Uncategorized

TAKUN SAKA 34

*_Typing????

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

______________________

*_Chapter Thirty Four_*

………..Harta yanke ba’a ɗaga ba, sai dai da ga ƙarshe ake sanar mata ta dakata ana amsa wasu kiraye-kirayen ne. Bakin gado taje ta zauna tana sauraren a ɗaga ɗin, dan an saka taken ƙasa ne domin kar a bar mai jira shiru. Kusan mintuna uku ba’a amsa mata ba taji haushi ta yanke. Tagumi ta rafka ranta zattakaici, taci alwashi duk ma yanda za’ai a yau ɗin nan sai tayi sanadin da za’a kama Master da su Halilu. Bazata yarda ta kira yaya Abubakar ba dan gudun kar’a sake irin na farkon kaita wajen ƴan sanda.

  

       ★★★★

     A ɓangaren su Master kuwa koda Musbahu ya fita sai ya koma can gefe. Da wayar gayen nan da Zaidu ya sano musu yay amfani, sai da ya tabbatar yayi duk wani abunda bazai saka rayuwar gayen a haɗari ba sannan ya ƙaddamar da shirinsu. Cikin ƙanƙanin lokaci shi da Master dake can ana cike masa form yana danna waya da subaɗi suka shiga wawasar kuɗaɗe. Yayinda acan kuma su Salis suma suke kaddamar da nasu shirin akan sauran asusan. Dan yau aikine ba’akan mutum ɗaya ba. Kusan asusu goma sha zasu yashe a ƙiyasi.

          Master na gab da tatse kuɗaɗen asusai uku daya haɗa gabansa yay wata irin faɗuwa. Addu’a yay saurin karantowa zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri. Cikin sauri ya dubi Zaidu.

      “Ba’are anya kuwa baƙaƙen shanun gidan ɗan sandamu basu shirin kaima gonata ta yammaci hari? Inaji a jikina maƙwafcina ya samu damar yimin ƙafar angulu kuwa”.

        Kai tsaye Zaidu ya fahimci zaurencen, dan haka ya ɗan kallesa a ɗan firgice. “Alhaji Baba wanne maƙwafcin a ciki? Mati mai igiya ko sambo?”.

       “Bansan waye a cikiba ba’are, sai dai zuciyata na min zargin Mati mai igiya ne dan nayi kuskuren ajiye wayar lantarkin nan da za’aimin wayarin wuta a kogon ɓaure. A lokacin Kuma Mati na cikin gonata zai bani taimakon ruwa saboda zafin ranar da akai jiya. Inhar hasashena yayi dai-dai akan idonsa na ajiye wayar lantarkinnan. Ɗakko tarho ɗinka ka kira min ɗan ƙane ka shaida masa ya leƙa gonata ya bincikamin waya a cikin kogon ɓaure, sannan ya sanar maka Mati mai igiya yana kan tudune koya tashi?”.

       “An gama alhajin ALLAH”.

Zaidu da duk jikinsa ke tsuma ya faɗa yana nufar hanyar fita daga cikin bankin. Waya master ya ɗaga yay kira. Ana dagawa ya fara magana cikin wani zaurancen. “Sallau kun gama tattare harawar nan kuwa?”.

       Gaban Salis dake gab da kammala nasa aikin ya faɗi. Cikin ɗan waige-waige ya bashi amsa da faɗin, “Muna gab dai”.

       “To maza kuwa ku tattare dan Mati mai igiya ina tabbatar da ya turo baƙaƙen shanun ɗan sandamu cikin gonar yamma. Da alama kuma zasuyi ɓarna bawai a gonata kawai ba harda ta maƙota. Kuyi himmar tafiya gonar yamman harda su Kalla ku tasamin ƙeyar mati kafin shanunsa su iso ya koma gabashi. Ni kuma zan kira maigari na tabbatar masa tsiyar da matin ke shirin tafkawa”.

     Lokacin da Master ke wannan ƙoƙarin na fargar da yaransa halin da ake ciki a dai-dai lokacin Hibbah ta sake kiran wayar. Kuma cikin sa’a aka dauka mata. Jikinta har rawa yake jin an amsa. Daga can aka tabbatar mata ta kira wayar taimakon gaggawane daga police station mai lamba talatin da uku a anguwar andu dake jihar. Wane taimako take buƙata. 

       “Babu taimakon da nake bukata, ina dai tabbatar muku a yanzu haka gawurtaccen barawon nan da yaransa na kan hanyarsu ta wawasar kuɗaɗen wasu mutane ta banki. Nima satoni yayi yanzu haka sun barni anan gidanne sun wuce”.

      “What!?”.

Aka faɗa daga can ana mikewa. “Ƴammata minene sunan anguwar da kike yanzu haka?”.

       “Nima ban sani ba yallabai. sai dai ku bibiyi wannan kiran nasan zaku dace. Dan a yanzu haka suna gab da dawowa na tabbatar”.

      

★★★

      *_Bank_*

       Cikin jin haushi gaye yace, “Nikam Baba kodai baka shirya buɗe accaunt ɗin nan bane na kama gabana? Inada abunyi fa na zauna taimakonka amma sai wani kiran waya kake akan wata wayar lantarki ɗin banza ne ko harawa ma oho maka”.

         “Kai ja’iri waccan harawar tanada mahimmacin da tafi wannan buɗe akawun ɗin. Kaga nama fasa buɗewar sai wani satin zanzo da jikana muzo tare.”

     Master yay maganar yana mikewa. A take mutane suka shiga bashi haƙuri da wasu ma’aikatan bankin, amma fafir yaƙi dan gab aikinsa yake da kammala shiyyasama ya tsaya yana biye musu. Kuɗin daya wawasa na kammala shiga accaunt ɗinsa wani irin jiniya ya fara a cikin bankin. Yanda abin yazoma mutane a bazatane ya tsoratasu bankin ya hargitse aka fara fita a guje. Tuni master yabi rububi ya fice bayan ya cire babbar rigarsa da mask ɗin fuskarsa ya yarda, da sandarsa da carbi. Securitys da ma’aikatan bank ɗin da sukasan minene ma’anar jiniyar dan an sakatane saboda tsaro dama hankalinsu yay masifar tashi. dan fara ƙaɗawar jiniyar yayi dai-dai da fitar maƙudan kuɗaɗe a cikin wasu asusai biyar na manyan mutane dake bank ɗin. Ƙoƙarin hana mutane ake fita ta ƙarfin tsiya, yayinda daga cikin bank har sun kira jami’an tsaro.

     Master na fitowa ya sake cire dayar mask ɗin face ɗinsa ya yarda, dan zuwa yanzu zuciyarsa ta gama bashi Hibbah ta ɓallo musu ruwan da yafi na bankin tsauri. Sam baiyi tunanin taga sanda ya ajiye wayar nan ba. Babbar damuwar wayace da sam babu wani tsaro tare da ita sai idan tana a kashe. Dan yana amfani da itane wajen yin magana dasu A.G, ya tabbatar inhar ta kunnata ko tai kiran wani cikin sauƙi zasu gano inda take musamman da ya san saƙon da ya aika na wawashe musu kuɗaɗe zuwa yanzu ya isa garesu. Hankulansu yana a tashe ne, tare da tsintar kansu ckin ruɗanin yanda akai reshe ya juye da mujiya.

★★★★

              Kamar yanda Master yay hasashe hakance ta kasance. Dan kuwa aikinsu na cika dukkanin wayoyin su A.G saƙwanin alerts na fitar kuɗi suka fara shiga musu. Duk da a mabanbanta wajeje suke kusan a lokaci ɗaya duk suka miƙe zumbur a cikin matuƙar ruɗani da tashin hankali kowa na tambayar mike faruwa? Yaya haka?. Zukatansu na jera musu waɗan nan tambayoyin suna ƙoƙarin kiran juna. Cikin ƙanƙanin lokaci suka fahimci cewar ɗan zakin da suke tunanin sun raina ya girma. Dama a kwanakin nan babu abinda sukeyi sai zaman meeting akan Master. Dan zukatansu na raya musu lallai akwai abinda yake shiryawa shiyyasa yaƙi basu kuɗaɗen da ake tarawa tsahon shekaru biyu. Sun yankema kansu shawarar yana kammala musu aikin nan da suka bashi zasu ruftashi kawai. Sai gashi shi ya fara rufta rayuwarsu alamar shirinsa daɗaɗɗe ne a kansu.

     A.G ne ya saka bibiyar masa number master ɗin duk da basu da tabbacin samu, ana tsaka da bibiyarne batare da an samu ɗin ba Hibbah ta kunna wayar, cikin hanzari jami’in da ke zaune a computer room ɗin nasu yana aiki akan number ya sanarma A.G. shine ya bashi damar yin azamar saita layin akan duk kiran da za’ai ya shigo wayarsune, sannan ya bibiyi a inda lambar take. Shi kuma ya fita yana bada umarnin a haɗa runduna za’a fita operation na gaggawa. Yana dawowa computers room ɗin ya samu Hibbah na zuba bayani ta waya, kuma komai akan kunnensa shima ta zayyane.

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button