TAKUN SAKA 46

*_Chapter Forty Six_*………..Duk da a yanayin da aka kawo su Hajiya mama ko’a jikin su A.G, sai ma wani kallonsu suke a wulaƙance. Hajiya mama dake kukan azabar da takeji a jikinta sai makyarkyata take dan kallon fuskokinsu kawai firgita rayuwarta yake.
Abba kam duk da a yanayin da yaga su Dr Sufi ɗin sai bai kawo komai a ransa ba. Ya duba A.G yana da ga zaune inda yaransu suka zubar da shi. “A.G ya halaka rayuwata, maimakon yaymin aiki sai yayi aiki akaina. Komai ya kwashe min, naira dubu 50 kawai ya barni da shi. Ya tafi da dukkan takardun dana bashi, na rantse bazan ƙyaleshi b……”
“Kai dalla yima mutane shiru”. Engineer ya katse Abba a harzuƙe. Ya nuna Abba da ke masa kallon mamaki. “Kai Halilu mu mun wuce kai mana wasan kwaikwayo anan. Yanzu kai ka rasa waɗanda zaka ruguza sai mu? Mune zaka cima dunduniya a garin nan bayan mune mukai maka sutura harka fito ake maka kallon mutum. Ka manta randa Balele ya kawoka nan tamkar ɗan dakon kashi. Amma bamu ƙyamaceka ba mukai maka buɗar kai da wanke duk wani datti naka da maƙudan kuɗaɗe. Shine a ƙarshe ka rasa waɗanda zaka halaka sai mu. mu zaka haɗa baki da matsiyacin yaron nan master kuci amanar mu……”
“Ni ɗin?!!”.
Abba ya faɗa a matuƙar razane har yana fama ciwonsa. Ya dafe ƙafar yana sakin marainiyar ƙara. Cikin rawar jiki ya shiga rantsuwa da ALLAH akan shi bai san wannan magana ta Engineer ba. Dan shi a gaba ɗaya rayuwarsa ma fa sau biyu ya taɓa ganin Master ɗin nan. Zaman farko da sukai ya bashi aiki kuma tare da A.G ne. Sai zama na biyu da sukai tare da su gaba ɗaya.
R.D ya sake katsesa da faɗin, “Kai maƙaryaci, idan har maganar daka faɗa gaskiyane yaya akai ya auri ƴar ɗan uwanka, sannan kuma matar da kake iƙirarin bakaso da manufa ka aureta ubanwaye ya sata barin gidanka ta koma wani daban? Mun kuma je can ɗaukarsu muka iske babu su a gidan”.
Abba da zuciyarsa ta fara hawa sama matuƙa yayma R.D ɗin wani shegen kallo, dama can yasan baya sonsa batun yanzu ba. “Amma yallaɓai ya kake magana haka kamar ba’a gabanku mukai komai da yaron nan ba a ranar. Miye haɗina da Asiya dazan ɓoyeta bayan nima nemanta nake ruwa a jallo. Ni kaga ma bansan ina suka koma ɗin ba har yanzu. Haka kazalika bansan an kamasu ɗin ba ma”.
“Ƙarya kake Halilu. Amma tunda bazaka faɗa ta arziƙi ba zaka faɗa ta yaren daya dace”. Cewar Alhaji Sallau a masife. Kafinma ya cema yaransu wani abu sun rufe Abban da duka shi da Hajiya mama. Cikin ƙanƙanin lokaci falon dama gidan baki ɗaya ya kaure da ihu da kururuwarsu. Abba da ya fahimci halakasu suke nemanyi a kiɗime ya nuna A.G. “Wlhy yasan komai, wlhy shi ya kamata ku tambaya inda master yake dan yafi kowa sanin sirrinsa anan wajen. Na tabbata da shi aka haɗa kai aka yashe mana kuɗaɗe dan nima shi naba takardun kaddarorina, kuma shine ya haɗani dashi, ta sanadinsa na sanshi”.
A razane A.G yake duban Abba, haka su Alhajin Mande ma a rikice suke kallon A.G ɗin. “Kai munafuki, ya kake neman ƙullamin sharri. Halilu anya ƙwalwar kanka kuwa bata samu matsala ba!!”.
“Na rantse da ALLAH kai ne”.
Abba ya sake faɗa cikin kuka wiwi. A.G da tuni zufa ta jiƙesa zaiyi magana Engineer ya katsesa cikin tafa hannu yana ƴar dariya. “Jama’a ga maganar Alhaji Sallau fa ta bayyana!”.
“Ban gane ta bayyana ba! Mi kake nufi?”. Cewar A.G yana kallonsa hankali tashe.
“Abinda kowa yaji a kunnensa mana A.G”. A matuƙar hargitse A.G ya miƙe ido rufe ya yarfama Engineer wani gigitaccen mari da sai da wutar kansa ta ɗauke. Abinka da jami’in tsaro yasan sirrin cin uban mutum. A razane duk suka miƙe baki buɗe. Har suna haɗa baki wajen ambatar sunan A.G ɗin.
A.G da gaba ɗaya ya birkice yace, “Sunana ne. Tayaya wannan mara mutuncin zai duba tsabar idona ya alaƙantani da cin amanarku. Duk iya ƙoƙarin da nake muku akan ɗan iskan yaron nan baƙwa gani har takai yau za’a kalleni da wannan suffar. In ban kashe Engineer ba kuce bani bane A.G”.
Da sauri Alhajin Mande ya riƙosa. “Haba A.G yada harzuƙa haka daga magana. A gabanka fa Halilu yace kaine minene laifin Engineer?”.
“Okay bakagama laifinsa ba! To yayi. Kai kuyita dukan Halilu da uwarsa har sai ya faɗi gaskiya”.
Tamkar ƙyaftawar ido zaratan samarin suka shiga lugudar su Abba har sai da suka suma aka zuba musu ruwa suka farfaɗo. Sake cigaba da dukansu sukai kuma babu ko tausayi balle duban tsufan Hajiya mama. Ganin zasu iya mutuwa Dr Sufi yace, “Nifa ina ganin duka bashi magani, idan kuma kun kashe Halilu ta ina zamu samu wani information kenan”.
Maganarsa ce ta saka Alhajin Mande dakatar dasu. Da ga Hajiya mama har Abba nishin azabar fitar rai kawai sukeyi. Dan tabbas sun sadaƙar yau kam zasu iya barin duniyar nan ma baki ɗaya.
Faɗa ya cigaba a tsakaninsu dan sufa sunƙi yarda da rantsuwar da A.G ke kwarara musu akan ƙarya Abba ke masa. Shi kuma ganin sunƙi fahimtarsa ya sake birkice musu kawai har takaisa ga fara dambatawa shi da Engineer da yafi kowa zaƙewa duk da tsufansu….
_________________________
A ɓangaren Master kam koda suka baro wajen su Ummi kai tsaye station suka nufa dan I.G ya shigo gari suna tare da C.P ma. Yaya Abubakar yayi matuƙar mamakin ganin inda sukazo, musamman daya san ana neman Isma’ill ɗinne ruwa a jallo. Sai dai kuma zargin daya jima a ransa ya sakashi yin shiru domin ganin ƙarshen wasan. Kasancewar Master bada fuskar Muhammad Shuraim yazo musu ba babu wanda yace da shi uffan. Sai dai saboda Abdull da wasu tsiraru ke gaishesu kasancewar sunsan yaron I.G ne. Sai ko shi yaya Abubakar daya haɗu da mutane biyu da ya sani.
Dama I.G ya shigo ne saboda case ɗin dake a hannun Master ɗin, dan haka sunayin knocking aka basu iznin shiga. Yaya Abubakar da Master suka ƙame kusan a tare domin girmamawa ga I.G da C.P.
Yaya Abubakar yay saurin juyowa ya duba Master, shima da yake shiɗin yake kallo sai ya sakar masa murmushi kawai ya ɗauke kansa ya maida ga I.G dake magana.
“C.P wannan shine A.S.P Muhammad Shuraim Aliyu, jami’i ne mai ƙwazo, dan haka na ɗorasa akan case ɗin nan na yaron nan master a sirrance. Bakuma hakan na nufin su waɗancan da suke aiki akan hakan bazasu cigaba ba”.
“Okay sir”.
Cewar C.P a girmame yana duban Master da ya ɗan sake ƙame jikinsa domin girmamawa ga C.P.
“A.S.P!”.
“Yes sir”.
Master ya amsama C.P ɗin.
“Tunda boss ya tabbatar da ƙwarewarka hundred percent muma mun yarda. Ina fatan kasan wannan aikine na gaggawa kuma mai buƙatar jajircewa. Duniya gaba ɗaya ta ɗauka burinta kawai taga Master a hannunmu, kowace hukuma ta tsaro farautarsa take domin ta kasance mai nasara. Kamar yanda wasu daga cikin jami’an mu suka tabbatar da harbinsa har sau biyu bazai kasance yayi nisa ba. Lallai-lallai yana cikin garin nan baije ko’ina ba, dan babu wata hanya da ba’a saka jami’an tsaro ba tun bayan mintuna goma sha bakwai da harbin nasa. Waɗannan mintunan kuma sunyi kaɗan ace ya fita a garin nan. Dan haka munada tabbacin yana cikin garin nan. Akwai teams da yawa dake zagaye da case ɗin nan, dan haka kaima zaka haɗa naka team ɗinne dan bama buƙatar duk waɗan can a naka operation ɗin”.