ALKALI NE Page 41 to 50

Itace ta bud’e masa k’ofa tana fad’in Jabeer nagode sosai, idan ka sake dawowa girki na zakaci. Jabeer yace lallai naga alamar da wuri zaki d’auki darasin abokina.
Murmushi tayi tana duk’ar da kanta cikin motar tace My D, kayi tuki a hankali bana so ka wahala, idan kun isa zankira naji yanda ka isa kaji. Kai ya d’aga yana d’aukar mukullin motar.
Tana tsaye har suka fita. Ajiyar zuciya ta saki tana jin wani dad’i na ratsa ta, sam batayi tunanin Ra’eez zaiyi saurin amincewa da buk’atar ta ba, shiyasa zata dage domin ta gyara komai matuk’ar hakan zaisa ta sameshi.
Juyawa tayi da niyar kiran mai aiki tazo ta kwashe kayan sai kuma ta tuna abinda Ra’eez yace. Murmushi tayi ta juya zuwa wajen kayan ta fara had’asu tayi cikin gida.
Tana shiga Momynta ta fara tambayarta an dace? Kai ta d’aga tana fad’in sosai ma, bara na kai kayan nazo. Tana fitowa tazo ta rungume Momy tana fad’in ai na fad’a maki Ra’eez bazaiki amincewa dani ba, ko awancan ranar baki ga yanda yake bina da wani kallo ba, gaskiya Momy Ra’eez ya had’u.
Momy tace amma naji dad’i sosai, kinga nan da wani lokaci sai mu fara shirin biki, lallai zanyi bikin da ba’a tab’ayinsa adangi ba, duniya sai ta sheda bikin ki Raheena, bari Alhaji yazo tun yanzu zamu fara shirya yanda komai zai kasance, ke dole duniya tasan za’ayi bikin ki.
Dariya Raheena tasa tana fad’in nagode Momy na, dole na koma group d’in mu dana fita na kawayena, domin ina son su san irin mijin da zan aura kuma inaso na tara mutane da yawa domin kowa ta samu abun fad’a.
Momy tace haka nake so ‘Diyata. Mai aiki ce tashigo bakinta d’auki da sallama. Da sauri Raheena ta amsa tana fad’in Lawisa ya akayi? Ba Lawisa ba har Momy tayi mamakin abinda Raheena tayi, domin tsakaninta da masu aikin gidan kyara ce, kome zakayi mata baka burgeta, haka kuma bata tab’a kiran sunan ka sai dai tayi amfani da kalmar Ke, ko Kai, sai gashi yau itace hada amsa sallama da kiran suna.
Duk’ar da kai Lawisa tayi tana fad’in dama abinda za’a dafa maki da dare nazo tambaya. Tashi Raheena tayi tana murmushi tace ai yau tare zamu shiga kicin d’in nima daga yau zan rik’a tayaki girki domin ina son na kware sosai.
Murmushi Momy tayi tana fad’in Raheena anya? Tashi tsaye tayi tana fad’in Lawisa muje, kallon Momy tayi tana fad’in Momy nasan bazaki so kiyima ‘Diyarki aure taje gidan miji bata iya komai ba.
Kai Momy ta jinjina tana fad’in wannan haka yake d’iyar albarka, amma naji dad’in wannan tunanin naki, ko kuma nace nagode ma Ra’eez domin nasan wannan sabon canjin daga garesa ne. Dariya Raheena tasa tayi kicin tana fad’in kai Momy.
****
Tunda suka tafi Jabeer yake damun Ra’eez da tambaya akan yanda zaiyi da Raheena. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in yanda kowane namiji yakeyi da ‘yan matansa nima haka zanyi da ita. Jabeer yace amma dai kai bakayi kama da mayaudara ba.
Ra’eez yace ka sani ko zan fara daga yau. Dukansa Jabeer yayi yana fad’in dan Allah muyi maganar gaskiya. Ra’eez yace amma dai a gabanka kaji tace tana sona ko? Kaga kuwa bazaka kirani da mayaudari ba, bata tsaya tayi binciken akwai wacce nake so ba ko babu kawai kanta ta sani, kaga kuwa idan taga na auri wata bazata zargeni ba.
Jabeer yace duk da haka, ya kamata ka fad’a mata akwai wacce kake so idan zata iya rayuwa da kai ahaka shikenan, idan kuma bazata iya ba kaga sai ta hakura.
Ra’eez yace bazan iyaba, ka sani ma wai ko ina sonta. Dariya Jabeer yasa yana fad’in ai har mata hud’u ma zaka iya aure, to Allah ya bada sa’a, amma wallahi duk ranar da aka rutsa ka kada ka nemeni. Ra’eez yace insha Allahu.
Sai da ya fara aje Jabeer gida kana yawuce gidansu Rumaisa, tana jin k’arar motarsa tayi saurin shigewa d’aki ta gyara fuskarta hada fesa turare.
Muryarsa tajiyo a tsakar gida shida Mama, kwala mata kira Mama tayi tana fad’in ki d’auko littafin ga Yayan naki nan yazo. Ciki ta shige ta barshi a saman tabarma.
Kai ak’asa Rumaisa ta fito, bakinta d’auke da sallama ta k’araso wajenshi. Tunda ta fito yaji k’amshin turarenta, dama shine yake shiya mata saboda yana matuk’ar son k’amshinsa saboda na mata ne.
Idanuwa ya tsura mata ganin yanda tayi kwalliya kamar mai shirin fita wani waje hada shafa janbaki ita da bata sonshi. Amsa mata sallamar yayi yana sakin murmushi.
Tana zama ta gaisheshi. Amsawa yayi yana fad’in Rumaisa ko dai bako zakiyi ne? Saurin kallonsa tayi tana zaro ido. Murmushi ya saki yana kallonta yanda ta zaro idanuwanta masu matuk’ar burgesa.
Maida kanta k’asa tayi tana wasa da hannunta tace ni babu wani bakon da zanyi, waye ma yake zuwa wajena. Ra’eez yace to wannan kwalliya wa akayi mawa? Rufe fuska tayi tana fad’in haka kawai naji ina buk’atar nayi.
Ra’eez yace Uhmm! Ke dai ki fad’i gaskiya. Rumaisa tace da gaske mana, yauwa wai Yaya ina kukaje? Ra’eez yace naje fira ne. Saurin kallonsa tayi idanuwanta tuni suka canza, a hankali ta mik’e tana shirin komawa d’aki.
Da sauri ya tashi yana fad’in ina zaki ba’ayi k’arin ba? Murya na rawa tace na iya ai. Ra’eez yace dawo ki zauna. Kasa dawowa tayi kawai tashige d’aki da gudu saboda kukan da taji ya taho mata, ashe dama ita kad’ai take haukanta, ta d’auka kulawar da yake bata soyayyace ashe ba haka bane a zuciyarsa, lallai ta cutar da kanta data bari ta girma da soyayyarsa a ranta.
Ra’eez kuwa jiyayi jikinsa yayi sanyi, tabbas yasan Rumaisa tana sonshi, meyasa zai fad’a mata haka? Kada garin neman ruwa kwad’o yayi masa k’afa. Lek’awa yayi wajen Mama yayi mata sallama.
A mota ya zauna yana tunanin abunyi. Kasa daurewa yayi kawai ya jawo wayarsa ya fara rubuta sako…. *Haba pretty na taya zaki tafi kibar Yayanki bayan kinsan ke kad’ai yake gani yaji dad’i, ina da kamar ki ina zan iya zuwa fira, wasa nake maki fa, Rumaisa ina matuk’ar sonki bazan iya had’a kowa da ke ba, kece rayuwata, da sonki na girma bana jin zan iya rayuwa babu ke, na dad’e ina son na fad’a maki wannan maganar amma ina tsoron kada ki kasa amincewa dani, ina sonki Rumaisa, kuma kisa aranki kece Uwar ‘Ya’Yana da yardar Allah, ina so ki maido mani da amsa idan ba haka ba bazan iya bacci ba.*
Ya mai-maita sakon daya rubuta yafi so biyar kafin ya tura fuskarsa d’auke da murmushi, yana turawa yayi saurin barin k’ofar gidan.
Rumaisa da Mama take tama fad’a akan k’uncin da ta sameta tanayi taji k’arar wayarta, amma saboda Mama tana wajen sai ta share taki dubawa. Mama tace idan kin gama k’uncin ki fito ki kai Abdallah yayi fitsari ya kwanta tunda bazaki fad’a mani abinda yake damunki ba, bansan lokacin da kika fara b’oye mani abu ba Rumaisa.
Tashi Rumaisa tayi tana turo baki tace bakomai fa Mama Yaya ne yace dole sai na bashi hadda gobe ko mu b’ata. Murmushi Mama tayi tana fad’in ai gara ku b’ata tunda kina son wasa da karatu.
Bayan ta kwantar da Abdallah taje tayi shirin kwanciya ranta a dagule, saman gadonta ta kwanta sai tsaki takeyi, wayarta ta jawo domin ta kunna karatu ko zataji sauki sai taci karo da sakon Ra’eez.
Da sauri ta bud’e, tana fara karantawa tayi saurin tashi zaune tana mutstsike ido, bata san lokacin da murmushi ya bayyana a fuskarta ba, filo ta jawo tana sakin dariya. Ta karanta sakon daya turo yafi akirga.