BAKAR INUWA 17

Typing📲
Episode 17
…………★Raudha na zaune yau an cire ƙafar tata a jikin ƙarfen dan kumburin ya sauka sosai, maimakon tayi ramar ciwo sai ta ƙara haske da ƙyau saboda samun canjin waje, ga abinci mai ƙyau ga a.c.
Idanu taɗan waro saboda mamakin ganin mahaifin nasu, cikin rawan baki tace, “Abbanmu!”.
Wannan kawai ta isa amsa ga bappi, dan cike da zumuɗi shima M. Dauda ya nufa gadon yana ware hannuwa wai zai ringume Raudha irin na turawa kar Bappi ya rainasu yaga su ƴan ƙauyene basu iya tattalin ƴaƴa ba. Sai dai kuma tunkan ya ƙaraso Raudha tai saurin ɗaukar filo ta tareshi tana faɗin, “Abbanmu lafiya?”.
Sosai dariya ta nema kufcema Bappi, yay ƙoƙarin kauda kansa yanayi ƙasa-ƙasa. Dan M. Gambo ya matsa da sauri ya ɗirkama M. Dauda dundu a baya. “M. Dauda ka nutsu mana miye haka zaka zubar mana da mutunci”.
Harararsa M. Dauda yayi, cikin yin ƙasa da murya yace, “Kai baka gane ba, idan ba’ayi hakan ba ai sai attajirin nan ya ɗauka bama kula da ƴaƴanmu, kasan su haka sukema ƴaƴansu kamar larabawa da turawa. Ko so kake yay tunanin dan munga sun raɓesune muka fara son su”.
“Eh kumafa hakane kayi gaskiya, sai dai kasan Raudhatu ustaziya ce bazata yarda ba fa, karma kaja ta bamu kunyar datafi wadda muke gudu”.
Duk zancen nasu sarai Bappi najinsu duk da a hankali sukeyi, dan shi ALLAH ya bashi ƙarfin ji, zama a iya cewa a wajensa Ramadhan ya gado ƙarfin ji, ko yaya kai magana kusa da su sai sunjika da izinin ALLAH, dan haka yay saurin katsesu dan karsu kasheshi da dariya. Ya gyara tsaiwarsa dayin gyaran murya yana faɗin, “Ya kamata ku dubata sai muje muyi sallar magrib, na kuma san masaukinku……”
Kafinma ya kai ƙarshe M Gambo ya katsesa da faɗin, “Ai bamu da wani masauki yallaɓai, dan shi M. Dauda ya rabu da gyatumar tata shiyyasa ta taho nan ita da yaran wajen tata gyatumar. Dama yanzu haka munzo biko ne da duba jikin Raudhatun”.
Raudha dake jin tamkar ta fasa ihu dan takaicinsu ta kauda kanta gefe idanunta na tara ƙwalla. Tana son mahaifinta, tana kuma fatan ya nutsu ya bar duk abinda yakeyi na ashsha, sannan sam bata baƙin cikin nunasa matsayin uba dan bata da kamarsa..
Bappi yay saurin dakatar dasu, “Ok ok babu damuwa muje muyi sallan first dai yanzu, sai musan abunyi kamar zaifi”.
Badan sun so ba suka bisa. Dan gaba ɗayansu idonsu nakan Haɗaɗɗun kulolin abincin dake gefen gadon Raudhan. Sai haɗiyar yawu suke tunkan suga abinda ke a ciki.
Suna fita doctor na shigowa. Hakan yasa Raudha roƙonsa aron waya dan gara ta kira Mommy ita kam bazata iya da halin Abba ba. Shima Dr Shamsu ya gamsu da hakan, dan haka babu musu ya bata ta saka number Mommyn, cikin sa’a kuwa bugu ɗaya aka ɗaga. Wani daɗi ya kama Asabe saboda jin muryar Raudhan Alhmdllhi, duk da dai da safe sunzo asibitin dubata ita da Aunty Hannah ma.
“Mommy dan ALLAH kizo asibiti wlhy Abba ne yazo shida baba Gambo”
Zumbur Asabe ta miƙe har tana neman yadda zani. Shi dauda ɗinne yazo Bingo harma asibitin da kike?”.
“Wlhy kuwa mommy gasu ma tare da baba alhaji (Bappi take kira haka). Yanzu ya jasu suka tafi massallaci”.
“Innalillahi wa-inna’ilaihirraji’un. Ashe kuwa zanci kaza kazan ubansu a garin nan. Ni yanzu babbar matsalata baza’a barni shiga asibitin ba….”
“Mommy dan ALLAH ki kwantar da hankalinki banga abin faɗa anan ba. Kizo asibitin Doctor zai shigo dake yace. Amma mommy dan ALLAH karki tayasa kuyi rikici Please”.
Tai maganar tamkar zatai kuka. “To” kawai asaben tace mata ta yanke wayar, badan tasan zata iya bin maganar Raudha ɗin ba.
BINA STATE PLACE
“Ranka ya daɗe bakace komai ba”.
Fulani ta faɗa a hankali cike da ƙasaita tana duban mai-martaba dake kishingiɗe a tsakkiyar falon hutawarsa da ko iyalan nasa ba kowacce keda ikon shigarsaba sai Fulani kawai.
Bai motsa ba, sai dai ya saki wani murmushin ƙasaita irin na manya, masu kuma ji da girman mulki. Kafin ya ɗago idanunsa ya ɗan dubeta ya ɗauke kansa.
“Wai miyasa ku mata a koda yaushe baku da hangen nesa ne? Yanzu banda dai son neman magana miya kawo zancen haɗa Aina’u da Ramadhan aure? bayan kunji Alhaji Hameed ya zaɓa masa mata…”
“Humm mai-martaba kenan, ni a ganina ai hakan ba wani abu bane, ƙara danƙon zumincine, ka tuna fa Ramadhan shine jikanka na farko namiji a gidan nan, da ace shi ɗin ɗane da namiji ya haifa ba mace ba shine kamarfa magajinka a yanzun, amma sam yaron nan baya son zama cikinmu, akoda yaushe sai dangin ubansa saboda Firdausi ta gama shanyesa su kaɗai yake gani ita da mijinta, amma idan muka haɗashi aure da Aina’u ta tayamu yaƙin jawosa jikinmu ai muma ka…….”
“Ya isa dan ALLAH. Yanzu nan Wasila bana hanaki irin wannan zancen ba? Yanzu miye abin asiri dan Ramadhan yafi buƙatar ya rayu a gidan su?. Karfa ki manta can ɗin shine adonsa, kuma shine tunƙahonsa, to bana son ƙara ji, hakama maganar haɗasa da Aina’u inhar ba sune suka sasanta junansu ba bana buƙatar sake jinta. Dan har abada Alhaji Hameed bazai saka doka na karya masaba koda akan ƴaƴana ne balle jikansa da yake da iko da shi tamkar yanda yake da iko akan mahaifinsa. Kuyi masa fatan alkairi kawai ku tsaya matsayinku”.
Fulani ta taune lip ɗinta da ƙarfi da haƙora kamar zata hudashi, sai dai sanin halin mijin nata yasata sakin ɗan murmushin yaƙe da cewa, “To shikenan ranka ya daɗe, yanda kace ai haka za’ayi insha ALLAH anbar zancen. Dama can rashin zama nayi nazarine akan batun shiyyasa ban fahintaba.”
“Haka nakeso ki kasance. ALLAH yayi muku albarka baki ɗaya”.
Da ƙyar fulani ta daure ta amsa tana haɗiyar zuciya. A ranta ko abubuwa masu yawa take kitsawa gameda kowacce shegiyar yarinyace zata aure mata jika sama taka.
(Hummm Fulani kina kaka inaga gimbiya Su’adah uwar miji. To maji yaya za’a kwashe to😜🏃).
★★__
BINGO CITY
Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Asabe da M. Dauda lokacin da akai kici-ɓus. Dan kuwa dai doctor Shamsu da kansa ya shigo da Aunty Hannah da Asabe, shigowarsu babu jimawa kuma Bappi da su M. Dauda suka dawo ɗakin domin yin sallama da Raudha.
Asabe ce ta fara janye idanunta tana jan tsaki, hakan yasa M. Dauda da jikinsa ke tsuma da sabuwar ƙaunarta matsowa kusa da ita cikin ɗan rawar jiki. “Haba Asabe nine fa Dauda ɗinki, dan ALLAH karkiyi fushi dani wlhy sharrin shaiɗanne”.
Hannunsa dake neman taɓata ta buge tana faɗin “Kaine sheɗan ɗin kanka ai macuci kaw……”
“Mommy Please!!…..”
Raudha ta faɗa tana fashewa da kuka dan tasan komai zai iya faruwa akan iyayenta na raba hali. Asabe zata sake magana Bappi daya fahimci su ɗinne iyayen Raudha ɗin yay saurin dakatar da ita.
“Inaga nan ba wajen magana bane, kamar zaifi muyi haƙuri muje daga waje ko masaukinku ko? Ko kuma mu bari zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu…..”
“A’a dan ALLAH ranka ya daɗe gara ayita yau ta ƙare, idan ta bar nan bazata sake yarda na gantaba, zama ta iya sace Aminar daga nan ɗin itama”.
Harara Asabe ta balla masa, sai dai riƙe hannunta da aunty Hannah tayi ya sata yin shiru ta haɗiye abinda taso faɗa.