Uncategorized

MIJIN MATACCIYA Page 41 to 50

***Tafiya yake yana hada hanya har yasamu ya cimma lafiyayyen gadonshi wanda yasha shimfidu masu laushi sannan ga pillows nan sama da guda goma manya da kanana kuma kaloli daban daban,

Zama yayi akai sannan ahankali ya zame ya kwanta yana jin jikinsa duk asanyaye, agogon dake ajiye kan bedside drawer dinshi ya kalla nan yaga karfe 11:30 yasan dare yayi amma yazama dole ya kira Khalid acikin daren nan ba sai zuwa gobe ba,yana da bukatar neman shawarar sa da kuma jin ta bakinsa kafin ya zartar da hukuncin da yake ganin shine daidai.

Kiran layin Khalid yasoma yi yana jin zuciyarsa kamar zata fashe dan tsabar nauyin da tayi masa,cikin dan magagin bacci Khalid ya daga wayar,

“Khalid zan saketa….” Shine abinda kunnuwan Khalid suka jiye masa ai bai san lokacin da ya wartsake ba yayi zunbur ya tashi yabar cikin bedroom dinsu gudun kada ya tada Muneerat,a falo ya zauna sannan cikin damuwa yace,

“Khalil what are you saying?…… Me ya faru?”

“Khalid zan saki yarinyar nan kawai inaga hakan zai fi….”

“Wai meya faru? Wani abun tayi maka mai girma har haka?”

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tashi zaune ya dafe kanshi da hannunshi guda daya,

“Babu abinda tayi min kawai dai naga kamar na shiga hakkinta ne kuma na zalunceta domin na kawota gidana na rabata da wanda take so….”

“Itace ta fada maka haka?” Khalid ya bukata,

“Ba ita ta fada minba amma dai kamar alamun hakan sun bayyana atattare da ita….”

“Kaga malam wannan ba hujja bace, bai kamata ka yi haka ba kaifa babban mutum ne Khalil karka manta, yanzu gaba daya idanuwa akanka suke da zarar kayi abinda bai kamata ba za afara yadawa ana yin yamididi da kai…. Ai gara ka ci gaba da zama da ita har zuwa ranar da zata mance da masoyin nata akan ka saketa ka mayar da ita yar karamar bazawara….. Khalil kasan zawarci kuwa? Kasan radadin da iyaye ke ji aduk lokacin da aka sakar musu yaya? To Wallahi duk amincin da ke tsakaninku da mahaifin ta daga ranar da ka sakar masa ‘ya shikenan sai wani kadari na Allah kuma…. Kayi tunani”

Shiru ya dan yi na wani lokaci tabbas yasan abinda Khalid yafada gaskiya ne to amma ya zaiyi da halin damuwar da ya jefata? Idan har ya zama silar rugujewar farin cikinta bazai taba yafewa kansa ba,

“Kayi hakuri ka kwanta ka manta da kowacce irin damuwa ka samu bacci brain dinka ta huta inyaso gobe sai mu karasa magana…..”

“Shikenan Khalid thank you, thank you for always being with me…. Indeed I have no words to thank you…. Sai da safe”

“Don’t mention it Khalil,you are always welcome….”

Katse wayar Khalil yayi sannan cikin karfin hali yasamu yayi addu’ar bacci ya kwanta wai ko Allah zai sa yasamu bacci,duk tunane tunanen da ke zuwar masa cikin rai a daidai wannan lokaci kin yi yayi da haka yasamu bacci yayi gaba dashi.

***

  Sosai sumayya taga alfanun daukar shawarar muhibba da tayi,ita kanta bata taba sanin tana da kwarin gwiwar iya yin haka ba sai yanzu,gaba daya ta fita sabgar mujahid babu ruwanta dashi wani lokacin ma shine zai yita takalarta har yasamu suyi fada,fada kam yanzu tsakaninsu kullum ne babu ranar banza da zata zo ta wuce basuyi wannan fadan nasu na sabo ba,

Sai dai kwana biyun nan yanzu ba sosai yake ganinta ba sakamakon exams da suka fara a makaranta,kullum tana cikin makaranta suna karatu bata dawowa gida da wuri,ranar da suka gama exams kuwa aranar ta tattara ta tafi katsina gidan iyayenta, mujahid duk sai yaji gidan babu dadi musamman ma idan yana son abu to sai dai yasaka yar aiki ko kuma yayi da kansa haka ma aikin nata da take yi wani lokacin mami shi take sawa yanzu yauma shi yayiwa mami guga ya goge mata kayanta duk gugar gashi babu dadi stones everywhere injishi da fada,tun yana daukar abun da wasa har yaga bafa na wasa bane,dan haka yacewa mami wai zaije ya dauko sumayya a katsina,ranar da safe ya shirya yatafi bayan yasha manyan kayansa brown colour din shadda da hularta,baisha wahalar samun gidanba saboda dama ya sanshi suna zuwa tare da mami,har ciki yayi sallama ya shiga sumayya na ta shan bacci a falo tana kan doguwar kujera,kafarta ya buga nan tayi firgigit ta juyo kamar a mafarki taganshi tsaye,

“Tashi mu tafi…..”

Mutsuttsuke idonta tayi tana son gasgata shin dagaske mujahid ne ko kuwa mafarki take yi?

“Nine nan daina wani kallo na”

Dan turo baki tayi ta zuro kafafunta kasa tana harararsa.

***

  Kamar yadda Khalid yafada masa washe gari wasai yatashi zuciyarsa babu wani sauran damuwa ko gurbataccen tunani haka itama murar tashi yau ya danji dama dama shiyasa ma ya shirya yafita office,ita kuma Hanan da damuwa ta wayi gari duk abunda takeyi tana yinsa ne cikin rashin walwala, wai meyasa ya kasa fahimtar ta ne? Meyasa yakasa gane son da take yimasa duk nauyinsa? Ranar dai haka ta wuni babu farin ciki dan adaki ma ta wuni taki fitowa,

Tsawon Kwana biyu basu hadu da Khalil ba gashi ita kuma gaskiya ganin gida ta ke son taje tayi domin zamanta anan bata ga abinda take tsinanawa ba inbanda zaman kashe wando babu abinda take yi. Waya suka yi da anty badi’a nan take fada mata cewa tana son ta dan shiga makarantar koyon abubuwa irinsu hada sabulai,turaren wuta da sauransu koda kuwa irin na online dinnan da akeyi ne shine anty badi’a ta hada ta da wata mata wai ita hajja hasinah kwararriya wurin koyar da mata abubuwa daban daban,kuma wani abun dadi ma kina zaune daga gida zaki koyi abubuwa masu tarin yawa matsawar kin maida hankali. Zunzuruntun kudi ta biya har naira dubu ishirin tayi registration saboda online classes ne nan hajja hasinah ta sakata a cikin group inda aka fara gudanar da lectures,irin tsarin yanda ake koyarwar abun yayi mutukar burgeta domin ana yin komai dalla dalla yanda zaka gane kuma ka fahimta,

Yanzu kam zaman banza ya ragu domin koda yaushe tana rike da wayarta da littafin da ta tanada musamman dan rubuta muhimman abubuwan da aka koyar gudun kada ta manta tunda shi dai WhatsApp baida tabbas,

Ganin yanda take bobboye kanta a daki yanzu bata fitowa falo sosai sannan bata biye Aryan suyi wasa sosai sai Khalil yafara zargin to ko dai dan ya hanata zuwa ganin gidane shine abin yake damunta? May be hakane zuciyarshi ta raya masa saboda duk lokacin da zaiga Aryan yana wasa a falon kasa ko falon sama shi kadai yake gani bai fi ita yaganta sau daya ko sau biyu ba,

Yau garin Abekuta yaje inda matasan yankin suka shirya masa wasan kwallon kafa da kambun girmamawa da zasu bashi kuma bashi yadawo Abuja ba sai misalin 11 harda rabi na dare,acikin daren saida ya je office yayi signing wasu mails da aka aiko masa sannan yanufi gida,wanka yayi ya sha coffee mai zafi sannan ya nufi part din Hanan,yayi mamaki lokacin da yaga haske dal tako ina acikin sashen nata wannan alamu ne dake nuna cewa batayi bacci ba idonta biyu,

Zaune take kan gadonta tana rubuta abubuwan da aka koyar dasu yau wanda bata samu damar rubutawa ba sakamakon baccin rana da tayi kuma koda ta tashi da yamma garden suka shiga ita da Aryan suka je suka shantake acan har magriba,

Knocking yayi wanda yasa Hanan taji tsoro ya shigeta,shiru yaji ba a amsa ba dan haka ya sake bugawa, ahankali ta sauko daga kan gadon cikin sanda sadaf sadaf tazo bakin kofar zata leka, bude kofar yayi nan taga cewa shine, kallon kallo suka tsaya suna yi dan rabon da suga juna face to face tun ranar nan,

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button