny, but Yaya is really painful, bansan yanda zanfada maka ba and please don’t ask me too much question bazan iya amsaka ba. “Is OK bazan tanbaye ka komai ba, but dole inji dalilin zubar hawayen jarumin kani na, what is that, meye ya taba zuciyar the stone heart Ibrahim khaleel? “Yaya. “No am not asking the new ango but am sure kana kukan farin ciki ne yau zakayi Aure and you will last on bed more than me. Yafada yana daga gira daya, ya tuno da irin question din da yamai ranar da sukayi hira a dakin shi da Naziya. Dafe kanshi kawai yayi tareda sakin yayan nashi, “Hmmm yaja dogon Ajiyar zuciya, “I know kani na sai yafi thirty minutes. Mikewa yayi cikin sauri, am coming Yaya bari inje cikin gida. Yafita fuuu dagashi sai guntun wando yau ko singlet babu a jikin shi yama manta da taron matan dake gidan, burin shi ya ganshi a cikin gidan. 

Dayake kowa na sha’anin gaban shi sannan kuma an Waye ba wani Abu bane don haka no one care, har ya shiga main palo, dai dai taci kukan ta tayi nak har wani zazzabi takeji ta fito jikinta kamar ba ruwa ba Wanda ya damu da ciwon zuciyar ta. Taga shigiwar khaleel fuuu ya wuce dakin shi, bayan shi ta hanga yana shigewa Wanda dole ta bishi taji inda zataga Ahmed domin ta gaza zuciyar ta tayi rauni, ta leka dakin khaleel din yafi sau goma tun jiya dukan su basa ciki, infact ko gyaran datayi bai baci ba. 

Shiga yayi ya kalli gadon cike da wani irin zafi zuciyar shi keyi Wanda bai taba jin irin shi ba, ya fisge zanin gadon ya jefar tareda zubewa kasa yasaki wani irin kuka mai karfi kadan Wanda ba Wanda zai jishi, 

Tayi matukar tsorata da kuma jin mamakin kukan namiji, tun dosowar ta kofar dakin kuma tanada yakinin a cikin dakin khaleel yake fitowa, wake kuka haka? Bude kofar tayi cikin Sauri, ya dago fuskarshi karab cikin idanun ta, tayi matukar girgiza, bata taba kawo zata ganshi yana kuka ba, meye yasa shi kuka haka ? The great mai girman kai, this is serious, kokarin juyawa tayi kawai domin a tunanin ta koma meye ba hurumin ta bane. “Wait. Yafada cikin sanyi tareda mikewa yana share hawayen shi, tsayawa tayi cak har ya iso wurin, hijabin dake jikin ta tarike gefen shi gam tana jiran taji me zaice, saida ya matsa ya tura kofar ya datse, ta zaro idanun ta, “meye na rufeni a dakin ka, bana son rainin wayau ka bude min kofa intafi. Tafada bakin ta na rawa kamar zatayi kuka, “Hmmm, me kike nema? “Mijina. Tafada kai tsaye batareda ta kalli y’an da ma yake ba, “bakida lafiya ne? Saurin dago kanta tayi ta kalle shi akaron farko tun shigowar ta, da gudu ta datse makullin idanun ta, “Auzubillahi. Tayi saurin ja baya, Wanda Abun yayi mugun batamai rai fiyeda tunani, 

Bata taba ganin bear chest din namiji ra’ayil aini ba sai yau ga kirjin nashi da shegen fadi da wata irin suma mai tada tsigar jikin mace, 

Fisgo hijabin ta da yayi cikin zafin rai yasa tafara istigifari tareda bude idanun ta tana mai kallon that’s why I hate you, “you are behaving like baki taba ganin namiji ba kaya ba, kina Abu kamar wata saliha, look karki daukeni jahili ko mara sanin iyakar shi, I know my limit shiyasa kike tsaye agaba na batareda wani Abu yafaru dake ba, ni kikeyiwa a’u’ziya? kamar Kinga shedan. Cikin tsiwa da zafin zuciya tace “meye banbancin ku da shi, kana ratsa mata tsirara bayan kasan haramcin Abun sannan wuce limit! yes you cross All the limit da ka rikemin hijabi now let me go. Tafada cikin karaji, saurin sakin hijabin yayi tareda sai daita kanshi yana shafo sumar kanshi tareda d’an naushin iska. 

“Am sorry, kiyi hakuri am worried ne because my brother is sick tun jiya. Saurin natsuwa tayi tareda sakin jiki tace “Ina yake? Jikin ta na rawa, yana part d’in mu na waj… Ko gama sauraran shi batayi ba ta bude kofar ta fice da sauri, 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button