MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 61 to 70

Lokacin da Umar Faruk ya je asibitin MEEMA na barci bata tashi baSai Zabba’u wacce ta kwana da ita, tana zaune a kan sallaya tana lazimin safe ya shigo. Suka gaisa

Sannan ya tambaye ta me jiki?

A nan take faɗa masa, “da sauƙi jikin ta ga ta nan ma tana ta barci bata tashi ba.”

Idanuwan sa na a kan kyakykyawar fuskar ta wanda take a rame sosai. Ta sake fayau da ita tayi haske sosai. Ƙure ta da ido kawai yayi yayinda hannayen sa na a ciki aljihu

Ganin ya tsaya ɗin ne sai Zabba’u tace, “baka zauna ba Umaru? Tsayuwar ai sai ya ishe ka.”

Murmushi yayi ba tare da musu ba ya ja kujeran Robber ya zauna a gefen gadon. Hakan ya ba shi damar ci gaba da kallon cuty face ɗin ta yayinda ya juya wa Zabba’u baya

Itama tunda ta ga ya zauna ɗin sai ta mayar da hankalin ta kan lazimin ta

Tsawon mintuna ashirin ya ɗauka a zaune a wajen ko ƙyafta idanun sa ba ya yi a kanta. Tun daga saman kanta da ke ɗauke da hulan sanyi har izuwa ƙafafuwan ta yake bi da kallo, tana sanye da doguwar riga ne baƙa me ɗan sakayau ɗin nauyi, tana da tsantsi rigan kuma bata da kwalliya, sai kuma blanket da ta rufa da shi wanda iyakan sa saman ƙirjin ta

A lokacin ne ta soma motsi alamun ta tashi daga barcin. Tana buɗe idanu kuwa a kansa suka soma sauka. Sai da ta rufe idon ta sake buɗe wa a kan nasa, sai dai ta kasa ɗauke wa daga kallon shi yayinda lokaci ɗaya ta dakata daga motsa jikinta

While Shima kallon ta yake yi ido cikin ido

Sun fi mintuna uku a haka kafin ita ta janye idanun nata ta sake rufe su ruf tana jin gaban ta na matsanancin faɗuwa, bugun da ƙirjin ta yake yi har shi yana iya gani. Sai da ta saka hannu ta janyo blanket ɗin ta rufa da shi har zuwa kanta ta juya kwanciya ta ba shi baya

A nan take ya lumshe idanun sa yana matse bakin sa. Sai kuma ya buɗe a hankali ya sake kai duban sa gare ta. In cool voice ɗin sa yace, “Are you all right? How your body?”

Tana jin sa sai dai ta kasa amsawa illa sake mayar da idanun ta da tayi ta rufe tana jin wani abu na tokare mata maƙoshi sakamakon tunawa da auren sa da tayi

Zabba’u wacce itama ta ji maganar nasa sai ta juyo tana kallon su, sai kuma tace, “ta tashi ne?”

“Eh Baaba.” Ya amsa mata yana tashi kana yace, “zan tafi.”

“To Umaru ka gaishe da su Momyn taka, Allah ya bada Sa’ar aiki, Ubangiji ya dafa maka.”

“Amin.” Ya furta but ya ƙi tafiya. Yana son sake kallon fuskar MEEMA amma ina ta shigar da fuskar nata a cikin blanket

“MEEMA open your face and say goodbye. He greets you without answering.” Cewar Zabba’u wacce ta kula da halin da yake ciki

Sai dai ko kulata ta ƙi yi, tamkar ma ba ta jin su

Dole ya sake yin ma Zabba’un sallama ya fice

Yana fita ta buɗe fuskar ta, ko kaɗan babu wani walwala a tattare da ita ta sauka a kan gadon ta shige Toilet

Itama Zabba’u ganin yanda take shan ƙamshi yasa ta ƙyale ta, sai dai a ranta murmushi tayi da cewa, “ƴar nema, wannan yarinya rigimammiya ce, kya yi kya gama ai”.

              Sai ƙarfe tara su Hajiya suka iso asibitin. Sai dai Uncle Hashim be jima ba ya tafi kasancewar zai je asibitin da aka kwantar da Sajjad ya ga halin da yake ciki daga nan ya wuce Police station, don ya saka an tsare Kawu Ali kuma ya hana a ba da Belin sa. Bare zancen Umar Faruk ya shiga ciki shiyasa su ma ƴan sandan suka riƙe shi gam. Koda ya je har a lokacin be farfaɗo ba domin sukan wuƙan da tayi masa ya shige sa sosai, ko numfashi ba ya yi sai da oxygen

Su Umma duk suna asibitin suna ta kuka but an hana su ganin shi

Kawu Zubairu ne ma ke ta sintiri wajen ganin an saki Kawu Alin amma an hana, shi ke ta shige da fice a asibitin da can station ɗin

Sai da Uncle Hashim ya tabbatar ya kai maganar kotu kafin hankalin sa ya kwanta. Domin so yake yi a hukunta Sajjad a kan abinda ya yiwa MEEMA har da ma iyayen nasa domin gani yake yi da ɗaurin gindin su, daga can kuma a raba auren nasu, da farko shi cewa ma yayi, “auren be ɗauru ba tunda dole yayi mata, babu wani zancen ayi ta jiran saki.”

Sai da Hajiya ta kwantar masa da hankali a kan, “a amsa takardan kawai a bar shi a auren ya yiwu, don bazai yiwu ace duk zaman nan da suka yi da mayar da ita matar sa da yayi ya zama zina ba, aure ba wasa bane tunda har an tabbatar da cewan ya tara jama’a ya aure ta to ya ɗauru.”

Domin a lokacin tuni ƴan sanda sun cafke Mutumin da ya siyar mishi da gidan, ta hannun sa suka ci galabar samo Mutanen da suka zo suka ɗauki MEEMA, tunda da su aka ɗaura auren su kuma sun tabbatar da hakan, har wajen Malamin da ya ɗaura auren sai da aka je, shima ya shiga koman ƴan sanda daga taimako

Yanda Uncle Hashim ya ɗau zancen ba da wasa bane; don shi ya saka a kama duk wanda yake da hannu koda ba shi da laifi. So yayi ma a ba shi su ya kai su barikin sojoji wanda ya tabbatar muddin ya tafi da su wlh sai dai uwayen su su haifi wani, don sai ya ɗanɗana musu azaban da tunda suka fito duniya basu taɓa jin sa ba. Yana jira ne yanzu ma Sajjad ya farfaɗo a shiga kotu ya ji hukuncin Alƙali, idan be masa ba da kansa yayi ninyan ɗaukan mataki zai mayar da maganar ne wajen aikin su, ko tausayin Sajjad ɗin ba ya ji duk da ya ga halin da yake ciki, da za’a bar shi ma a haka ya hukunta shi da tuni ya hukunta shi ɗin.

           Kwana uku MEEMA tayi a asibitin aka sallame ta tunda jikin ta yayi sauƙi, ga shi tana samun kulawa ta ɓangarori da dama na Mutanen gidan su, har Ummee kamar ta goya ta tsaban kulawa, shiyasa komi ba ta ce mata domin itama tana son kulawar uwa, tana kewar mahaifiyar ta shiyasa a ranta take jin kamar ta yafe mata, sai dai takan koka idan ta tuna tun farko ita ce ta ja mata, da bata aikata hakan ba da tuni babu ita a Nigeria. Wani lokacin kuma ta kan ga kamar rashin yarda da ƙaddara ce irin nata, idan ta yarda da ƙaddara baza ta taɓa ɗaurawa mahaifiyar ta laifi ba, komi da ke faruwa a rayuwar ta Allah ne ya ƙaddara, mutuwar Abee ɗin ta da silan dawowar ta Nigeria; hakan ke saka wa take jin sanyi daga tsanar da tayi mata.

               A wajen Umar Faruk kullum yana a asibitin, idan be zo sau uku a rana ba zai zo sau biyu

Yanda yake nuna damuwar sa a kanta sam-sam ita hakan be mata ba, shiyasa ko kallon sa ba tayi bare ta tanka shi. Tun Hajiya da Zabba’u suna mata faɗa har sun gaji sun zira mata idanu

Koda aka sallame ta ma a ranan lokacin yana Office ne. Yana koma wa gida ya ci wanka ya fito da zummar zuwa gidan, har ya fita kuma ya dawo ya saka Luwaira ta shirya su Hafsah domin ya tafi da su

Kasancewar yanzu yana bata kulawa, duk kuma yana ƙoƙarin ya ga ya sauke haƙƙin ta, suna zaune lafiya babu wani abu kuma tunda Umar Faruk Mutum ne me tausayi da son kyautatawa na kusa da shi, ya riƙe Luwaira hannu bibbiyu yana faranta mata duk abin da take so tana samu, sai dai har yanzu ba ya jin ta a zuciyar sa

Ita kuma a ganin ta ya soma ƙaunar ta ne sakamakon shawarwari da Abida take bata wajen ta ga tabi wasu hanyoyi ta mallaki zuciyar sa. Haka kuma tana jan yaran sa a jiki sosai wanda shawaran Abida ne domin a ganin ta hakan zai saka ta sake samun zuciyar sa, tana basu kulawa sosai.

             Koda ta gama shirya su ɗin ɗaukan su yayi ya fice ba tare da ya sanar da ita inda zasu je ba

Itama bata damu da sai ta tambaye shi ba illa adawo lafiya da tayi masu ta shige ɗaki abun ta

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button