AMANA TA CE 1-END

AMANA TA CE Page 51 to 60 (The End)

  Munay da Kausar kulum suna hanyan Asibiti a d’an kw’anak’in da sukayi suna zuwa Asibiti Munay tana sh’ish’ige ma Auta ta kuma bata hak’uri akan abunda ya faru baya.

 Kw’anan Ammar biyu a Asibiti aka sallame sa, tunda suka dawo Auwal ke dawainiya da su, sam bai nuna gazawarsa. 

Yau Ahyan zai dawo H Mamu ta kira Kausar tace”ina son kiyi girki ma yayanki yau zai dawo, ta da’uko wasu k’aya masu ky’au tace kisa wannan zakije ki da’uko sa daga Airport. Cike da ladabi ta amsa tace”nagode Mum Allah ya k’ara bud’i yasa afi haka. Ameen!

Sai da ta gama girki kafin tayi wanka tasa goduwar rigace bakaramin ky’au ya mata ba. Key d’in motarta ta d’auko ta nufi d’akin Mum da sallamarta ta tura k’ofar ta shiga, tace “Mum nagama girkin na jera su a inda ya dace, kuma bros ya kirani yace nan da 40minutes jirginsu zai sauk’a, ina son inje da wuri k’ar yayita jirana.H Mamu tace”to sai kin dawo Allah ya kare, banda tuk’in gan-ganci. Ta amsa mata da to ta fito cikin nutsuwa take tafiya harta isa ABUBAKAR TAFAWA/BALEWA AIRPORT. Bata dad’e da zuwa aka sanar nan da 5minutes Jirgin UK zai sa’uka. Jirgin na sa’uka fasinja suka suma fitowa mik’ewa nayi naje gurin, sai da mutane suka fir-fito can na hango Yaya Ahyan cikin wata bakar Suite yayi masifar ky’au ya kara haske da k’iba,sai ya dawo min tamkar wani bako ciiin zuciyata nake cewa”gsky Yaya Ahyan na karshe ne duk macen da ta same shi taji dad’i,” Ya Ahyan yana matuk’ar burgeni amma kash zai yi wuya na saye zuciyarsa. Ahyan kuwa tunda yake sau’kowa ya ky’alla idonsa a kan kausar sai da ya kusa suman tsaye, d’an shek’ara biyu zuwa uk’u da yayi baya gari, Kausar ta k’ara cika da ky’au tamkar ba ita bace. Hmmm yace”Kausar ina matuk’ar sonki tun kina yar yarinya amma nasan Mum da wuya ta bani ke. Dai-dai lokacin ya iso kusa da ita. Sam bata san ya iso ba saida ya hura mata iska a idonta wani sas-sanyan ajiyar zuciya ta saki, sai alokacin ta farga ya iso kusata ita, watsowa yayi dab da ita har tana jiyo fitar numfash’insh’i, ga shi duk ya cikata da kamsh’in turarensa Ayhan yace”Kausar mai kike tunani haka?. In ka ji yanda ya ke maganar tamkar rad’a zai mata a’cikin kunnenta.

Cikin jin kunya tace maba babu ok! Trolley da ke hannu sa ta karb’a suka sh’iga mota, tun a hanya Ahyan ke satar kalonta har suka iso gida. Munay tana jin tsatuwar mota ta fito da gudu tana oyoyo my bros, tana i’sowa sukayi sharking din hannu, suka nufi cikin gd.sai da Ahyan ya huta Kausar ce tayi serving d’insa bayan yaci abinci ne ya shiga gaida Mum.

Bayan sun gaita H Mamu take tambayarsa Yaya karatu? Alhamdulilah! Yanzu kam mun kammala result yayi ky’au duka suka amsa da Alhamdulilah! Allah ya sanya Al’k’airi Ameen.

Mum tace”Ahyan kaje ka huta zuwa dare ina son ganin ka zamuyi magana, ya amsa da to ya tashi ya nufi d’akinsa da Kausar ta gyara masa sh’i. 

Ammar kam jiki Alhamdulilah ya war-ware har ya fara fita, abunka da mai zafin nama. Yana zaune wayars tayi kara Hajiya Mamu yagani cikin girmamawa ya d’aga wayar bayan sun gaisa Hajiya tace”Ammar ya karfin jikinka?, yace da sauki, tace Alhamdulilah! Yau in ka taso daga kasuwa ina son ganinka da magriba, to Mum zan’zo in Allah ya kaimu, yauwa nagode sai’anjima.

Ammar na sallah magriba ya zo gun Hajiya sai da ya gaisa da mai gadi kafin ya sh’iga ciki.

Munay ya fara gani a falo yaukam cikin nutsuwa ta gai dash’i ya amsa ta je kitchen ta kawo masa drink da abinci, tace”barin k’ira maka Mum din, bata jira amsan sh’i ba ta nufi sama, tana zuwa ta sanar da Mum Ammar ya zo H Mamu tace”ki kaisa falon baki can zamuyi magana, sannan ki bi kice ma Yayanku ya same ni acan to ta amsa. Sai da ta fad’a ma Ahyan tukun ta sanar da sak’on Mun wa Ammar, dake ba bak’oba ne falon ya sh’iga ya zauna, sai ga Ahyan ma ya sh’igo hannu ya mika masa suka gaisa, Mum ne tash’igo itama da sallama suka amsa ta nimi gu ta zauna, nasiha ta musu sosai mai sh’iga jiki, sunansu tak’ira d’aya bayan d’aya suka amsa ta d’anyi sh’iru kafin tace”na yanke hukunci had’aku aure da k’anne ku. Cikin razana suka d’ago a tare suna kallonta, sake mai-maita abunda ta fad’a tayi, Ahyan ta kanka zan fara, kasani tun lokacin da yar’uwa ta take raye muka yi al’k’awarin zamu had’a ya’yanmu Aure, ina son in cika wannan burinmu, kuma bin umarni na sh’i zai sa na yafe maka abunda kayi min, don haka na yanke hukunci had’aka aure da yar’uwan ka Kausar har na sanar da yan Sokoto. Ba shawara nake baka ba umarni na baka, ta kai dubanta ga Ammar ta kira sunansa, ya amsa jiki ba kw’ari,tace”Ammar kaima ina ga zaka auri Zainab don tafi sabawa da kai ta sh’ak’u da kai sosai, Ammar a cikin zuciyansa yafurta Alhamdulilah!.a fili kuma sunkuyar da kansa yayi yace to Mum Allah yasa hakan shine mafi al’kairi!, Ta amsa da ameen. Tace”don haka kuje ku fara sh’iri wata sati ne d’aurin Aure da tarewa. Sannan bace sai kunyi kayan karya ba a’a mu al’kairin abu mukeso suka amsa da to sh’ikenan ku tash’i kuje Allah ya muku albarka ameen. Amm Ammar ina so ka zo min da Auta da kayanta zata dawo gdn nan harsai anyi biki sai ka d’auketa to ya amsa suka fita.

 Ammar na isa gida wata zuciya tace karkayi sauri sanarda Auta kai zata Aura halama bata sonka kawai ka gwadata ka gani.

Da sallama ya sh’iga gidan amam ya d’aure fuska Auta da fara ta masa sannu da zuwa, ganin yanayin sa ya sa tace”Yaya na mai ya sameka? Kona maka laifi ne? Kai ya gir-giza mata alamar a’a to mai yasame ka? Dan Allah ka sanar min.

Cikin al’hini ya soma yimata bayani kam hahiya zata hadasu Aure kuma wata sati duk Auta ta k’agu taji da waye yace ni da Kausar da ke da Ahyan what?? Tace “ina sam bazaiyuba ni wlh bana sonsh’i. Ina da wanda nake so, cikin damuwa Ammar yace” wa kike so?.shiru tayi tana kallonsa don bata san lokacin da ta furta maganan ba, Ammar yayita bata kalamai akan ta d’au k’addara da abunda Allah ya zab’a mata, Auta kam kuka ta somayi mara sauti, daren ranan bata rintsa ba.

Da safe kuwa idonta duk ya kumbura Ammar na ganin ta sai duk ta bashi tausayi kamar zai fad’a mata ko zata samu sauki, don yana hango tsagw’aron Sinsa acikin kw’ayar idinta amma ya share.

Yace”Auta ki sh’irya zuwa dare ina dawo zan kaiki, cikin fush’i tace”ni ba inda zanje kai naga alamr ma baka damuba daman baka damu dani ba, kuka ta saki mai tsuma zuciya har k’asan zuciyansa yake jun kukanta, fita kawai yayi a d’akin don bazai iya saura-ronta ba. Yinin ranan bata ci abimci mai ky’au ba sai da azahar ta samu bacci ya d’auketa ko da ta tash’i bayan la’asar idonta ya washe wanka tayi takiyin kw’aliya tace”ni ba ida zani daman son da Ammar ke min bana gsky bane, hmm ko ajikinsa bai damuba mts ni haushin Kausar din ma na fara ji. Ni rash nace”kw’aji min Autan nan harta na da bakun iya fush’i Ammar kuma fa da ya ganta da saurayi yayi yaya?.

Da yamma da Ammar ya dawo sunsha rikici don fir tace ita ba inda zata je, sai data ga ya bata rai kafin ta fito tana kuka ta dan debi kayanta kad’an suka tafi.

A gd basu same su ba don sun fita sayayya tana zuwa dakinta ta wuce, sai magriba suka dawo ganin karsu fahimci halin da take ciki yaa ta d’an biye damuwarta ta sake kad’an, sukayi hira har zuwa 8:40 Mum ta haura sama Munay ma haka Kausar da Auta kad’ai a falo.

1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button