Uncategorized

TAKUN SAKA 44

*_Chapter Forty Four_*…………Ba’a ƙaramin harmutse su A.G suke ba. Dan ƙaimin da suke nunawa akan neman master yasa mafi yawan al’umma maida hankali garesu da son ganin yaya za’a kwashe. A gefe kuwa sunyi zaman meeting yafi sau goma shi da su Alhajin Mande. Gaba ɗayansu sun fita hayyacinsu cikin lokaci

ƙanƙani. Babu iyalai babu kuɗi. Dan ma mutane manya irinsu da suke huɗɗar arziƙi nata tura musu kuɗaɗe ana musu jaje. Hakanne ya ɗan sanya zukatansu ƙarfin ringa zaman meeting akan Master ɗin da suka kasa samun bakin zare koda guda akansa. Sai dai ga al’umma sai faman cika baki suke akan suna gab.      Yau ma kamar kullum bayan A.G ya gama da zaman meeting ɗinsu na jami’an tsaro nan yayo gidan hutun Alhaji Mande. Inda gaba ɗayansu sun hallara ne domin tattaunawa tamkar yanda suka saba.

        A kallo guda da zaka musu zaka fahimci ɗunbin damuwar dake tattare da rayuwarsu, da yawansu hawan jini neman bugesu yake, wasu kam dama suna da shi ya motsa yana neman fin ƙarfinsu. R.D da yafi kowa jigata ya duba A.G idanu jajur dan sai da ya kora giyarsa yay mankas ko zaiji ɗan sanyi a ransa.

     “A.G ya ake ciki ne wai? Har yanzu matsiyacin nan ba’a gano inda yake a fake ba?”.

          Kai A.G ya girgiza masa, shi kansa har wata ramar dole yayi a kwana ukun nan. Cikin rauni da ɗacin murya yace, “Lamarinsa ya fara bani tsoro gaskiya. Dukan hanyoyin da muka sani ada da mafakarsa jami’anmu sun shiga amma babu alamarsa. Sannan babban abinda ke ban mamaki ko yaransa su katafila banga alamar zamuga kowa ba, idanma kunyi tunani ya jima baya barin mu haɗu dasu. Anya kuwa yaron nan ba ƙasar nan ya bari ba…”

         “Ƙasa kuma? Haba A.G ya kake wannan maganar tamkar ba jami’in tsaro ba. Tayaya zai iya ƙetare wannan ƙasar bayan bala’in da yake ciki ta ko’ina nemansa akeyi. Kadai sake wani tunanin amma ba wannan ba. Idan ma ance yabar ƙasa su kuma iyalanmu fa?”.

      “Gaskiya ne Engineer. Nima dai nafi yarda da cewar wanine ya bashi mafaka kodai a cikinmu, kokuma wanda ya sammu, danni nama fara zargin acikinmu ɗin nan akwai maiyi mana SARAN ƁOYE wlhy…”

      A harzuƙe Dr Sufi yace, “Haba Alhaji Sallau ya zakai wannan maganar haka babu daɗin ji. Shekararmu nawa tare babu wanda ya taɓa munafuntar wani sai a yanzu da muke a tsaka mai wuya. Naga yaron nan tare ya kwashe mana kuɗaɗe, yay kidnapping iyalanmu. Ta yaya za’a zargi wani kuma banda dai son zuciya!!”.

      A harzuƙe Alhaji Sallau ma yace, “Ya kakemin ihu danna faɗi gaskiya. Dan an sace iyalanmu tare an kwashe mana kuɗi sai ya zama lallai zukatanmu ɗaya. Ai wanda ma zai munafuncemu ɗin zai iya yarda a kwashi kuɗin nasa da iyalan dan ya bada ƙafa. Ya dawo cikinmu kuma yana jin sirrikanmu yanda bazamu taɓa sanin ina matsiyacin nan yake ba. Inba da saka hannun wani acikin namu ba tayaya za’ai wannan ɗan iskan yaron da muka raina da hannunmu yafi ƙarfinmu. Yanda kukasan ya mana magani muka dinga barin masa tarin kuɗi a hannunsa mun gagara cewa uwar komai ma sobada mu manyan lusarai ne…..”

      Alhajin Mande ya katsesu a tsawace da faɗin, “Kai ya isa haka dan ALLAH. Dr Sufi, Alhaji Sallau ya kamata ku barmu muji da damuwarmu. Idan hankali ya ɓata hankali ke nemosa ba wannan haukar naku ba.”

        Engineer da ransa ya ɓaci shima yace, “Faɗa musu dai dan ALLAH. Kai nifa bama irin tunaninku duk nakeyiba a yanzun. Tunanina tun a daren jiya ya karkata ne ga wata katoɓara da mukayi”.

      “Tami?”.

Cewar R.D cikin rawar jiki.

      Engineer yace, “Ta kawo Halilu cikin al’amarinmu na kwanaki. Bana raba ɗayan biyu Halilu yasan ina yaron nan yake. Kuma ko tantama babu ranar da yazo suka haɗu da shi koda ya fita bai tafi ba laɓewa yay yaji sirrinmu. Kugafa ya yashe masa accaunt shima amma bai ɗaukar masa iyalai ba. Sannan matar tasa da ƴaƴan ɗan uwansa mun aika dan a ɗauka mana su an tarar basu a gidan har wajen aikinsu. Ya kamata ku sakama wannan batun alamar tambaya. Yanda Halilu yake mayen kuɗi ace an yashe accaunt ɗinsa harda kuɗin daya ƙwallafama rai amma zuciyarsa batako bugaba. Wannan al’amari da matuƙar mamaki yake”.

       Kusan gaba ɗayansu sun nutsu suna sauraren Engineer ne. A fuskokinsu kuma zaka tabbatar da zancen nasa na shigarsu matuƙa. Alhajin Mande yace, “Wato Engineer kanka naja matuƙa. Kuma wlhy Halilu komai zai iya aikatawa akan kuɗi. Ka tuna abinda sukaima Alhaji Dauda shi da Balele. Karku manta yaranmune fa su, amma yaran nan har wani gasar sayen motoci da gina gidaje sukeyi damu. Bayan mune muka sakasu a harkar nan muka kuma jiƙasu da dukiyar da suke taƙama da ita. Lallai a nemo mana Halilu ya amsa tambayoyi”.

       A take duk suka gamsu da hakan. Babu wani ɓata lokaci A.G ya kira yaransa biyu ya aikasu gidan su Hibbah ɗakko Halilu.

(Kawunmu????????????????).

★★★

       Tunda abinnan ya faru Abba baida maraba da zararre. Bashi kawai ba hatta hajiya mama da momy basa cikin hayyacinsu. Yaranma kansu hankulansu a tashe yake. Dan suma ba ƙaramin shanawa suke da dukiyarba gashi yanzu komai an yashe. Ga Junaid babu lafiya hakama Abban. Duk wani motsinsa zakaji yanata surutai da lissafin kuɗaɗe. Koda mai gyaran karaya ma ya dawo domin duba ƙafarsa data goce ranar ansha fallasa. Dan surutai yayta zubawa harda yanda ya ƙulla alaƙa da master. Hankalin su Momy ya tashi, indama ALLAH ya taimakesu dagasu sai su sai ko mai gadi daya taimaka musu suka riƙesa. Mai gyara kuwa basa tunanin ma yana fahimtar inda zantukan na Abba suka dosa. Bayan an kammala gyaran suka sallamesa da abinda ya samu. Surutan Abban ne yasa suka banka masa maganin barci. Koda ya farka kuwa sambatun yake yana kuka da faɗa musu yawan kuɗinsa da master ya yashe.

         Hajiya mama da lamarin keta sake birkita mata tunani ta kora su Momy waje ta kulle ɗakin tanama Abba tambayoyi. Bai ɓoye mata komai ba akan kuɗaɗen da yaso handamewa dan mafita yake nema yanzun. Hankalin Hajiya mama a tashe ta yarfa masa mari tana kuka. “Yanzu nan Halilu sokai ka kashemin jikoki kenan? Inda kamin bayani duk yanda zanyi kuɗin su dawo hannunmu ni ai zanyi. Koda kake ganin bana kula su Muhammadu ina sonsu kodan Aliyuna. Uwarsu ce kawai ni bana ƙauna dan bata da tsarki ƴar zina ce. Yanzu ai gashi nan mu bamuci kuɗinba wani matsiyaci ya cinye harda nakan daka tara da guminka. ALLAH wadaranka Halilu lusarin banza. Wlhy ni haihuwarka bata amfaneni da komaiba, dama kai ka mutu aka barmin Aliyuna. Dan ni dai tunda na haifoka duniyarnan banda masifu da tashin hankali babu abinda kake jangwalomin. Ga waɗannan shegun ƴaƴan naka nan riɗa-riɗa a cikin gida suna kallon kansu dai-dai damu babu aure”.

     Takaici yasa Abba saka ƙafarsa mai lafiya ya hankaɗa Hajiya mama dake kusa da shi zaune a bakin gadon ta faɗa. Wata irin wahalliyar ƙara ta saki tana dafe ƙugu dan azaba. Da gudu su Momy suka iso ƙofar sai dai kuma a rufe. Yanda Hajiya mama ke ihu da kururuwar ƙugunta yasa dole aka kira maigadi ya ɓalle ƙofar. Kafin su shigo ta haɗa gumi tayi kashirɓan dan azaba. Duk kanta suka rufu, yayinda Abba ya juya musu baya yana kwasar kukansa shima.

       Yanda take jera kalaman tsinuwa ga Halilu da gaba ɗaya zuci’arsa ne ya bama su momy mamaki suka shiga tambayarta miya faru?. Cikin kuka da azaba tai musu bayanin shine ya turota a gadon. Bakuma zata yafe masa ba. Sudai komai basu iya sunce ba. Dan sun lura Abban da Hajiya maman neman basu sabon ciwon kai suke bayan wanda suke ciki. Ga gida zagaye da jami’an tsaro an hanasu fita ko ƙofa. 

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button