SULTAAN 17-18

???? *S U L T A A N*Mss Flower????
*FITATTU HUƊU????*
_RESEMBLANCE OR SIMILARITIES OF STORY/LIFESTYLE SHOULD BE CONSIDERED AS TOTAL COINCIDENCE_
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*
*17-18*
Na miƙe tare da nufarsa, zama na yi a gefensa cikin kasala na ce “ba ka ci abinci ba”, ya ware lumsassun idanunsa a kaina sannan ya ɗan langaɓar da kansa yana lasar lips ɗinsa ya ce “na ƙoshi” tamkar mai raɗa
Sabon daɗi ya kamani na ce “wai yaushe ka fara magana?”
Bai ce uffan ba sai ɗan murmushi da ya yi, sannan ya juya tare da ba ni baya ya kwanta sosai ya rufe idonsa, ganin bai son jan zancen ya sa na tashi tare da tattare kwanukan abincin na rufe masa ƙofa.
Ban kuma saka shi a ido ba duk yadda zuciyata ke son ganinsa, ban san dalili ba amma sosai na damu da lamarinsa har rana ta take kasa wani bacci ni na yi, da na kwanta sai ya faɗo min a rai musamman maganar da ya fara yi a bazata, muryarsa wata iriyar tsadaddiyar murya ce mai cike da daɗin sauraro, idona na lumshe tare da sakin murmushin da ban san dalilinsa ba.
Da yammaci ina zaune a ɗaki ya turo ƙofar ya shigo, da murmushi na tarbe shi tare da cewa “abinci fa ranka ya daɗe”
Ya lumshe idonsa wanda hakan ya zame masa jiki sannan ya gyaɗa min kai, fahimtar abin da yake nufi ya sa na tashi tare da nufar kitchen, gefensa na zauna bayan na yi serving ɗinsa, a tunanina zai ci da kansa ne sai na ga ya tsura min ido, hakan ya sa na ɗauki spoon ɗin na shiga ba sa, ya ɗan ci sosai kafin ya kauda kansa alamun ya ƙoshi, kansa ya ɗora saman kafaɗata ya rufe idanunsa, hannu na saka na kama na shi ina wasa da shi, sai ya cafe hannun nawa ya shiga murzawa, murzawar da ke ɗaga min hankali ta fitar da ni daga hayyacina, hakan ya sa na yi saurin janyewa da na ji yanayina na canzawa na ce “ko mu fita mu ɗan zagaya, akwai wurare masu burgewa a masarautarku”
Ware kyawawan idanunsa ya yi masu ɗauke da ruwa narai-narai ya sauke a kaina, sai kuma ya lumshesu tare da ɗan ɗaga min kai alamun e, ya cire kansa daga kafaɗata, miƙewa na yi na ɗauko masa ƙatuwar sweater fara mai kwalliyar jikin damisa daga ƙasa, wadda ta hau da tufar da ke jikinsa, Ni ma sauyawa na yi cikin doguwar riga da ta kusa kawo min ƙwauri, na rufe kunnuwana da gashina sannan na ɗaure, hannunsa na kama muka fita daga gidan.
Garin ya yi wani irin lufff sai sanyi da iska da ke kaɗawa, tsuntsaye na ta shawaginsu a bishiyun, wata hanya muka bi da ta ƙawatu da flowers sai wani asirtaccen ƙamshin roses take fitarwa, nesa kaɗan ga pond da red, white and pink flowers suka zagaye, wajen na malale da grass carpet, wajen is just way more than amazing, sosai ya haɗu, da murmushi na dubi fuskarsa da ke cike da annuri na ce “let’s stay here!”
Lumshe idonsa ya yi tare da ɗan ɗaga min mai in acceptance, wani stone bench muka samu muka zauna, sai dai shiru don ni duk ya canza min bare na shiga mai hirar da na saba, wani mugun kwarjini yake min, har kasa magana nake, ko in na dage zan yi ɗin na shiga stammering.
Miƙewa na yi na nufi pond ɗin da colorful fishes ke yawo na tsugunna cike da jindaɗina ina wasa da ruwan da hannuna, sai nishaɗi nake yayin da yake zaune hannunsa a ƙirji yana kallona, ana haka na ji muryar Prince Wahid yana min magana.
Miƙewa na yi cike da nishaɗina da nake ciki na dubesa tare da sakar mai murmushi, murmushin shi ma ya saki tare da cewa “having fun?”
Gyaɗa kaina na yi sannan na ce “me ka zo yi nan?”
“Nemanki nake?” Ya ce
Dariya na yi na ce “ya aka yi ka san ina nan?”
Sautin zuciyarsa ya nuna tare da cewa “wannan ce ta shaida min!”
Cikin kunya na sauke kaina ƙasa wanda hakan ya sa gashina da ya ɗan zaro daga tufkar da na mi shi ya rufen gefen fuska, hannu ya sanya ya gyara min tare da cewa “you are so beautiful!”
Giggling na yi tare da cewa “I’m not” cikin dariya
“You are!” Ya faɗa
“I’m not” na ce ina dariya
“Okay! Tsaya mu gani” ya ce yana riƙe haɓata tare da tsurawa fuskata ido, can ya saki ya ce “i believe you, you are more than beautiful”
Dariya na saki sosai wadda ta bayyana haƙorana, yayin da shi kuma ya tsura min ido delighted.
Hannuna ya kama ya ce “let’s sit!”
Wani irin faɗuwa gabana ya yi ko da na waiwaya na ga mugun kallon da yake aiko min, sai kuma ya lumshe idonsa tare da kama lips ɗinsa na ƙasa, Prince Wahid ja na ya yi har inda yake zaune sai dai duk jikina ya yi sanyi, farincikin da nake ciki duk ya disashe dalilin mugun kallon da ya aiko min, jiki ba ƙwari na zauna.
Prince Wahid hannu ya saka ya kwaɗa mai duka a baya yana cewa “Psycho ya jikin naka?”
Buɗe lumsassun idanunsa ya yi ya kallesa, bai ce uffan ba ya kauda kai babu kuma wani yanayinsa da za ka iya karantawa, Prince Wahid ya yi dariya tare da ɗora hannunsa a kansa ya shiga wargaza sumarsa yana cewa “ina son ka samu lafiya ko don na yi hira da kai a matsayin ɗan uwana”
Wani ihu na ji Prince Wahid ya saki da na ɗan sauke idona, ko da na duba sai na ga hannun Prince Wahid cikin hannunsa ya yi mai wata iriyar muguwar matsa, sai ƙoƙarin ƙwacewa yake ya kasa, ganin kamar zai karya mai hannu cikin ruɗewa na ce “ka sake shi mana, meye haka?!”
Ya ɗago dara-daran idanunsa da suka ƙara walwali dalilin ruwan idanunsa da suka kuma cikowa ya tsura min ido, sai kuma ya ɗauke tare da sakinsa calmly, ya kama hanyar tafiyarsa.
Ajiyar zuciya na sauke tare da duban Prince Wahid na riƙe hannunsa ina cewa “sannu, ba ka ji ciwo ba ko?”
“Ahhh! Kamar na goce a nan!” Ya ce cikin wata iriyar murya
Idona na kansa duk da ya yi nisa na dubi Prince Wahid na ce “ko ka je ka ga doctor, ni bari na bi bayansa”
“Washh! Hannuna!” Ya ce cikin azabar ciwo
Na waiwaya na kuma kallonsa zuciyata na son bin sa amma na kasa dalilin kusan kukan da Prince Wahid ke yi, hannun nasa na kama na shiga ɗan matsawa a hankali, lumshe idonsa ya shiga yi tare da ja na muka zauna, sai dai zuciyata a jagule take. Bayan na jima ina masa massaging hannun na tashi da niyyar tafiya, da hanzari ya riƙeni tare da rungumeni a ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya ya ce “please don’t go!”
Shiru na yi ina sauraron yanda zuciyarsa ke fat-fat kafin na ɗago daga jikinsa na kalli fuskarsa, idanunmu suka sarƙe a na juna, na kasa janye idona dalilin kallon da yake aiko min kafin ya ce “Please stay!”
Duk jikina ne ya yi sanyi haka na zauna yana ta labaransa ina dai sauraransa sai dai hankali da nutsuwata duk ba sa jikina, ganin duhu ya fara yi sosai na miƙe na ce “Ni zan tafi, sai da safe”
Ban ma ko tsaya sauraronsa ba na wuce da hanzari kada ya tsaidani. Tamkar babu laka a jikina na tura ƙofar ɗakinsa dan ban tarar da shi a parlor ba, zaune na gansa ya ba wa ƙofa baya, ko da na ƙarasa inda yake duk a ɗan tsorace, idona ya sauka kan hannunsa da ke ɗigar jini, a ruɗe na kama hannun duk na gigice ina cewa “me ya sameka?”
Ya ɗago idanunsa da ke a kulle ya ware a kaina, bai ce uffan ba sai zare hannunsa da ya yi daga riƙon da na yi masa, kuma kama hannun na yi ƙwalla na cika idona na ce “ya aka yi ka ji ciwo”
A fusace ya janye hannunsa tare da ɗago kaina ya matse kumatuna da ɗan ƙarfi, ya lumshe idonsa sai kuma ya sakeni ya ce “fita!” Cikin wani irin sanyi.
Kwarjinin da ya yi min da ya kafeni da idonsa sai na kasa yi masa musu, hawaye suka shiga zarya a idona, na juya ke nan ya riƙe hannuna tare da cewa “na sallameki, ki sanar wa Kala ta canza miki wajen aiki!” cikin wani irin sanyi yake magana