AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 1 to 10

1⃣&2⃣

 A kwance yake abakin wani tafkeken beach , yana kallon duk matan dake kaida kawowa a wurin cikin fitinannun bikini da kuma lafta laftan sun glasses, wani irin ya mutse fuskar shi yakeyi domin kamar kashi haka yake ganin su, ba Abinda ya dameshi, bayajin mace zata iya burgeshi just like that saboda shigar banza,  

Kallon shi nayi dakyau, gayen ba laifi chocolate ne shi duk da banga idanun shi ba saboda suna boye a cikin sun glass, Amma nasan zasu kasance masu kyau da tsari, lips dinshi kuwa I can clearly see them suna sheki very soft and shinny, he is behaving like jinin sarauta Amma I don’t know yet who is he? Gefen shi system dinshi ne tareda wayoyin shi guda biyu, daya tayi kara ya dauka cikin sauri domin ganin sunan dake jikin screen din wayar, “heartbeat, Hmmm no wonder mata basa burgeshi duk da yawon da sukeyi a gabanshi necked, sai dai me, yanda yake zuba shagwaba tareda maganar da yakeyi yasa mamaki ya cikani domin daga gani bada mace yake magana ba, is he a gay??? 

“Yaya please, wai kai are you really serious you are getting married??,

Banajin maganar dayan side d’in saidai Amsar shi, “of cos yaya dole inzo Auren ka nine fa best friend best brother and ur best partner in life, am coming insha Allahu, but kasan halin momy kuma I don’t want problem shiyasa nake zama na a bangkok, is alright am on my way don’t worry heartbeat, just for you. 

Datse call din yayi ya mike, a lokacin na kalleshi da tsarin jikinshi daba riga sai guntun wando kawai ga six packs dinshi da suka fito gwanin burgewa alamar yana gyming, tareda kulada lafiyar jikinshi sosai, zare sunglass din yayi, na kalle sexy eyes da lashes dinshi kamar na mace zaro zaro, he is really handsome, one look zakiyi mai ki afka soyayyar shi indai zaki kalli wa’innan killer eyes dinshi, gashi ya iya juyasu, kamar wani karuwar namiji, cikin takun kasaita ya zura beautiful sleepers dinshi na maza ya kwashi kayanshi tareda key ya nufi can gefe inda ya parker open jeep dinshi, ya zube su tareda zama yajata a guje yabar wurin,. 

Wani D’an madai daicin gidane a cikin jerin gidajen dake cikin unguwannin dake shahararriyar Unguwar ta 

  Phetchaburi Road, Makkasan,

 Ratchathevi, Bangkok 10400 Thailand. unguwa ce ta wanda ya tada Kafada da Abubuwan duniya, duk da gidan da ya shiga ba wani kato bane amma kana ganin shi kasan ya gaji da haduwa, maid dinshi ne yayi saurin taron shi da gorar ruwa tareda towel, karba kawai yayi ya nufi bathroom, ya dauki Kusan hour guda kafin yafito kamar zai canjo fata, 

Yana fitowa daure da guntun towel ya tsaya Turus tareda zubawa dakin ido yana mamakin ta, tayi mai dai dai tareda kashe shi da idanu, he just hate that character a wurin mace, shi so yake rana daya Allah ya hadashi da mace mai kunya, that is, tagama siyemai zuciya, but this kind of girls dake rayuwa a irin wannan garin wai in the name of study, Ahh he really hate them, karuwai kawai, 

Ganin kallon rainin wayau Dayake watsa mata yasa ta zaburo tareda matsowa cikin rangwada, doguwar riga ce har kasa she cover all her body but akwai gyara a al’ amarin ta, duk da kyakykyawa ce gata a dire, kuma fara tas bai hana kagano idanun ta sun bude,. 

“Hey dear tafada cikin kashe murya, wani irin kallon don’t touch me ya mata tayi saurin daga hannun ta sama tareda cewa “is ok I won’t dear, but please  just once give me chance to prove myself. 

“Dont even try to suffer ur self, nafada miki fauzy am not interested, just back up. ” am ready to follow you I promise zanyi duk y’anda kakeso am ready to change for you, nafada ma dady na kai nakeso zamu koma kano tare dakai please na horu ka soni don Allah, “Look don’t even try, bazan Auri sauran wasu ba  infact am not ready for marriage now shiyasa dana gama school naki komawa gida saboda nasan Abinda zai faru, don haka kifita a rayuwa ta banason naci. Kuka tasa mai tareda  dukawa kasa, “I swear bantaba bari wani yasanni ba kawai romance ne kuma kasan is a normal thing ai, kana ganin saboda kai nakasa komawa gida kullum cikin karya nake musu please  karka tarwatsa min Rayuwa kaine cikon numfashi na, tausayin ta yaji sosai domin ta dade tana wahala a kanshi tun baya kulata har yafara D’an sauraran ta, “Oh come on, kinsan natsani kuka ko, ki shirya am going tomorrow mutafi nija am going for good, if you are ready….. “Of cos dear am ready, tafada tana dariya mai hade da tausayin kanta, goge hawaye tayi tafita cikin sauri domin ganin ta tattara duk Abinda zata bukata. 

“Ahhh yafada tareda dafe kai, this girl is headache I swear, 

Shiryawa yayi cikin guntun wando da black singlet yafito gwanin burgewa  sai tsadadden agogon shi da kuma dankwalelen zoben dake karawa hannun shi tsari da kyau wa’inda baya taba rabuwa dasu, infact ko shopping zaiyi agogo ne first a tsarin shi he just love watches saboda suna karamai tsari da kwarjini, 

 Abincin shi ya zauna yafaraci wa’inda duk ganye ne sai crabs roasted ones, saida ya dauki lokaci kafin ya kammala ya sanya tissue ya goge bakinshi ya mike, duk al’adar Chinese ta gama ratsa shi abincin su harshen su al adunsu, wainda zasuyi matukar wahalar dashi a nija,. 

Saida yayi clearing komai a daren, about visa da sauransu, karfe uku na Asuba jirgin su ya daga wanda zai kasance long journey duk da a jirgine, tafiyace ta Kusan awoyi,  tana zaune a gefen shi ta zuba mai ido sai faman danna system dinshi yakeyi like ba wata halittar dake existing a kusa dashi, 

She don’t bloody care tunda yace su koma nija tasan komai zaizo cikin sauki,  

Saida  ya dauki lokaci kafin ya rufe ya saka headphones ya rufe idanun shi yana farin cikin zaije wurin yayan shi wanda yafi kowa daraja a duniya a wurin shi yana mashi so mai girma yana kaunar shi fiyeda kanshi, 

Duk da su marayu ne ubansu ya mutu tun yana D’an karami, baiyi lacking komai ba, domin baban su gawurtaccen D’an siyasa ne kuma D’an kasuwa wanda yanada share a manyan campanonin dake ciki da wajen kasar mu harma da ketare, subiyu ne kacal wurin mahaifiyar su, yayan shi Ahmed sai shi Ibrahim khalel wanda khalel din  ne yafi amfani dashi, 

Gatan da yake dashi baya faduwa haka kudi ba matsala bane a rayuwar su domin mahaifiyar su itama ba azaune takeba tana aiki da first bank tareda matsayi mai girma, 

Akwai banbancin hali a tareda shi da d’an uwanshi, domin shi mai zuciya ne, shikuma Ahmed yanada sanyin hali da hakuri,  shakuwa ce mai girma da tausayi a tsakanin Y’an Uwan biyu sukan iyawa juna sadaukarwa ta kowacce hanya, tun suna yara balle kuma yanzu, kowa yasan how they love each other, don haka ko ginin su a hade yake basu taba raba gida ba duk da sunfi karfin hakan, katoton gidan mahaifin su suka kara fadadawa tareda buga plat biyu nasu tangama tangama sai na mahaifiyar su wanda a ciki ma akwai part part dinsu, domin bataso suyi mata nisa, mace ce mai tsananin zafi da kuma rashin hakuri gashi bata son sunan talaka bare kuma talauci batason rashin Aji a rayuwar ta don haka kullum burinta ta fantama, bakaramin shiri takeyi a Auren ya’yan taba tunkafin su tashiyi ma, saidai kash ansamu akasi domin Ahmed ya kaucewa tsarin ta ta hanyar dakko Y’ar talaka tulus, wanda bakaramin daga akasha ba kafin ta Amince da zancen Auren bayan dogayen sharuddan data gindaya bayan Amincewar ta. To muje dai zuwa yanzu zamu fara,. 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button