Comment on GARKUWA Page 51 to 60 (The end) by Unknown

“Kici kije da gudu ki kira Mata, tazo in gaya mata, su Ya Giɗi sun kusa dawowa ta dena kuka, anji lbrin inda suke”.
Rufe akoshin tayi kana ta miƙe da sauri tace.
“Da gaske ya Ba’ana an ji inda suke?”.
Cikin haɗe fuska yace.
“Na taɓa yimiki ƙarya ne?”.
Da sauri ta jujjuya kanta kana tace.
“Bari inje in gaya mata tazo sai inci naman a gida”.
Da sauri yace.
“A a jeki kirata, in tazo sai ki tafi da naman, kije kuci keda Ummiy da Bappa da ita ƙawar Mata, ita kuma zan bata nata a nan”.
Ai tana jin hakan ta juya ta tafi, da sassarfa.
Tana isa gida, ta kamo hannun Shatu, cikin haki tace.
“Adda Shatu taso, taso muje ya Ba’ana zai gaya miki inda su ya Giɗi suke, yace anji lbrinsu”.
Wani irin zabura tayi, hakama Rafi’a dake bakin ƙofar kitchin ɗinsu.
Cikin tarin kaɗuwa tace.
“Ke Junainah, kada kiyi mana ƙarya”.
Cikin haki tace.
“Wallahi tallahi, haka yace min zo muje kiji”.
Da sauri ta kamo hannun Rafi’a tace.
“Adda Rafi’a kema zo muje tare”.
Cikin jin daɗi Rafia tace.
“A a Junainah kuje, Ni kuma kafin ku dawo nayi mana abinda zamuci, da sauri tace.
“A a Adda Rafi’a ki bari kar kiyi girki, Innar ya Ba’ana ta aiko mana gasassun zabbi yanzu zan amso mana su sai muci”.
Murmushi tayi kana tace.
“To sai kinzo”.
Ita kam Shatu tuni ta fita, ta nufi Garkensu Ba’ana.
Ita kuwa Ummiy ido kawai ta zuba, musu tana son ta kira Shatu ta hanata zuwa amman ta kasa.
Ita kuwa Rafi’a kitchin ɗin ta shiga.
A can garkensu Ba’ana kuwa.
Yana hango Shatu, ya saki wani irin ajiyan zuciya, ido ya zuba mata,
Gaba ɗaya ta rame tayi fiyau da ita, fuskarta tayi jazir alamun yawan kuka, kana, ga kumbura da idanunta sukayi.
Da sauri take tafiya, sai dai tanayin takun a hankali ne, doguwar rigace a jikinta ta atampa, hijabi da ta saka wanda yazo mata har guiwa.
Ta ɗan ja hulan kan hijabin dan ya ɗan kare mata kumburarrun idanunta.
Wani zafi yakeji a ransa, Allah ya sani baya son ganin Shatu cikin damuwa duk ƙaƙantar-ta, yakanyi komai na zalumci, amman baya yi kan Shatu, shi kanshi ya yarda shi tantirine, azzalumi, kuma mugu, hakanan kuma ya yarda so gsky ne kuma so ɗaya ne tak kuma ya sani duniya ta sani yana son Shatu,
yana son sama mata farin ciki a rayuwarta, yana son su rayu tare. Shiyasa yake son rabata da kowa nata wanda suke ƙoƙarin ganin sun hanasu Kasancewa mata da miji.
Wani farin buzu ya shimfiɗa mata a bakin ƴar bukkartasa, tun kafin ta ƙara so.
Tana isowa, murya can ƙasa tace.
“Assalamu alaikum.”
Ido ya zubawa fuskarta cikin tausayawa yace.
“Mata ki zauna”. Murya a disashe tace.
“Ya Ba’ana ka amsa sallamar mana”.
murmushi ya ɗanyi kana yace.
“Mata na amsa bakijini bane”.
A hankali ta zauna bisa buzun, cikin sanyi ta lumshe idonta da takeji sun tsastsafo da zafafan hawaye, murya na rawa tace.
“Ya Ba’ana, wai anji lbrin su ya Gaini?”.
Matsowa yayi bakin bukkar, ido ya ɗan zubawa fuskarta, sabida lumahe idon da tayi batasan yana kallontaba ganin hawayenta na zubowa ne yashi yin mgna, a hankali yace.
“Mata, kiyi haƙuri, ki kontar da hankalinki, in dai yayunki suna raye, zan nemisu, ko dan farin cikinki, ki bar kuka Mata, bana son ganin hawayenki inajin ƙuna a raina”.
Ya ƙarishe mgnar murya can ƙasa.
Cikin rawan murya tace.
“Ya Ba’ana, ya zanyi? Ina zansa raina in ji sanyi, zuciyata tana ƙuna, Yayuna huɗu kab na rasasu lokaci ɗaya, bani da wa wanda zan nuna a faɗin nahiyar nan ince ga wani na a duniyar, babu ya Giɗi, wanda shine tamkar aboki ƙawa aminiya, abokin faɗata abokin dariyana, Babu ya Seyo, yaya mai kamar uwa, sabida yawan tausayinshi da nuna ƙaunarshi gareni, ko uwa iya abinda zata nunawa ɗanta kenan, babu ya Gaini da yake tamkar uba, babusu babu gawansu babu lbrinsu.
An kashe min ya Lado da yake GARKUWA a gareni.
Ya Ba’ana, ya zanyi in banyi kukaba, Ina zan fara nemansu, Ni macece inada rauni, ta ina zan nemosu? An kashe mana Innarmu”.
Ta ƙarishe mgnar tana mai kife kanta bisa guiwowinta ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciya, cikin kuka taci gaba da cewa.
“An kashe Inna, sanadin haka Ummiy na ta zama tamkar zautacciya, duk gidan dake cikin Rugar Bani babu gidan da ba’a kashe a ƙalla mutun biyarba a ƙaramin kari, suwaye ne ya Ba’ana, me mukayi musu? Me suke nema damu? Me muka tsare musu? Me laifinmu dan mun kasance Fulani makiyaya?”.
Karon forko a rayuwarsa da yaji rauni har ta kaishi ga zubda hawaye, koda yake raunin soyayyace, cikin zubda hawaye murya na rawa yace.
“Mata gani, zan zame miki madadin uwa, uba, yayunki, Inna, zan zame miki Garkuwa, in sha Allah bazan bari ki cutuba, zan bada raina domin kare naki, zan nema miki farinciki da dukkan abinda na mallaka na duniya, zan zame miki adalin miji, Mata ki dena kuka, kiyi haƙuri”.
Cikin shessheƙan kuka ta ɗago kanta, ta zuba mishi ido, tabbas kuka yakeyi kamar yadda ta zata, cikin mamaki tace.
“Ya Ba’ana meyasa kake kuka?”.
Hannun yasa ya sharce hawayenshi, karon forko a rayuwarsa da yayi abu ya gommace bayiba karo na forko a rayuwarsa da yayi mugunta yaji dana sani kan sace su Gaini. Da yatsarsa manuniya ya nunata, da mamaki tace.
“Nice na saka kuka?”. Kanshi ya gyaɗa mata, cikin al’ajab tace.
“Me nayi maka?”. Motsowa yayi ta bakin bukkar sosai can cikin sassanyan murya yace.
“Kukanki ne yasani kuka Mata,
farinci bazai samu gurbi a rayuwataba, muddin ke kina cikin ƙunci, dan Allah ki daina kuka,”.
A hankali tasa tafin hannunta ta share hawayenta.
Shi kuwa Ba’ana, wani babban kura tanɗu yajo, cikin sanyi ya ajiyeshi gabanta a tsakiyarsu. Cikin sanyi yace.
“Shatu”. Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi domin yauce karo na forko rana ta forko a tarihin rayuwarta da taji ya kirata da Shatu, cikin mamaki tace.
“Na’am ya Ba’ana”.
Girgiza kanshi yayi kana ya fara fito da wasu sabbin aska cikin zabirar da yanzu ya jawota, a hankali ya ɗago ya kalleta cikin yaƙini yace.
“Shatu, zan faɗa miki abinda, babu wanda ya sani a kaina a duniya, Shatu zan nuna miki abinda duk duniya ban yarda da in nunawa kowaba, sabida ban yarda da kowaba sai ke ɗaya rak Shatu, nasan zuciyarki ciki da woje, ke mai imanice, bazaki taɓa zalumtata ba, bazaki bari a kuma zalum ceniba. Na amince da soyayyarmu, zamu rayu a tare har gaban abadan.”
Ido kawai ta iya zuba mishi.
Ganin Junainah ta iso wurin ne, yasashi jawo akoshin gasassun zabbin gabanshi.
Ita kuwa Junainah da sauri ta kuma sa hannu zata jawo akoshin.
Kanshi ya jujjuya mata alamun ta bari.
Cikin kwaɓe fuska da ɗan karen kwaɗayi da yunwar da takeji yana azalzalar ƴaƴan hanjin cikinta tace.
“Yah Ba’ana ka bani mana yunwa nakeji”.
Cikin sanyi yace.
“Bazan bayar ba”.
Da sauri tasa hannu ta zari akoshin tayi gaba
Shatu ce ta fara kiranta tana.
“Junnu! Junnu!!! Junnuhhh!”.
Ina bata kulata bama bare ta juyo.
Shi kuwa Ba’ana ajiyan zuciya yayi tare da mgnar zuci.
“Uhummm ƙuda garin kwaɗayi kya mutu, kwaɗayinki ne zai karki”. Kai ya gyaɗa wa Shstu kana ya juyar da kanshi.
Ita kuwa Aysha shiru tayi tabi Junainah da ido.
Shi kuwa Ba’ana cikin sanyi ya wore ƙafafuwan sa,
takalmin roba na sau ciki wato, tashi kabi shanun dake ƙafarsa ya zare.
Sabbin askan ya ɗauka, kana ya fito da wasu ƴan kananun layu guda biyu.
cikin yaƙini yace.
“Shatu, kinga waɗannan layun?”.
Kai ta gyaɗa mishi cikin yin kici-kici da fuska.