Uncategorized

AMANA TA CE Page 11 to 20

           Da gari ya waye sallah yayi yace ta zauna a gun kartaje ko ina zaije ne man abunyi ko da dako yasamu don su rinka samun abunda za suci da in da zasu zauna, haka ko akayi ya shiga cikin kasuwar winti, haka yayi yawo sosai amam shiru ba lbr aiki sai azahar ya dawo yaje ya sayo musu shinkafa sukaci, bayan sunci tace Yaya na anyi nasara kuwa cikin mutuwar jiki yace ina Allah baisa an dace ba, idonta yaciko da kwalla tana shirin yin kuka ya girgiza mata kai alamar aa, yace ko kin manta Allah yana tare da mu bazai barmu haka ba, kuma duk bakin da Allah ya tsaga bazai hana shi abinci da zaici ba.

haka suka sake kai dare nan suka sake kwana.

           Washe gari ma haka yafita yayi yawo har ya gaji gashi yan kudinsa sun soma karewa saura dari biyar, yau sai bayan la’asar ya dawo dake ya ba ma Auta naira dari don tasayi abunda zataci ko da yadawo yasamu tana bacci akan yar fallen zanin da ta shimfida tausayinta ya kama shi, Allah sarki auta yau itace tamkar wata tsintaciyar mage gwamma shima namiji ne, idonsa ne ya ciko da kwalla a zuciyarsa yake adu’ah Allah ya kawo musu dauki baisan hawaye yana sauka da ga idonsa ba saiji yayi auta na share masa hawaye itama idonta yaciko da kwalla, tace Yaya na sai dayaji sanyi har cikin ransa, mai yasa ka kuka ban son ganin hawayen ka, in kai kayi hawaye wazai rarrashe ni, kaine mai sani farin ciki, Allah gatana kaine gata na, yaya na waya taba ka karkasa kanka cikin damuwa Allah zai kawo mana mafita yana tare damu kaji, kaman karamin yaro ya daga mata kai, tace kayi min murmushi, ammar baisan lokacin daya murmusa ba, itama murmushin tayi ta rike hannunsa tace Ya Allah kaja kwanan yaya na kabani abunda zan saka masa dashi.

®WISDOM HAUSA WRITER’S

   

Rash Kardam

[7:35PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

   

               ®WWA®

                           

Hancin ta ya lakace yace Ameen amma kwanan mu gaba daya, haka suka zauna cikin farin ciki har dare yayi suka kwanta.

            Da safe ammar ya sake fita nan ma ya barmata kayan karin kumalo ya fita, nan yayi ta yawon niman aiki da kyar ya samu wani shago zasuna debo kaya daga stored suna kaiwa cikin shago amma ba kullum ba sai randa za a saka kaya a shago ko sun dawo daga sari, haka ya dawo da murna yake sanarmata, nan ta tausaya masa tace Yaya na zaka iya yin dako kuwa kai ya daga mata yace eh kan wata, in dai zamu samu abunda zamuci Alhamdulilah.

Washe gari haka suka tashi kudin su ya kare sai naira hamsin shinkafa ya sayo ma auta ya zauna yasata a gaba taci, tace aa sai dai su ci tare fir yaki don ba zai ishesu dukansu ba, auta taki ci ganin haka yasa ya dau cokalin roba ya fara bata lbr abun dariya yana bata a baki tana ci har ta cinye , ta kalli kwanon tace kai yaya na gashi kasa na cinye kai ya girgiza mata alamar kar ta damu, haka sukayi ta hira har dare,

      Futha ce ta fito sanye cikin shiga ta alfarma ta shiga motarta ta nufi makarantar da tafara zuwa, bayan sunyi lectures kenan tafito tana zaune, kiran sady ne ya shigo bayan sun gaisa ta tambayeta kwana biyu tace lfy nan suka taba hira ta hakuri gameda abunda babanta ya mata nan sukayi sallama ta dau ko hanyan gd tun daga nesa ta hango wata sabuwar mota honda ta hadu motar blue kalo daga gidan su Auta tafito wanda yanzu su Sady ne acikin gdn, sai da tazo kofar gidansu ta tsaya don ta karbi lab top dinta da tabada ya duba mata, bayan ta karba ta fito taga wan nan Honda tatsaya dai2 ita nan aka zuge glass wacce ta gani a motar bakara min mamki tayiba da ace itace a wannan motar, pinky ce yar kanini baban Auta wato yar Baba Isiyaka, hy tace mata sai a lokacin ta dawo daga duniyar tunani gaisawa sukayi ya kwana biyi tace lfylau ya school tace Alhamdulilah, sun dayi hira kafin sukayi sallama, futha ta tafi tana tsananin mamaki sosai da sosai pinky ce haka harda mota lalle sun samu duniya tabbas dawata a kasa dole ma tabi didigi haka taja motarta tashiga gida tan tunani kala2.

            Can cikin dare wani hadari ya hadu ga iska daya taso sosai, Yaff yaff yaff ruwa da iska yasoma zuba, kan kace me sai ga ruwa ya barke baka dan ba,

nan Ammar suka farka kafin sunimi matsuguni rua ya soma dukan su bakadan ba duk inda zasu fake ankulle nan suka dun kule a gindin shiya ruwa nan dukansu Auta ta kan kame ammar tana yar kuka ga ruwa sai dukar su yakeyi wani tsawa aka sake sosai wanda yasa Auta kara rugume ammar har sai da yaji tsikar jikinsa ya tashi yaso ya ture ta don yanda yasoma feelings, ga wani murdawan da maranta keyi alamar period ga ruwa na dukan su gaka ruwan ya kare akansu tass barin sanyi auta takeyi ga maranta na murda mata gashi ba kayan canzawa haka suka tsuguna a tsugune har gari ya waye jikinsu har ya bushe auta kam mara ke ciwo gada2 ga zazzabi na neman mata mumunan kamu nan hawaye ya soma zuba don tabbas period dinta ne gashi kudinsu ya kare ga pant daya ke jikinta kayan da zata canza ma baba gashi kwananta 2 ba wanka sai yau da ruwa ya mata duka Yasalam!!! Allahuma ajirni fi musibati wa aklifli khairan minha, jikinta yayi zafi sai barin dari takeyi Ammar ko da ya taba jikinta nan take ya rikice ya shiga da muwa gashi kudinsu ya kare ga auta jikinta yayi zafin Innalilahi wa inna ilaihi raji’un yake furtawa a bakinsa.

   ®WISDOM HAUSA WRITER

Rash Kardam

[7:35PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

   

               ®WWA®

                           

Jikin auta yayi zafi sosai ga ciwon mara, ammar duk ya rude yarasa me ke masa dadi ga kudinsu ya kare gefen wani shagon daya ga ba a budewa yaje ya kwantarta lokacin gari yayi haske sosai ya cire yar rigansa na janfa ya luluba mata nan yace auta kiyi hakuri barin fita neman kudi ko zan samu sai in saya miki magani kai ta daga masa hannu sa ta riko cikin muryan marasa lfy tace Yaya na Allah ya ka fita sa’a ya amsa da amin, ya fita 

       Shagon dako yaje yayi sa’a an kawo kaya nan ya yasoma aikin kwasan kaya tun bakwai yagara sai karfe shadaya ya gama nan aka bashi kudin aiki 200 dake kayan ba masu nauyi bane shiyasa, hamdalla yayi yana shirin barin layin masu kayan zai wuce yaji wasu suna neman mai zubar da shara nan yayi aikin ya gyara musu gurin tass suka bashi 50 daya layin ma sun kitashi nan ya fara musu aiki aka soma kiran sallah ya bari da sauri ya ce zaije ya dawo yana fita chemist yaje yasayo maganin mura dana zazzabi yabi yasayo musu shinkafa auta harda tea irin na masu yawo suna hadawa yasa mata da murna ya kama hanya zuwa gunta.

     Futha bayan ta huta washe gari tacr ma Sady tana so su hadu akwai abunda takeson sani, nan sady tace zasu acikin Kad poly haka ko akayi da yamma suka hadu bayan sun gaisa futha take bata lbr abunda ta gani Sady tace nima abun ya daure min kai don pinky bakara min busha take ba kuma Abba na nima yace wai ya sai min mota ba a shigo da ita bace ni kaina futha yanda suke bushasha da dukiyar su Auta abun har na razana ni kuma har yanzu sunki yarda ayi binciken akan wayanda sukayi kisan nan da kuma inda Auta take, futha tace kar kidamu sannu a hankali komai zai zama tarihi Allah ya toni asirin duk wannda keda hannu a wannan al’amarin Sady tace Ameen nan suka yi hira gameda karatu har sai magrib suka rabu.

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button