Baiwata

BAIWA 4

SADAUKARWA GA

  *AHALINA*

GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.) 🤜🤛
(Burinmu d’aga muryoyinmu sama domin anfanar da al’umma had’e da ciyar da adabin hausa.)
[G. M. N. A] ☆ 📖🖊️

Bismillahir rahamanir rahim

              _4_

Da mamaki Alhaji Yusuf ya kalli Saleema yace “Me ya sa baki zo gida ki sha ruwan ba? Gidan ya na da tsafta ne?”

D’aga kai kawai tayi tana ci gaba da rarraba ido alamar rashin gaskiya, Safiya dake kallonta sarai ta fahimci gidan da ta je, wato ta tsaya wajen Hafsatu mai d’inki ko? Girgiza kai kawai tayi ta mik’o hannu ta karb’i ledar aiken ta shige ciki, cike da farin ciki Saleema jin Abbanta bai mata fad’a ba, Mamanta ma haka sai kawai ta shige ciki da zumud’in wayewar garin gobe dan ta je ta nuna wa Hafsatu d’inkin da ta yi kamar yanda ta buk’ata.

Tana idar da sallah azahar ta fito kai tsaye k’ofa ta nufa wajen mai gadi tace “K’awata ta zo?”

“A’a.” Ya bata amsa, juyawa tayi za ta koma sai yace “Ga ta nan Hajia.”

Da sauri ta juyo da farin ciki ta kama hannun matashiyar da ba za su wuce tsara ba, kai tsaye d’akin Mahaifiyarta ta wuce da ita kamar kullum, tana zama kan kujera ta fara ciro litattafan da suke karatu da su, d’auko na ta tayi ta zauna kusanta tace” Yau me malam ya koya muku?”

Nuna mata tayi tace” Gashi nan, shi ne zan koya miki ke ma, kuma malam ya ce wai ki maida hankali sosai.”

Da fara’a ta jinjina kai tana jin dad’in yanda malamin na su ke nuna kulawarsa a kanta, tunda aka hanasu zuwa makarantar ya ke turo k’anwarsa tana d’ora mata karatun, ya yi iya k’ok’arinshi ma su had’u da mahaifin Saleema dan su yi magana kan kar a dagula mata karatunta amma Alhaji Yusuf ya k’i yarda su had’u, dan haka Saleema ta kawo wannan shawarar duk da yana tsoron abinda zai faru, amma dai gashi izuwa yanzu har an shekara d’aya ba abinda ya faru, alamu ne na mahaifin bai iya saka ido sosai a kan yaranshi ba kenan, dan da yana saka ido akan motsin ‘ya’yan shi mata da yanzu ya fahimta duba da har bayan sallah isha’i a na zuwa a d’ora mata karatun.

    *Washe gari*

Mik’ewar da ta yi daga kan teburin ya sa shi kallonta yace “Mamana ba dai kin k’oshi ba?”

“E Abba.” Ta fad’a tana wucewa abun ta, da kallo suka bita har ta shige d’akin, jim kad’an ta fito daga d’akin da jakarta da ta b’oye a cikin hijabi ta nufi hanyar fita, Safiya ce ta kalleta tace “Ina za ki je kuma ?”

Littafin makarantar ta ta nuna tace “Mama wajen Khairat zan je ta koya min lissafin nan.”

Harara ta wurga mata tace “Kuma shine sai yanzu da safiya za ki je musu ? Ki…”

Da sauri Alhaji Yusuf ya katseta da fad’in “Karatu fa ta ce za ta je, ki barta ta tafi.”

Kallon Saleema ya yi yace “Uwata ta kaina, je ki kin ji sai kin dawo.”

Ai da sauri ta wuce kamar za ta daka da gudu saboda farin ciki. Tana fita ba ta zame ko ina ba sai gidan Hafsatu, kayan da ta nuna mata yasa Hafsatu mamaki da ta tabbatar mata ita tayi duk da na yara ne, da mamaki ta sake kallonta tace “Amma ta ya kika d’inkasu?”

Cike da jin dad’in an yaba mata tace “Idan Mamanmu suka je karb’an d’inkinsu ne wajen tela sai na hau na yi.”

Da fara’a a fuskar Hafsatu tace “Da gaske?”

Jinjina kai tayi alamar e, ita ma jinjina kan tayi tave “Masha Allah, kinga kam da Abbanki zai siya miki tela cikin sauri za ki iya d’inki.”

Kallon fuskarta tayi tace “To amma za ki dinga koya min?”

“Sosai ma.” Ta fad’a tana jinjina kai, dariya tayi tace “To zan fad’a masa.”

Ko da ta dawo ta samu Mamanta d’aki take fad’a mata “Mama, aunty Hafsatu ta ce wai na fad’a ma Abba ya siya min tela za ta koya min d’inki.”

Da mamaki Safiya ta kalleta tace “To, ke kuma yaushe kukayi haka?”

Cike da shagwab’a tace “Yanzu ai na biya can.”

Kallon tuhuma ta mata tace “Kin tabbata karatu kika je ?”

Jim ta yi tana kallonta da tunanin kar dai ta fad’a mata ta hanata ko ta fad’awa Abbanta, sai kawai ta d’aga kai alamar e tare da fad’in “Allah ko Mama.”

Jinjina kai tayi tace “Ni dai ba zan fad’a masa wannan shirmen ba, ki bari har ki fara koyon d’inkin tukuna, idan kika iya sai a siya miki.”

Takwaf takwaf tayi da fuska tace “Amma Mama ai dama cewa ta yi idan na je can na koyo na dawo gida sai na dinga aiki da telata, ta hakane zan fi sauk’in zama mad’inkiya.”

Girgiza kai Safiya tayi tace “Saleema, abun da mahaifinki ya ke so ki zama daban, abin da ke kike so daban.”

Sake girgiza kai tayi tace “Allah ya zab’a miki ma fi alkairi.”

Dariya Saleema tayi cike da yarinta tace “Mama idan na iya d’inki kinga faba sai kun kai ba, ni da kaina zan muku ke da aunty da su Hadeeya.” Murmushi kawai tayi a ganinta shirmen Saleema ne kawai.

Bayan Wata uku

Duk girman farfajiyar gidan nan ta su cike yake da maza da mata, abun mamakin kuma yanda mata da mazan ke cakud’e wuri d’aya, kafatanin taron babu macen da ke d’auke da babban gyale bare hijab, dukansu shiga ce ta alfarma dake nuna matsayin kowace da kuma rayuwar da take ciki, kusan kowace riga da siket ne jikinta ta sagala mayafinta a kafad’a, mai d’an dama dama a cikinsu ce za ta d’orashi duka kafad’un biyu, inda fuskokinsu ke d’auke da rantsatsiyar kwalliyar da suka biya mak’odan kud’i aka cab’a musu ita, wasunsu ma har da zubo da gashi suke ya kwanta har kan wuyansu wanda aka kashe ma kud’i, jaka da takalmi masu sababin tsini kuma suka ce ja bani waje.

Ba wannan ne abun tsaya wa a kalla ba sai yanda gurin ba zaka gane ina matar wane ko waccen ba, saboda bariki da wayewa ya sa kowane namiji ya saki matarsa a wani wurin yana gaisawa da abokai da kuma matan abokan, inda su ma matan ke gaisawa da abokan mazan da kuma matansu.

Takon tafiyarta yasa dayawa daga cikin taron juyawa suna kallon mai tahowa, Ardayi ce cikin tsadaddar shiga wacce ta dace da yanayinta, kalarta da kuma jikinta, wanda hakan yasa ta sake haska wurin gwanin birgewa, iya d’an kwalin dake d’aure a kanta ne kawai, duk rabin wuyan rigar nan a waje yake yayin da siket d’in ya matse jikinta sosai, komai na jikinta ya bayyana ya fito mata da surarta. Alhaji Yusuf dake tsaye kusan abokanshi yana kallonta, murmushi kawai a saki ganin yanda abokanshi ke kallonta alamu ne na ta birge sai abun ya sa ya ji dad’i da jin cewa lallai ya yanko wulak’anci wannan wurin, duk da ‘yar k’ibar dake gareta amma ba za ka ganta ka ce ita ta haifi su Hadeeya ba saboda iya d’aukar wanka.

Saleema na gefe zaune akan kujerar k’arfe mai zaman mutum biyu, daga nan take hangen irin bidirin da ake inda hankalinta ya fi karkata kan irin d’inkunan dake jikin mata, duk da k’arancin shekarunta amma tana mamakin yanda mahaifinta ya fi ba wa wannan rayuwa mahimmanci fiye da komai, ita dai a kan idonta ta ga ya kashe kud’in da suka ba million baya a kan abinda za’a tarbi bak’in nan kawai saboda su tayashi murna na girma da ya k’ara samu a wajen aikinshi kasancewarshi malamin kud’i, a iya saninta ita dai ba ta tab’a ganin wata bajinta da mahaifinta ya yi ba ga addininshi da zai nuna ya na kishin addinin na sa, dama dama ma idan azumi ya zo, a masallacin dake jikin gidan na su ya kan sa wa ana fitar da abun bud’a baki ga mabuk’ata, sai kuma abun sahur idan aka fara sallah tahajjud, wannan ne za ta iya cewa aikin alkairin dazata iya shaida mahaifinta na yi.

Maida kallonta tayi kan Hadeeya da ta shirya ko ta ce mahaifiyarsu ta shiryata cikin wata arniyar rigar kanti iya gwiwoyin Hadeeyar, ta yi kyau sosai dan ka rantse ma yar turawa ce, sai dai a ganin Saleema kamar ba ta dace ba, sam gani take yi shigar ba ta birgeta ba. A hankali ta sadda kanta kan takardarta fara tas sannan ta fara zana wuyan rigar da ta ga Mamanta ta saka d’azu ita ma da za ta zo wajen taron, dan wuyan ya burgeta sosai hakan yasa ta tsurawa rigar ido ta gama hardaceta a kan ta kafin Safiyar ta saka.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button