TAKUN SAKA 33
*_Chapter Thirty Three_*………..Can cikin dare Hibbah tai ɗan juyi cikin barci, da sauri ta sake mirginowa baya jin zata faɗa ƙasa. Gaba ɗaya ta manta a inda take ma. Ƙara bajewa tai jinta yanda takeso. Hakan sai ya sake bata damar matsawa jikin Master da har yanzu baiyi barci ba saboda zazzaɓi da jikinsa ya ɗauka mai zafin gaske.
Jin yanda ta matsosa har tana janye masa bargo ne ya sakashi ɗan buɗe idanunsa, hannu ya kai zai gyara bargon sai yaji ta duƙunƙunesa a jikinta, ya cija lip ɗinsa kamar ya mangareta, dan wannan shine karonsa na farko a rayuwa da yake kwance tare da mace a gado ɗaya. Ya ɗanja bargon da ƙarfi, Hibbah da batasan mi ake ba ta biyo bargon gaba ɗayanta ta shige jikinsa. Zafin zazzaɓinsa ya sata sake matsawa sosai dan ɗumin ya mata daɗi kasancewar itama har yanzu tana ɗan jin sanyi.
Saurin jan numfashi da rumtse idonsa yayi da ƙarfi. Babu shiri yakai hannu zai janyeta ta sake dabaibayesa har dayin filo da damtsen hannunsa. Ta sakala hanunta ta gefen cikinsa. Wani irin harbawa da ƙirjinsa yayine ya sakashi matseta babu shiri yana datse leɓansa cikin haƙora kai kace zai hudasu ne.
Ƴar ƙara Hibbah ta saki tana ƙoƙarin janye jikinta cikin lalube. Ina ta rigada tazo hannu, dan wani ƙara matseta yayi da ƙyau. Cikin rawar sanyi dana harshe ya ce, “Please ”. A hankali cikin kunnenta.
Kanta ta shiga jujjuya masa duk da kuwa a cikin duhu suke. Jikinta sai tsuma yake najin sabon al’amari ga rayuwarta. Bata sake tsurewa ba sai da ya tattaro jallabiyarsa dake jikinta yay sama da ita alamar zai cire dan ta rage masa wasu kaso na ɗumin jikin nata da yafi buƙata a yanzu. Duk da kuwa shima jikin nasa tsumar yake na shiga sabon yanayi akaf tarihin rayuwarsa. Rashin ƙarfin jiki da ciyo ya haddasa masa baisa tafi ƙarfinsa ba. Dan cikin ƙanƙanin lokaci ya zare rigar ya barta yanda Ummi ta sulmiyita duniya. Kuka ta fashe masa da shi tana yunƙurin tashi. Yasa hannu ya kuma matseta, cikin muryar ciwo da rakinsa ya fara magana a cikin kunnenta.
“Baki da tausayi ko?, kina son kiga na mutu. Please Muhibbat 30minutes kawai…”
Sake firgicewa Hibbah tayi dan bata taɓa jin makamanciyar muryar daga garesa ba. Gaba ɗaya ya tashi mata da ga Master data sani mai mazurai da tsare gida ya koma mata wani daban. Harga ALLAH tanajin tausayinsa, sai dai ayanda suken akwai tashin hankali da tsoron kar wani abu ya faru, dan sarai tasan minene aure, tunda tanada iliminta dai-dai gwargwado. Ɗan karatun nan na littafi tana taɓawa a waya, ga kawaye a gefe…….
“Ina jin tsoro Yaya Master, dan ALLAH kar kaimin komai”. Ta faɗa cikin suɓutar baki.
Duk da halin ciwo da yake ciki maganarta sai da ta saka wani lallausan murmushi subuce masa. Ya tura yatsun hannunsa cikin sumar kanta tare dayo ƙasa da kansa yasa goshinsa akan nata. Hancinsu na gogar na juna. Cikin shaƙaƙƙiyar muryarsa yace, “Ashe Tanee ɗin Ummi tasan minene aure?”.
Kanta ta shiga ja baya tana faɗin, “Ni wlhy A’a, dan ALLAH ka bari”. Yanda ta ƙare maganar hawaye na rige-rigen sakko mata a kumatu ya sashi sake yin murmushi da har taji sautin fitarsa a maƙoshinsa. A gefen zuciyarsa kuma yana sake yarda da tarbiyyarta, dan yanda ta ruɗe zai tabbatar maka bata taɓa tsintar kanta a yanayinba. “Relax!, Yaya master ba ɗan iska bane bazaiyi komai ba ga ƙanwar nan tasa mai bakin akku himyim??”.
Baki ta tura gaba duk da a cikin duhu suke. Ta sake ƙoƙarin ja baya ya sake matseta a jikinsa da har yanzu yake tsumar sanyi. Duk yanda taso ya barta hakan ya gagara. Dole ta nutsu waje guda badan taso ba. Sai dai yanda zuciyarta keta faman harbawa da sauri-sauri zai baka tabbacin haƙurin na dole ne kawai, ta riga tazo hannu babu mafita. Itama a ɓangarenta tana jiyo sautin motsin da zuciyarsa keyi a cikin ƙirjinsa. Har abin na bata mamaki da tsoro. Dukansu sunyi shiru kowa na sauraren na ɗan uwansa. A hankali barci ya fara fisgar Hibbah, dan yanda yake ɗan motsa yatsun hannunsa da har yanzu suke a cikin gashinta tanaji kamar yana mata susa ne.
Cikin ƙanƙanin lokaci Master ya farajin numfashinta na sauka a hankali jikinta na saki alamar barcin yaci ƙarfinta. Bakinsa ya matsar bisa goshinta ya sumbata da sake turata a jikinsa sosai yana maijin nutsuwa da wani yanki na guntun damuwarsa na sauka. Yayinda wata sassanyar ajiyar zuciya ke sauka a hankali. Sai gashi barcin da ya kasa tun ɗazun na fisgarsa yayinda jikinsa ke ƙara ɗaukar zafi.
Barcin da basu sami yi da wuri ba ya sakasu makara da asuba. Dan sai wajen bakwai saura Master ya farka. Har yanzu jikinsa da zazzaɓi bai gama sauka gaba ɗaya ba. Ga idanunsa sun ƙara girma na alamar mura ta tabbata. A hankali ya buɗe idonsa saboda nauyin da kansa yay masa. Akan Hibbah dake lafe a jikinsa ya saukesu. Barcinta take hankali kwance, gashin kanta daya warware dukya baje akan filon da fuskarta. Bakin da baya barin saita kwana yake kallo, idanunsa ya sake lumshewa da buɗewa a kanta lokaci guda. kafin ya saka yatsunsa yana janye mata gashin daya sakko mata akan fuska. Taɓa rumfar idonta da yatsansa yayi a mistake ya sata farkawa. Idanunta ta buɗe itama a hankali dan tama manta a inda take. Akan fuskar boginsa ta sauke, wadda inba faɗa maka akaiba bazaka taɓa ɗauka ba tashin bace. Wani zabura tai babu shiri tai azamar juya baya zuciyarta kamar zata wantsalo ta fito. “Innalillahi….” ta faɗa tana rumtse idanunta da ƙanƙame bargo da ƙarfi.
Uffan baice mata ba, sai ma mikewa yay zaune yana dafe kansa da yay masa nauyi. Kafin ya miƙe gaba ɗayansa ya nufi toilet da alamun har yanzu jikinsa babu ƙarfi. Yana shigewa Hibbah ta miƙe zaune da nufin guduwa tabar ɗakin sai ta ganta salin alin. Bama tasan sanda ta daddage ta fasa ƙara ba da maida bargon ta rufe jikinta.
Cikin sauri Master ya fito a zatonsa wani abune ya sameta. Yay saurin yaye bargon data ƙudundune a ciki, wata sabuwar ƙarar ta sake fasa masa da saurin faɗawa jikinsa ta duƙunƙunesa ita a dole batason yaga jikinta. Babu shiri wata dariya ta nema kufce masa. Dan ya fahimci abinda takema wannan kwakwazon. Sai dai yay ƙoƙarin danne dariyar ya dafe kansa da hannu ɗaya. Sanin su Habib na a cikin gidan yasashi fara mata magana a Master ɗinsa babu wasa. “ALLAH idan baki rufemin bakin nan ba a safiyarnan zan canjaki”.
Duk da magana yay ta hikima kuka Hibbah ta fashe masa da shi. “Ni wlhy bazan yarda ba. ni ba ƴar iska bace ka maidani wajen Ummi na. Ummina tace karna sake namiji ya tabamin jiki, amma kai har ganina kayi, nashiga ukuna ni Muhibbat bazan yafe ba.”
Ɗagota yay gaba ɗayanta ya maida ya zaunar, tai azamar lalubo bargo ta sake duƙunkunewa tana kuka wiwi. Harara ya zuba mata, cikin ɗan faɗa-faɗa yace, “Ohhh! To ni Mamyna tace na bari mace ta taɓamin jikine mai Ummi. Koni na gayyatoki bisa gadona? Idan wannan bakin baimin shiru ba anan na rantse sai na haɗiyesa”.
Ya ƙare maganar yana matsota da dungure mata kai. Babu shiri tasa bargon ta toshe bakinta hawaye na sakkowa. Sake zuba mata harar yayi da jan siririn tsaki yana miƙewa. “Sai shegen tsiwa ga tsoro”. Ya faɗa yana nufar toilet.