TAKUN SAKA 23

*_Typing????_**_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*
*_Chapter Twenty Three_*
………….“Kaga wani salo kamar a film”.
Ammar ya faɗa dariya na kufce masa a bazata. Dan haka kawai wasan yay matuƙar birgesa da ƙayatar da shi.
Su yaya Abubakar kam da gaba ɗaya mamaki da al’ajab ɗin Isma’il ɗin ya daskarar da su a tsaye da ƙyar suka iya fisgo numfarfashinsu sukai azamar zuwa suka sha gabansa ganin Abba ya ke nufa gadan-gadan. Dan su gaba ɗaya abinda zukatansu ke basu lallai Isma’il yana tare da wani bahagon aljani ne ƙila.
Idanunsa ya rumtse da ƙarfi ganin sun tare sa. Cikin wata irin murya mai ƙaraji da saka firgici ga ma’abocin saurare yace, “Minti uku na baku a fitar min da wanann sauran gawar anan. Kar kuma na sake ganin ƙafar waninku anan. Inba hakaba…. Ya ƙyalƙyale da dariyar da ta saka su Yaya Abubakar sake zama turus a gabansa.
Jiki na rawa Momy ta kama ƙafafun Junaid ta fara ja tana kuka. Yayinda tuni Hajiya mama ta fece da gudu har tana cin tuntuɓe zata faɗi. Su kawu Garba da ke gefe a maƙure suma ne sukai karfin halin matsowa suka taya Momy ɗaukar Junaid da zuwa yanzu ya sume sabida azabar murzar da wuyansa yasha da haƙarƙarinsa.
Da gudu Ammar ya taho ya rungume Isma’il ta baya yana dariya da hawaye a lokaci ɗaya. Hakan yasa Ummi ma da tai mutuwar zaune tana kallon Isma’il ɗin ta miƙe zuwa garesu. Hannun Isma’il ta riƙo cikin nata hawaye na sakko mata saman kumatu. Jawo hannun nasa tai ta zaunar da shi akan kujera tare da ɗaukar goran ruwa da ke a saman centre table da aka ajiyema baƙi ta ɓalle murfin ta ɗora masa a baki tana shafa kansa.
Babu musu ya hau sha yana jan ajiyar zuciya. Sai da ya shanye shi tas ta janye goran tana cigaba da shafa kan nasa.
A hankali ya lumshe idanunsa da komawa baya ya jingina jikinsa da kujerar, numfashinsa tun yana sauka da zafi-zafi har ya koma sauka a hankali alamar zuciyarsa nayin sanyi.
Ummi ta share hawayen fuskarta tanayin murmushi da duban su Yaya Usman da har yanzu ruɗani da al’ajabin mamakin Isma’il ɗin ya gaza barinsu. Matsowa sukai gareta. Yaya Umar da yaya Usman suka rungume Isma’il ɗin. Yayinda Ammar yazo ya zauna gabansa ya ɗaura kansa a saman cinyarsa fuskarsa washe da dariya tamkar gonar audiga.
Hannu ya kai a hankali bisa kan Ammar yana shafawa. A karon farko ya saki murmushi da ɗago kansa ya na kallon Ummi da su Yaya Muhammad.
“Kiyu haƙuri Ummi, lamarin mutanen nan sai da over acting. Na fahimci wannan ce kawai mafita a garemu. Inba haka ba sai wata fitinar ta kaure har akai ga jima wani ciwo”.
Yanda yay maganar cikin sanyin murya tamkar yanda suka sanshi ne ya saka su Yaya Usman sakin ajiyar zuciyoyi.
“Amma Isma’il ka bani tsoro matuƙa wlhy, har mun fara tunanin ko baka da lafiya ne”. Cewar Yaya Muhammad yana murmushi.
Ɗagowa Isma’il yayi zaune sosai yana saki ƴar dariya. “Yayanmu lamarin tsohuwar nan ne sai da haka. Sai dai fa nasan wlhy ba haƙura sukai ba, dan da alama na jima wancan wawan yaron Junaid ciwo a haƙarƙari. Ummi inhar shirinku na barin gidan nan na nan to lallai dole ne ki tafi kema a yau ɗin nan. Kamata yay ma ace yanzu kawai. Kinga sai ki tarbi amare da kanki”.
Yaya Abubakar da har yanzu shi dai yake kallon Isma’il ɗin cike da nazari da wasiwasi ya gyaɗa kansa cikin gamsuwa. “Wannan mafita ce mai ƙyau. Dan Abba kam ba kanwar da za’a lasa bace aji kaifi kawai. Ummi kamar yanda Isma’il ɗin ya faɗa barin gidan nan yanzu shine mafita kawai”.
Sosai itama Ummi ta gamsu da zancen. Dan duk abinda zai ɓata mata taron auren yaranta bata fatansa. Sarai kuma ta fahimci abinda su Hajiya mama ke burin yi kenan. Sai dai kuma cikin damuwa da rauni ta ce, “Tanee ɗin fa an ganta?”.
Da sauri Yaya Umar ya gyaɗa mata kai. “Eh karki damu tana tare da ƙawayenta ashe. Zuwa anjima nasan zatabi masu kai su can kawai”.
Duk da zuciyarta a raunane take hakan bai hanata gamsuwa ba. Ta mike tana warware mayafinta da dama tana tare da shi tun ɗazun ta sake yafawa. Dama ba wani muaten bane sosai a sashen. Makwafta da suka shishshigo sukai mata ALLAH sanya alkairi duk sun fita saboda yamma tayi sosai. Sai ƙawayenta na kusa sosai irinsu Hajiya Mardiyya. Suko sunsan da shirin barin gidan. Dan dama sune zasuje amsar amare acan. Jin hukuncin da su Yaya Muhammad ɗin suka yanke ne ya sakasu mimmiƙewa suma suka hau kimtsawa.
Su Ummi basu da matsala da komai na sashen dan sun tsince masu muhimmancin sun killace sauran. Su hajiya mama nacan akan Junaid cike da ruɗani suka samu suka fice dan dama gari ya fara duhun magrib da ake ta faman kira a masallatan anguwar. Mutanen da ke a tsakar gida kuwa gulma da tsugudidin da suka haɗa kai sunayi group-group yasa basu hankaltu da su Ummin ba. A tunaninsu kawai ƴan biki ne zasu wuce gida.
★★★★★
A can L.E street kuwa cike da farin ciki da ƙaunar yaran har cikin rai baba Saude ta mike domin gabatar da sallar la’asar ɗin itama. Tana idarwa ta fito ta hau shirya musu abincinsu na rana da basu ci ba.
Kasancewar yunwar kuwa na ƙwaƙular cikinsu ana idar da sallar la’asar ɗin suka dawo gidan. Sai dai su kaɗai suka shigo falon banda Master da yay zamansa a ƴar runfar bunun da ke a gefen swimming pool ɗin gidan. Dan yasan tunda suka dawo gidan shegen surutinsu ba zai barshi ya huta yanda yake bukata ba.
Suko da ga can cikin zalamar kayan daɗin da baba Sauden ta baje musu a babban dining ɗin suka baje da fara ɗurama cikinsu. Yayinda kowa ya fara kai lauma sai sabon surutu ya ɓalle, baba Saude na gefe na musu dariya kamar yanda ta saba har suka kammala. Sune suka zaɓar mata ɗakin da zata zauna anan downstairs ɗin. Hundred percent kuwa ta gamsu da ɗakin, dan yana ɗan nesa da ɗakunansu ga shi kuma gab da kitchen.
Sune suka shiga gyara mata komai duk da bama wani datti bane da ɗakin. Bayan sun kammala Salis yay list ɗin abubuwan da yasan Baba Sauden zata buƙata na amfani musamman a toilet. Da ga haka suka dawo falo kowa ya kama hidimar gabansa. Lokaci-lokaci suka sakko zancen Zaidu da ke can gidan su Hibbah yana gano duk cakwakiyar da ke faruwa batare da kowa ya fahimci shi ɗin wanene ba.
*_8:16pm_* ya shigo gidan. Lokacin su Idris da dawowarsu da ga sallar isha’i babu jimawa na baje a falo suna kallon ƙwallo. Duk sun cika falon da hayaniyar gaddamarsu.
Khalid da ya fito da ga kitchen riƙe da drik ne ya fara farga da Master da ko sallamarsa basu ji ba. Cikin ɗan daga murya yanda zasu fahimta ya ce, “Barka da dawowa Master”.
A take falon kuwa yay tsit duk suka juyo ga ƙofa. Cikin ɗan hararsu ya ajiye ledojin da ya shigo musu da shi ya haura sama da ɗaya batare da ya amsa sannu da zuwan da suka haɗa baki wajen masa ba. Suna ganin ya gama hayewa har rige-rige tasowa Zaidu da bai jima da dawowa gidan ba suke shi da Salis wajen zuwa su ɗauka ledojin da ya jiye. Suma sauran tasowa sukai akan ledojin cike da farin ciki da ƙaunar Mastern nasu.