Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 54

Episode 54

……….Koda suka kammala falon suka sake dawowa, ya kuma ɗaure fuska yanda bazata roƙesa fitar ba. Dole ta kama kanta dan kuwa koda ya zaunar da itama

karshen 3seater sai ya kwanta shi ya ɗaura kansa a cinyarta. Ya kuma kamo hannayenta duk biyu ya ɗora a sumarsa sannan ya canja musu tasha.
     Raudha babu bakin magana, tun tana cuna baki gaba har laushin sumar da takema kallon zatai ƙarfi saboda yanayinta na irin tamu ada ya fisgeta ta tura

yatsunta a ciki a hankanli. Lumshe idanu Ramadhan yayi da sauke numfashi a hankali dan hakan abune da yake matuƙar so a rayuwarsa shima.
      A hankali ta cigaba da wasa da yataunta cikin sumar cike da shauƙi harta shagala ta manta dawa take tare. Haka ta cigaba da wasa da sumar kansa cikin

shagala tana kallon film, yayinda shi nashi idon ke’a lumshe ya lula duniyar tunani.

      ★Kowa bai damu da rashin ganinsu a gidan ba har yamma, sai gimbiya Su’adah ce data cika tai fam da takaici, dan har Muneera ta aiko tai mata cid ɗinsu

ta koma ta sanar mata ai duk yau ma bata tunanin Raudha taga rana. Gara Ramadhan kan fita yayo salla. Dama kuma shi yaje ya gaisheta da safe ma.. Har lunch

ta shirya masa da kanta da maganin da Adda Asmah ta kawo waina fidda son Raudha a ransane ya tsaneta. Har sai ya mata korar kare a government house. Sai dai

abinda bata sani ba na tsananin jan ra’ayinsa da mallakar zuciyarsane akan Ayna’u, malamin daya bata ya tabbatar mata Ramadhan yaci maganin nan sai ya manta

har gimbiya Su’adah ɗin ma da kaf Taura family ya koma ƙarƙashin ikon ƴarta Ayna’u, hatta da mulkin ƙasar NAYA Aynah ce zata koma mai tsarawa da zartar da

yanda za’ayi.
      Sai dai kuma Ramadhan ya kwafsa mata baije sashen da rana ba. Washe garima babu wanda ya gansu, sai randa suka cika kwana uku yaje sashen nata shi da

Raudha da rana. Hakan baisa ta gaza tanadin na dare ba a cikin gasashshiyar kazar da taji kayan haɗi na ban mamaki aka aika masa har sashen Anne da kunun

madara da yasha zuma a ciki a wannan rana. Ita kanta Raudha basu ƙyaleta ba. A baki Bilkisu sukaji abinda tafi so, amma kasancewar guri ya ƙure aka haɗa

mata zoɓo mai sauƙi aka barbaɗe da magani sanin Ramadhan baya shan zoɓo shi kuma.
     Tunda Lubnah ta nufi sashen Anne da abinci sai kuma zuciyar gimbiya Su’adah ta shiga ƙunci, rasa mike mata daɗi tayi tanata faman kaikawo a bedroom

ɗinta. Gaba ɗaya zuciyarta na nuna mata ƙiyayya da abinda ta aikata akan ɗan data haifa saboda tsanar matarsa. Sai dai kiyayyar da takeji akan Raudha nata

ƙoƙarin danne gaskiyar dake son bayyana kanta ga kuskuren da idonta ya rufe ta kasa fahimta…

       Sam Anne bata kawo komai a ranta ba ta haɗa kayan wajen gimbiya Su’adah a cikin dinner ɗin su Ramadhan. Taya ma zatai tunanin za’ai amfani da uwa

wajen cutar da ɗanta? Ita bama ta taɓa kawoma ranta wani cikin surukan nata na bin malamai koda akan Pa ba. Tama shedesu akan hakan ɗari bisa ɗari dan bata

taɓa ganiba gaskiya. Ita kuma mutumce da bata yanke hukunci akan abinda bata ganiba sam.
          Raudha yarinyace mai tsarta, haka kawai taji gabanta na faɗuwa lokacin da sukai zaman cin abincin. ALLAH ta shiga ambato a zuciyarta, yayinda

Ramadhan gashin kaza ya ruɗesa ya ɗan ɗiba da cokali mai yatsu ya kai bakinsa yana ambaton “uhhm”. Kallonsa tai kawai batare data iya cewa komai ba. Sai da

zai kai lauma ta biyu ne ALLAH ya bashi ikon ambaton Bismillah. Ƙaramar ajiyar zuciya ta sauke, koda yace suci kazan catai ta ƙoshi, dan itakam idan tace

zatai irin cin namansa ai matsala za’a samu. Bai wani ci da yawa ba ya tashi akan zaije wajen meeting idan an tashi yazo yaci. Amma ta tabbatar taci abinci

inba hakaba ya dawo ɗura zai mata da kansa.

     Gimbiya Su'adah ce ƙarshen shigowa. Ramadhan ya gaidata cike da kunyar tun safe bai koma sashenta ba. Koda yake Anne ma da suke tare sai ya fito 

salla take ganinsa. Ya ɗanyi mamakin yanda ta amsa masa a sake, ta kuma gaida su Anne itama. Kowa zaune yake a kujera har su Yafendo, shine kaɗai zaune

ƙasan lallausan carpet ɗin falon domin girmamawa ga iyayensa.
     Ba Ramadhan ɗin kaɗai ba, hatta su Pa sakewar gimbiya Su’adah ya basu mamaki, duk da suna danganta hakan da abinda ta kawo take ganin zataci nasara. Su

dai babu ruwansu, idan Ramadhan ya amince ya karɓa zasu tayasa so, idan baya so kam bazasu masa dole ba tunda yay musu biyayya akan Raudha kar su cika shiga

hakkinsa.
  Bayan an buɗe taro da addu’a Bappi ya bama Gimbiya su’adah damar faɗin abinda tazo musu da shi kafin yau. Tunda ta fara bayani Ramadhan ya ɗago a

rikice yana duban mahaifiyar tasa. Fara’ar fuskarsa kuwa tuni ta ɓace sai dai komai baice ba harta kammala. Bappi ya jinjina kansa da maida hankalinsa ga

Ramadhan da ya maida kansa ƙasa.
      “Ramadhan kaji abinda mahaifiyarka tace. Tana buƙatar ka auri ɗiyar ƴar uwarta domin likita ya sanar matarka bazata sake haihuwa ba saboda ciki data

zubar a kwanaki”.
       Ramadhan daketa jera kalmomin innalillahi a zuciya ya nisa da ƙyar. Abinda Maah bata sani ba ya daɗe da kammala bincike akan yanda Raudha tasha

magani, sai dai takamaimai wanda ya bama su Muneera maganin suka zuba mata dama yake nema ruwa a jallo. Sai gashi a cikin sauƙi ta tabbatar masa da itace,

domin inba itace ɗinba taya tasan mahaifar Raudha zata lalace harta gagara haihuwa….?
      “Ramadhan!”.
Inna dake gefensa ta kira sunansa. Numfashi ya furzar da ɗago idanunsa da suka kaɗa ya kalleta. Sai kuma ya maida kansa kasa yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa.
      “Kiyi haƙuri Maah bazan bijirema umarninki dan baki isaba. Sai dai zanyi hakane tare da tabbatar miki wannan BAƘAR INUWAr da kike hangemin gwara ranar

da kike gudanmin da ita. Ban musa miki wasu a dangin Ameenatu nada tabo na ƙaddarar rayuwa ba, amma ina son ki sani wlhy Ameenatu yarinyace kamila mai

addini. Sannan ta kawomin mu..tuncin…ta har gida. Idan zan faɗa miki wacece wadda kikema kallon mutuniyar kirkin a yanzu zakisha mamakin hakan. Maah

laifin wani baya shafar wani ko’a wajen UBANGIJI. Sannan ALLAH na fidda rayayye a cikin matacce. yana kuma fidda matacce a cikin rayayye. Hauhuwa kuwa ta

ALLAH ce, amma insha ALLAH akoda yaushe zaki iya ganin zuri’ata basai na auri wata ba”.
     Dukkanin wata fara’a dake a fuskar gimbiya Su’adah ta ɓace ɓat, baka ganin komai sai ɗunbin ɓacin rai da azabar masifa. Gasu Pa kuwa gaba ɗaya murmushi

ne kwance a fuskokinsu, bana bijirema gimbiya Su’adah da Ramadhan yayi bane. Na yabo da tabbatar da ingancin tarbiyyar Raudha da sukajine daga bakinsa.

Wanda su sanin kansune Ramadhan baya iya boye abu inhar bai masa daɗi ba zai faɗa, hakama idan yayi masa zai yaba koda da murmushi ne. Koba komai hankalinsu

ya sake kwanciya da yarinyar da suka jima suna kyautatama zato.
      Babu wanda ya sake cewa komai har ita. sai Inna ce tai musu nasiha da gaba ɗaya take nufin da gimbiya Su’adah take amma sai ta haɗa kowa da kowa a

ciki. Daga haka taron ya tashi babu wani armashi. Dan ko bikin yaran gidan da sukaso tattaunawa a yau ɗin shima bai yuwu ba dole aka barsa sai wani lokacin

dan ana jiran sauran gidajen angunan su kawo kuɗi ne. Ƴammata kusan shidda za’a aurar a gidan nasu Ramadhan. Ciki harda Lubnah da Bilkisu kuwa. Sai Sumayya,

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button